An Kama Mutanen da ake Zargi da Bankawa Ofishin PDP Wuta a Zaben Fitar da Gwani
- Rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi ta kama wasu mutane da ake zargi da hannu a harin da aka kai sakatariyar PDP yayin zaben fitar da gwani
- Ana zargin waɗanda aka kama da haɗa baki wajen aikata laifi, tayar da hankalin jama'a da lalata dukiyoyi a lokacin da 'yan PDP ke zabensu
- Kwamishinan ‘yan sanda ya yi gargaɗi ga masu tayar da rikicin siyasa tare da jaddada aniyar hukunta masu laifi, kuma ana binciken wadanda aka kama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
'A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Bauchi – Rundunar ‘yan sandan Bauchi ta sanar da cafke wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a harin da aka kai sakatariyar jam'iyyar PDP a jihar.
A wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, SP Nafiu Habib, ya fitar, ya ce jami'an rundunar da ke aiki a sashen ‘B’ a GRA ne suka gudanar da kamen bayan gudanar da bincike a kan lamarin.
Sanarwar ta ce an kama waɗanda ake zargin ne bisa laifukan haɗa baki wajen aikata laifi, tayar da hankalin jama'a da kuma lalata dukiyoyi bayan harin da aka kai sakatariyar jam'iyyar.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa rahoton da rundunar ta samu ya nuna cewa a ranar 24 ga watan Mayun 2026 da 2.00 na rana, wasu sun kutsa cikin harabar sakatariyar PDP da ke kan titin Maiduguri Bypass a lokacin da ake gudanar da zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar gwamna.
An dagula zaben PDP a Bauchi
Leadership ta wallafa cewa maharan sun haddasa tarzoma tare da dagula zaman lafiya a yankin, sannan suka lalata allunan yaƙin neman zaɓe na ɗan takarar gwamnan jam'iyyar.
Rahoton ya kara da cewa mutanen sun farfasa gilasan wasu motoci da aka ajiye a gefen hanya kafin daga bisani su tsere ta kan babura.
Bayan yaɗuwar rahotannin harin a kafafen sada zumunta, rundunar ‘yan sanda ta ce ta ƙaddamar da bincike da tattara bayanan sirri domin gano masu hannu a lamarin.
Yan sanda sun damka matasa a Bauchi
Sakamakon binciken ya kai ga cafke Hamza Abdullahi wanda aka fi sani da "Dawa", mazaunin bayan tsohon filin jirgin sama na Bauchi, da kuma Abdul Malik Dahiru wanda aka fi sani da "Black", mazaunin yankin Doya a cikin birnin Bauchi.
Rundunar ta bayyana cewa an miƙa waɗanda ake zargin ga sashen binciken manyan laifuffukan tashin hankali domin zurfafa bincike cikin sirri da kuma tattara ƙarin hujjoji.

Source: Twitter
Ta ce da zarar an kammala bincike, za a gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar tuhume-tuhumen da suka dace.
A nasa jawabin, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yi kakkausar gargaɗi ga duk masu aikata ayyukan da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya ko lalata dukiyoyin jama'a.
Ya tabbatar wa mazauna jihar cewa rundunar na ci gaba da ɗaukar matakan tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Tsagin PDP ya tsayar da dan takara
A baya, kun samu labarin cewa duk da rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar PDP, an ayyana tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar shugaban kasa.
An tabbatar da takarar Jonathan ne a taron musamman da aka gudanar a Abuja, inda Fred Agbedi ya karbi takardar shaidar nasara a madadinsa domin bai halarci taron mika masa tutar ba.
Bayan jami’an tsaro sun hana shiga wurin taro na farko, shugabannin bangaren PDP sun sauya wuri tare da alkawarin sanar da ranar mika tuta yayin da rikici tsakaninsu da Wike ke kara zafi.
Asali: Legit.ng

