DSS Ta Kama Yan Kasar Waje da Wasu da ake Zargin Sun Sace Dalibai 300 a Papiri

DSS Ta Kama Yan Kasar Waje da Wasu da ake Zargin Sun Sace Dalibai 300 a Papiri

  • Hukumar DSS ta cafke wasu mutane da ake zargi da safarar makamai ga ‘yan bindigar da suka sace ɗaliban makarantar Katolika ta Papiri a jihar Neja
  • Hukumar tsaron fararen kayan ta gano cewa daga cikin mutanen da ta kama akwai 'yan kasar waje guda biyu da kuma wasu masu alaka da Boko Haram
  • Jami'an sun yi nasarar kwato miyagun makamai da suka hada da bindigu ƙirar AK-103 guda 15, mujallu 15 da harsasai da suka haura 1000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Niger – Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta cafke mutum biyar, da ake zargin suna da hannu a harin da aka kai wata makaranta a jihar Neja kwanakin baya.

Daga cikin mutanen da aka kama har da wasu ‘yan ƙasar Nijar biyu, da ake zargi da safarar makamai ga ‘yan bindigar da suka kai hari makarantar Katolika ta St. Mary’s da ke ƙauyen Papiri a jihar Neja tare sace mutu 300 a watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace tsohon manjo janar da matarsa a Katsina

DSS ta cafke mutum biyar da ake zargi na da hannu a sace daliban Papiri
Wasu daga cikin jam'an hukumar DSS a bakin aiki Hoto: DSS Unofficial
Source: Twitter

The Nation ta kawo labarin cewa wata majiya mai tushe a fannin tsaro ta shaida cewa jami’an DSS sun samu nasarar ƙwato tarin makamai masu yawa daga hannun waɗanda aka kama da suka hada da bindigu ƙirar AK guda 15 da harsasai 1,434.

Yadda jami’an DSS suka kama bata-gari

TVC News ta kawo labarin cewa jami’an tsaro sun fara kama Yusuf Mohammed wanda aka fi sani da Bature tare da abokinsa Mubarak Ibrahim a kan babbar hanyar Zariya zuwa Kaduna yayin da suke kan hanyarsu ta karɓar makamai domin kai wa shugabanninsu.

Majiyar ta bayyana cewa Yusuf Mohammed yana cikin jerin mutanen da hukumomi ke nema ruwa a jallo bisa zargin kasancewa 'dan kungiyar Boko Haram da suka addabi jama'a.

Bayan wannan kamen, jami’an DSS sun gudanar da wani samame wanda ya kai ga cafke Goni Ibrahim, wanda ake zargin fitaccen mai safarar makamai ne daga yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar.

Kara karanta wannan

"Ina tsaro a Kano?" Aminu Gwarzo ya dura a kan gwamantin Abba

An kuma kama Tukur Sani tare da shi saboda zargin haɗin gwiwa a harkar kuma suna da hannu a harin da aka kai wata makaranta a jihar Neja.

DSS ta gano alakarsu da satar Papiri

Bayan kwanaki kaɗan da waɗannan kamun, jami’an tsaro sun sake cafke wani da ake kira Alhaji Adamu, wanda aka fi sani da Gado Banufe, a garin Yauri da ke jihar Kebbi da ake zargi aikata laifuffuka a yankin.

Majiyar tsaron ta ce binciken farko ya nuna cewa mutanen biyar da aka kama suna cikin wata ƙungiyar masu safarar makamai da ke kai wa ‘yan bindigar da suka kai hari makarantar kwana ta Katolika da ke Papiri kayan yaƙi.

An sace dalibai, malamai da ma'aikatan makarantar Papiri a 2025
Taswirar jihar Neja inda aka sace dalibai sama da 300 a 2025 Hoto: Legit.ng
Source: Original

A safiyar ranar 21 ga Nuwamba, 2025, daruruwan ‘yan bindiga dauke da makamai sun kutsa cikin makarantar firamare da sakandare ta Katolika, inda suka tattara ɗalibai da malamai ƙarƙashin barazanar bindiga.

An ceto daliban Papiri a jihar Neja

A baya, kun samu labarin cewa gwamnatin tarayya ta tabbatar da kuɓutar ɗalibai da malamai 230 na makarantar St. Mary’s Catholic da ke Papiri, Jihar Neja da aka sace a jihar Neja.

Kara karanta wannan

Zargin fyade" ADC ta fara bore bayan kotu ta tasa 'keyar da takararta zuwa kurkuku

Sanarwar da Ma'aikatar yada labarai ta fitar ta bayyana cewa an mika dalibai 130 da aka ceto ga gwamnatin jihar kafin a haɗa su da 'yanuwansu bayan sun kwashe lokaci a hannun yan bindiga.

Mamallakin makarantar da aka kwashe masa dalibai, Rabaran Bulus Dauwa Yohanna, ya tabbatar da isowar ɗaliban a Minna yayin da iyaye da sauran yan uwansu ke cikin tashin hankali a lokacin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng