Atiku Ya Kalubalanci Tinubu kan Sayo Motocin Alfarma a kan N15.13bn
- Atiku Abubakar da ke neman takarar shugaban kasa ya yi mamakin yadda bayanan sayo motocin alfarma na N15.13bn a gwamantin Bola Tinubu
- Atiku da ke adawa da salon mulkin Tinubu ya bayyana bukatar a bayyana kamfanin da ya samar da motocin da lambobin chassis dinsu
- 'Dan takarar shugaban kasar ya kuma yi maganar wasu kudi Naira biliyan 947.70 da aka ce an ware domin aiwatar da ayyukan jin kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya caccaki gwamanti kan sayo motocin alfarama 39.
Ya bukaci gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta fito fili ta bayyana cikakkun bayanai kan shirin sayen motocin alfarma 39 da aka ware kuɗinsu Naira biliyan 15.13 a kasafin kuɗin shekarar 2026.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa Atiku ya yi wannan kira ne bayan ƙungiyar sa ido kan kasafin kuɗi ta Tracka ta bayyana cewa an ware N15.13bn domin sayen motocin SUV guda 39, lamarin da ya nuna cewa kowace mota za ta kai kusan Naira miliyan 387.
Atiku ya dura kan gwamnatin Tinubu
The Guardian ta wallafa cewa a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan hulɗa da jama'a, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta yi bayani game da motocin alfarmar.
Ya nemi ta bayyana nau'in motocin, samfurinsu, shekarar ƙera su, kamfanin da zai samar da su, bayanan kwangilar da kuma VIN wato lambar chassis ta kowace mota.

Source: Facebook
Ya ce:
"Idan an riga an sayo motocin, gwamnati ta gaggauta fitar da nau'in su, samfurinsu, shekarar ƙera su, kamfanin da ya samar da su, bayanan kwangilar da kuma chassis number, na kowace daga cikin motocin 39."
Atiku ya ƙara da cewa idan har ba a kammala sayen motocin ba duk da an shafe watanni takwas ana aiwatar da kasafin kuɗin bana, ya dace gwamnati ta bayyana dalilin jinkirin.
Atiku ya yi mamakin tsadar motocin
Ya kuma tambayi dalilin da ya sa aka kiyasta irin wannan tsadar kuɗi, yana mai cewa idan ba motocin alfarma irin su Rolls-Royce Cullinan, Bentley Bentayga, Lamborghini Urus, Ferrari Purosangue ko Mercedes-Maybach GLS 600 aka saya ba, to me ya sa farashin ya kai haka.
A cewarsa:
"Idan ba irin waɗannan motocin alfarma aka saya ba, mene ne ya sa aka saka irin wannan farashi?
"Wane irin Shugaban Kasa ne zai sanya hannu kan kasafin kuɗi mai irin waɗannan alkaluma ba tare da an yi cikakken bincike ba?"
Baya ga batun motocin SUV, Atiku ya kuma yi kira da a bayyana yadda za a kashe Naira biliyan 947.70 da aka ware domin ayyukan ƙarfafa tattalin arziki 2,579. Ya bukaci gwamnati ta bayyana inda za a gudanar da ayyukan, waɗanda za su amfana, 'yan kwangilar da ke aiwatar da su da kuma yadda za a tabbatar an kashe kuɗin jama'a yadda ya dace.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa na neman hada Obi fada da ƙabilarsa, ta fadi yadda zai cutar da su
Atiku ya tabo Tinubu kan tsaro
A baya, mun kawo labarin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da kin fitar da kudaden tsaro da Majalisa ta amince da su wajen aikin da ya dace.
Atiku ya ce sama da mutum 17,000 sun rasa rayukansu tun bayan hawan gwamnatin Tinubu, yana danganta hakan da gazawar aiwatar da kasafin kudin tsaro da aka amince da shi a dokar kasa.
Ya kuma yi alkawarin cewa idan gwamnatin ADC ta hau mulki, za ta gyara tsarin tsaro tare da tabbatar da cewa ana fitar da duk kudaden tsaro a kan lokaci domin ba jami'ai damar aikinsu yadda ya dace.
Asali: Legit.ng

