Gwamna Ya Ajiye Girma Yana Rokon Talaka Afuwa da Sake Zaben APC a 2027

Gwamna Ya Ajiye Girma Yana Rokon Talaka Afuwa da Sake Zaben APC a 2027

  • Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya roki mazauna jihar da su yafe kura-kuran gwamnatinsa da na ’yan majalisar da aka zaba
  • Bugu da kari, gwamnan ya yi kira ga jama'ar jihar Ebonyi da su sake bai wa jam’iyyar APC goyon baya a babban zaben shekarar 2027
  • Gwamnan ya yi wannan kira ne a ranar Lahadi, 31 ga watan Mayun 2026 yayin wani taro da aka gudanar a wajen ibada na gidan gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ebonyi - Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya bukaci al’ummar jihar da su yafe kura-kuran gwamnatinsa da na ’yan majalisar da aka zaba, tare da rokon su su goyi bayan jam’iyyar APC a babban zaben shekarar 2027.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan siyasa da jam'iyyu ke shirye-shiryen zaben 2027 domin samun madafun iko a matakai daban-daban.

Kara karanta wannan

'Ba mu da zabi': Nyesom Wike ya yi magana kan sake zaben Tinubu a 2027

Gwamna Francis Nwifuru
Francis Nwifuru a wajen taron APC a Ebonyi. Hoto: Rt. Hon. Francis Ogbonna Nwifuru
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa Nwifuru ya yi wannan kira ne yayin taron godiya da aka gudanar a ɗakin ibada na gidan gwamnati da ke Abakaliki domin bikin cika shekaru uku da gwamnatinsa ta yi.

APC: Gwamna ya roki talakawa

Da yake jawabi ga masu ibada, jami’an gwamnati da shugabannin addini, gwamnan Ebonyi ya amince cewa gwamnatinsa, 'yan majalisar tarayya da na jiha na iya yin wasu kura-kurai yayin da suke yi wa jama’a hidima.

Sai dai ya bukaci mazauna jihar da su yi masu afuwa, su yafe masu kura-kuran tare da ci gaba da goyon bayan wakilansu da aka zaba.

Punch ta rahoto gwamnan ya ce:

“Don Allah ku yafe mana; ku yafe min tare da mambobin majalisar tarayya da na majalisar dokokin jiha. Ku yafe kura-kuranmu sannan ku sake zabenmu,”

Nwifuru ya samu nasarori

Da yake waiwayen shekaru ukun da ya yi a kan mulki, Nwifuru ya gode wa Allah bisa nasarorin da gwamnatinsa ta samu, yana mai cewa shugabanci wata hanya ce ta ci gaba da koyo wadda ke bukatar tawali’u, jajircewa da fahimtar jama’a.

Kara karanta wannan

"Ina tsaro a Kano?" Aminu Gwarzo ya dura a kan gwamantin Abba

Gwamnan ya amince cewa babu wata gwamnati da za ta iya cewa ta kai matsayin kamala, amma ya tabbatar wa jama’a cewa gwamnatinsa na ci gaba da himmatuwa wajen fadada abubuwan more rayuwa da sauransu.

Ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen ci gaba da manufofin da aka fara domin inganta walwalar mazauna jihar.

Gwamna Francis Ogbonna Nwifuru
Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru yana bayani a coci. Hoto: Rt. Hon. Francis Ogbonna Nwifuru
Source: Facebook

Taron godiyar ya samu halartar fitattun jagororin siyasa, ciki har da tsofaffin gwamnonin jihar, daga cikinsu akwai Ministan Ayyuka, David Umahi.

Kotu ta rusa jagororin APC

A wani labarin, mun kawo muku cewa kotun daukaka kara da ke jihar Rivers ta tabbatar da rusa shugabannin jam'iyyar APC da aka zaba a baya.

An bayyana cewa rusa shugabannin da suke yi wa ministan Abuja, Nyesom Wike biyayya zai iya shafar matakan da suka dauka a kafin hukuncin kotun.

Hakan na zuwa ne yayin da gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ya sanar da cewa ba zai nemi takarar gwamna a zaben fitar da gwani na APC ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng