Taraba: Bayan na Tsagin Wike, Tsohon Minista Ya Samu Tikitin Neman Gwamnan PDP

Taraba: Bayan na Tsagin Wike, Tsohon Minista Ya Samu Tikitin Neman Gwamnan PDP

  • Tsohon Ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Sanata Joel Ikenya, ya lashe zaɓen fitar da gwani na gwamnan PDP a Taraba
  • Ikenya ya yi alƙawarin farfaɗo da tattalin arziki, inganta ababen more rayuwa da jawo masu zuba jari idan ya zama gwamnan Taraba
  • Dan takarar ya musanta cewa akwai rikicin ɓangarori a PDP ta Taraba, yana mai cewa jam'iyyar tana haɗe domin kwato mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jalingo, Taraba - Tsohon Ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Sanata Joel Ikenya, ya samu tikitin takarar gwamna a PDP bayan zaben fitar da gwani.

Ikenya ya zama wanda ya lashe zaɓen fitar da gwani na gwamna da ɓangaren jam'iyyar PDP karkashin jagorancin Turaki ya gudanar a Taraba.

Tsohon minista ya samu tikitin takara a PDP
Shugaban tsagin PDP, Tanimu Turaki da Joel Ikenya da aka ba takarar gwamna a Taraba. Hoto: Kabiru Tanimu Turaki.
Source: Facebook

Yawan kuri'un da Ikenya ya samu

Kara karanta wannan

'Ba mu da zabi': Nyesom Wike ya yi magana kan sake zaben Tinubu a 2027

Shugaban kwamitin zaɓen, Honorabul Felix Hassan Hyat, ne ya sanar da sakamakon a Jalingo, inda ya bayyana cewa Sanata Ikenya ya samu ƙuri'u 34,173, cewar Tribune.

Hyat ya ce Ikenya ya doke abokin takararsa, Mista David Usman Dinshiya, wanda ya samu ƙuri'u 4,853 a zaɓen fidda gwanin da aka gudanar.

Ya bayyana cewa an gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci, tare da yabawa kwamitin gudanarwar PDP na Taraba kan yadda aka gudanar da shi cikin lumana.

Tsagin Turaki ya fitar da dan takarar gwamna
Shugaban tsagin PDP, Tanimu Turaki. Hoto: Kabiru Tanimu Turaki.
Source: Twitter

Alkawuran da Sanata Ikenya ya yi

Da yake jawabi bayan nasarar, Sanata Joel Ikenya ya yi alƙawarin sake farfaɗo da Taraba tare da dawo da martabar jihar idan aka zaɓe shi gwamna.

Ya ce zai sauya Taraba daga tattalin arzikin da ya dogara da albashi zuwa jihar da masana'antu za su bunƙasa tare da samar da ayyukan yi.

Ikenya ya ƙara da cewa yana da burin farfaɗo da ababen more rayuwa a jihar tare da jawo masu zuba jari domin ƙarfafa tattalin arziki, cewar Punch.

Ya ce:

"Zan sauya Taraba. Zan mayar da ita daga tattalin arzikin albashi zuwa tattalin arzikin masana'antu mai ƙarfi."

Kara karanta wannan

Bayan watsi da jam'iyyar APC, 'dan Nasir El Rufai ya tashi da tikiti a ADC

Dan takarar gwamnan ya kuma musanta zargin cewa akwai wata ɓangarantar PDP a Taraba, yana mai cewa babu wata jam'iyyar PDP daban a jihar.

Ikenya ya ce PDP ɗaya ce kacal a Taraba kuma dukkan mambobinta suna aiki tare a matsayin iyali guda domin kwato mulki daga gwamnatin Gwamna Kefas ta APC.

Rahotanni sun nuna cewa a makon da ya gabata, ɓangaren PDP karkashin jagorancin Nyesom Wike ya ayyana Sanata Emmanuel Bwacha a matsayin ɗan takararsa na gwamna a Taraba.

Na kusa da Wike ya samu takara

Mun ba ku labarin cewa wani na kusa da Nyesom Wike kuma dan majalisar tarayya, Kingsley Chinda, ya lashe tikitin takarar gwamnan APC da aka yi a Rivers.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa hakan ya biyo bayan kasancewarsa shi kadai a zaɓen fitar da gwani da aka yi.

Chinda, da ke da alaka da Nyesom Wike, ya yi alƙawarin gudanar da mulki cikin gaskiya, tsoron Allah da bin doka idan aka zaɓe shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.