Yadda aka kama Sarkin Fulani da manyan ƴaƴansa kan zargin garkuwa da mutane
- 'Yan sanda a Ogun sun kama Sarkin Fulani na Ijebu Ode tare da ɗansa bayan zarginsu da alaka da masu garkuwa da mutane
- Sarkin Fulanin ya musanta hannu a satar mutane, amma ya amince cewa ya san ɗansa Bala yana aikata laifin garkuwa kafin a daure shi
- 'Yan sanda sun ce Bala da wasu 'yan uwansa sun tsere ta cikin daji bayan samun labarin zuwan jami'an tsaro, yayin da bincike ke ci gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abeokuta, Ogun - Rundunar ƴan sanda a Ogun ta cafke wani Sarkin Fulani da yayansa kan zargin garkuwa da mutane.
Abdullahi Muhammadu, mai shekaru 67 da haihuwa, wanda shi ne Sarkin Fulani kuma jagoran al'ummar Fulani a Ijebu Ode, ya musanta masaniya kan lamarin.

Source: Facebook
An kama shi tare da babban ɗansa bisa zargin hannu a hare-haren garkuwa da mutane da suka addabi al'ummomi daban-daban a yankin Ijebu na Ogun, cewar Punch.
Yadda aka gano jakar kudi a gidansa
Ko da yake ya musanta hannu a laifukan, an ce jami'an tsaro sun gano daya daga cikin jakunkunan da aka yi amfani da su wajen karɓar kuɗin fansa.
Rahotanni sun nuna cewa an gano jakar ne a cikin girkinsa yayin binciken da rundunar yaki da masu garkuwa da mutane ta gudanar.
Sarkin Fulanin ya amince cewa ya san ɗansa Bala Muhammadu yana harkar garkuwa da mutane kafin a kama shi a baya.
Ya bayyana cewa Bala ya yi zaman gidan yari na tsawon shekaru biyar saboda laifin garkuwa da mutane kafin daga bisani a sake shi.
Muhammadu ya ce bayan dawowar Bala daga gidan yari, ya kai shi asibiti domin jinya saboda rashin lafiyar da ya same shi.
A cewarsa, ya yi tunanin cewa Bala ya daina aikata laifuka kuma ya koma harkokin noma da kiwon shanu.

Source: Original
Zargin da jami'an tsaro ke yi
Sai dai jami'an tsaro sun yi zargin cewa Bala da wasu 'yan uwansa sun tsere bayan samun bayanin zuwan jami'an tsaro yankinsu.

Kara karanta wannan
Mai dokar barci: Sojoji sun damke 'dan bijilanti da zargin yi wa ISWAP leken asiri
Wata majiya ta kara da cewa ba Bala kadai ke da hannu a lamarin ba, domin ana zargin wasu 'yan uwansa ma.
Muhammadu ya shaida wa manema labarai cewa ya kwashe sama da shekaru 30 yana rayuwa a yankin Yarabawa tare da mata hudu da yara 30, kuma an ba shi sarautar Sarkin Fulani ta Ijebu Ode.
Ya jaddada cewa bai taba yin garkuwa da wani mutum ba kuma bai san yadda jakar ta shiga gidansa ba.
Bello Muhammadu, babban ɗan gidan da aka kama tare da mahaifinsu, ya ce shi makiyayi ne kuma ba shi da hannu.
Ya bayyana cewa yana gona lokacin da jami'an tsaro suka isa gida, kuma bai san ayyukan Bala ba, cewar Daily Post.
Bello ya ce idan mahaifinsu ya san Bala ya koma aikata laifuka, da kansa zai hukunta shi saboda baya goyon bayan miyagun ayyuka.
Martanin rundunar ƴan sandan Ogun
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Ogun, Oluseyi Babaseyi, ya yabawa jami'an rundunar saboda nasarar aikin.
Ya ce goyon bayan Sufeto Janar na 'Yan Sanda, Olatunji Disu, ya taimaka wajen gudanar da ayyukan tsaro cikin nasara.
Babaseyi ya kuma yabawa Kwamishinan 'Yan Sandan Ogun, Bode Ojajuni, bisa jagoranci da dabarun da suka taimaka wajen samun sakamako mai kyau.
Yan bindiga sun farmaki ɗalibai a Ogun
A baya, kun ji cewa yan bindiga sun kutsa dakunan kwanan dalibai na Jami'ar OOU da tsakar dare, sun yi awon gaba da abubuwa masu muhimmanci.
Bayanai daga mazauna yankin sun bayyana cewa daliban makarantar sun shiga yanayin firgici yayin harin, wasu da dama sun samu raunuka.
Rundunar yan sandan jihar Ogun ta ce ta tura jami'anta zuwa yankin domin gudanar da bincike kan abin da ya faru a gidan kwanan dalibai.
Asali: Legit.ng

