'Dan Uwan Fubara Ya Fito Neman Takarar Gwamna Ribas, Ya Yi wa Jama'a Alkawari
- Ɗan’uwan gwamnan jihar Ribas, Ambasada Blessing Fubara Senior, ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a jam’iyyar NDC
- Ya fito takarar ne bayan 'dan uwansa, Siminalayi Fubara ya rasa damar sake neman takara a babban zabe mai zuwa a inuwar APC
- Fubara ya janye daga neman takarar ne awanni kadan kafin zaben fitar da gwani, lamarin da ake ganin yana da alaka da rikicinsa da Nyesom Wike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Rivers - Ambasada Blessing Fubara Senior, ɗan’uwan gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar gwamnan jihar ƙarƙashin jam’iyyar NDC.
Ya bayyana hakan ne gabanin zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar, inda ya bayyana kansa a matsayin ɗan takara mai ƙwarewa, ƙarfi da kuma jajircewa wajen dawo da zaman lafiya da bunƙasar tattalin arziƙi a jihar Rbas.

Kara karanta wannan
'Dan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya samu tikitin takarar gwamna a zaben 2027

Source: Facebook
Jaridar Punch ta kawo labarin cewa Fubara ya ce jihar Ribas ta yi asarar damammaki da jarin masu zuba hannun jari sakamakon rikice-rikicen siyasa da suka dabaibaye jihar a ‘yan shekarun nan.
Ribas: 'Dan uwan Fubara ya fito takarar gwamna
Da yake jawabi ga magoya bayansa, Blessing Fubara ya ce lokaci ya yi da mutanen Ribas za su haɗa kai domin dawo da martabar jiharsu, kamar yadda The Sun Nigeria ta wallafa.
Ya ce:
“Mun rasa damammaki, mun rasa kudin masu zuba hannun jari, mun rasa martabarmu da kuma alfaharinmu a matsayin mutanen Ribas.”
Ɗan takarar ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi a matsayin gwamna, zai mayar da hankali wajen dawo da zaman lafiya da bunƙasa tattalin arziƙin jihar.

Source: Facebook
Haka kuma, ya jaddada cewa dole ne a ci gaba da bin tsarin karɓa-karɓar mulki tsakanin yankunan sanatoci na jihar, yana mai cewa dole ne a bar yankin Kudu maso Gabas na Ribas ya kammala wa’adinsa na shekara takwas.
A cewarsa:
“Ba mu yarda a mai da mu kamar waɗanda aka ci da yaƙi ba. Lokaci ya yi da za mu dawo da jihar Ribas zuwa matsayin da aka santa a matsayin taskar arzikin ƙasa.”
Alkawarin Fubara Snr. ga mutanen Ribas
Blessing Fubara ya kuma bayyana cewa ya shirya yin wa’adi guda ɗaya ne kawai na shekara huɗu domin bai wa wani yanki damar karɓar mulki bayan kammala wa’adinsa a jihar ta Ribas.
Ya ce:
“Na yi alƙawarin yin wa’adi ɗaya kacal na shekara huɗu domin kawo ci gaba da wadata a jihar Ribass. Bayan haka, za mu mara wa ɗan’uwa na gaba baya domin ya fito daga wani yankin sanatoci.”
Ribas: Makusancin Wike ya samu takara
A baya, mun kawo labarin cewa na kusa da Nyesom Wike kuma dan majalisar tarayya, Kingsley Chinda, ya lashe tikitin takarar gwamnan APC da aka yi a jihar Ribas bayan wasu sun janye bukatarsu.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa hakan ya biyo bayan kasancewarsa shi kadai a zaɓen fitar da gwani da aka yi, wanda ya ba shi damar fito wa a matsayin dan takara ba tare da hamayya ba.
Chinda, da ke da alaka da Nyesom Wike, ya yi alƙawarin gudanar da mulki cikin gaskiya, tsoron Allah da bin doka idan aka zaɓe shi a babban zabe mai zuwa bayan Tinubu ya ki mara wa Siminalayi Fubara baya
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

