Dubu Ta Cika: 'Yan Sanda Sun Cafke Tantirin Jagoran 'Yan Bindiga a Zamfara

Dubu Ta Cika: 'Yan Sanda Sun Cafke Tantirin Jagoran 'Yan Bindiga a Zamfara

  • Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Zamfara sun samu nasara a yakin da suke yi da masu aikata miyagun laifuffuka
  • 'Yan sandan sun samu nasarar cafke wani tantirin jagoran 'yan bindiga bayan samun bayanan sirri
  • Hakazalika, 'yan sandan sun samu nasarar cafke wasu 'yan bindiga da dama tare da kwato makamai masu yawa a hannunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Zamfara - Jami’an sashen mayar da martani ga laifuffukan tashe-tashen hankula (VCRU) na rundunar ’yan sandan jihar Zamfara, sun cafke wani jagoran 'yan bindiga.

Jami'an 'yan sandan sun cafke Ali Bahago Danakulu, tare da wadanda ake zargi mataimakansa ne a karamar hukumar Kaura Namoda.

'Yan sanda sun cafke jagoran 'yan bindiga a Zamfara
Jami'an 'yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da Legit Hausa ta samu.

Kara karanta wannan

Sojoji da 'yan ta'adda sun gwabza kazamin fada a Kogi, an rasa rayuka

'Yan sanda sun samu nasara a Zamfara

Ya ce an samu nasarar kama su ne biyo bayan samun bayanan sirri wanda ya jagoranci jami’ai zuwa ga wata ƙungiyar masu laifi da ke addabar mazauna yankin Kasuwan Daji da sauran maƙwabtan kauyuka.

A cewarsa, wadanda ake zargin sun daɗe suna kan jadawalin bincike na rundunar saboda zargin hannu a fashi da makami, fashin daji, da sauran laifuffukan tashe-tashen hankula a yankin.

Jagororin 'yan bindiga sun shiga hannu

Wadanda aka kaman sun haɗa da Ali Bahago Danakulu na Kasuwan Daji, Hassan Dan Kure, shi ma na Kasuwan Daji, da kuma Dahiru Lawali na Gidan Ango.

Ya ce binciken farko-farko ya nuna cewa wadanda ake zargin mambobi ne na ƙungiyar masu laifi ɗauke da makami wadda ake zargi Ali Bahago ne ke jagoranta, wanda kuma aka haɗa shi da ayyukan laifi da dama a yankin.

DSP Yazid Abubakar ya ƙara da cewa an kashe mamba ɗaya na ƙungiyar a lokacin gudanar da aikin, yayin da aka kama mutane uku da ake zargi.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe kansila da babban darakta a Zamfara kwanaki 10 da sace su

An kwato makamai

Kayayyakin da aka samo a lokacin gudanar da aikin sun haɗa da bindiga ƙirar pump-action guda ɗaya, bindiga mai baki ɗaya guda ɗaya, bindiga ƙirar G3 da aka ƙera, bindigogin farauta guda biyu, harsasai masu kaurin 7.62mm guda huɗu, harsashin pump-action guda tara.

Sauran sun hada da sarka guda ɗaya ta ankwa, bindiga ƙirar bastola da aka ƙera ta cikin gida guda ɗaya, baburan Boxer guda uku.

'Yan bindiga sun shiga hannun 'yan sanda a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

A halin yanzu wadanda ake zargin suna tsare yayin da ake ci gaba da bincike, tare da ƙoƙarin gano sauran mambobin ƙungiyar domin kama su.

Rundunar ta sake jaddada jajircewarta na ci gaba da gudanar da ayyuka kan ƙungiyoyin masu laifi ɗauke da makami, kuma ta buƙaci mazauna yankin da su ci gaba da ba da sahihan bayanai a kan lokaci ga hukumomin tsaro.

'Yan bindiga sun yi barna a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ta'adda sun kashe wani kansila da wani darakta na karamar hukumar Talata Mafara a Zamfara.

Kara karanta wannan

Yadda aka kama Sarkin Fulani da manyan ƴaƴansa kan zargin garkuwa da mutane

Kisan da 'yan ta'addan suka yi ya biyo bayan kin karbar kudin fansa da aka ba su domin sakin su bayan kwanaki 10 da sace su.

Wadanda aka kashe sun hada da Muslim Habibu, kansilan mazabar Jangebe, da Jamilu Sani, daraktan tsare-tsare na karamar hukumar Talata Mafara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com