'Dan Marigayi Sheikh Dahiru Usamn Bauchi Ya Samu Tikitin Takarar Gwamna a Zaben 2027

'Dan Marigayi Sheikh Dahiru Usamn Bauchi Ya Samu Tikitin Takarar Gwamna a Zaben 2027

  • Jam'iyyar APGA ta ayyana 'dan marigayi Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin dan takarar gwamnan jihar Bauchi a babban zaben 2027 da ke tafe
  • Shugaban APGA na jihar Bauchi, Ibrahim Dantalle, ne ya sanar da hakan ranar Alhamis, inda ya bayyana kwarin gwiwar kan Naziru Dahiru Bauchi
  • Ɗan takarar ya yi alƙawarin samar da shugabanci na gaskiya da riƙon amana tare da bai wa matasa da mata muhimmanci idan aka zabe shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Nigeria - Jam’iyyar APGA ta tabbatar da Naziru Sheikh Dahir Usman Bauchi a matsayin ɗan takararta na gwamna a jihar Bauchi gabanin zaɓen shekarar 2027.

Shugaban jam’iyyar APGA na jihar Bauchi, Ibrahim Dantalle, ne ya sanar da hakan ranar Alhamis, inda ya bayyana kwarin gwiwar jam’iyyar na samun nasara a zaɓen da ke tafe.

Kara karanta wannan

Atiku ya bayyana tsare tsarensa game da Najeriya bayan lashe tikitin ADC

Dantalle ya ce APGA ta dade tana siyasa a Najeriya kuma ta samu nasarori a jihohi daban-daban na ƙasar nan tsawon shekaru, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Ya bayyana cewa jam’iyyar na da cikakken shiri na tsayawa takara a dukkan mukaman siyasa a jihar Bauchi a zaɓen 2027, domin neman karɓe ragamar mulki da sauran kujerun siyasa.

A cewarsa, jam’iyyar ta gabatar da sahihin ɗan takara mai ƙwarewa, Naziru Tahir Bauchi, wanda ya bayyana a matsayin matashi mai himma da hangen nesa wajen kawo ci gaba mai ma’ana.

Ya ƙara da cewa sauran masu neman tikitin gwamna a jam’iyyar sun janye da kansu tare da amincewa da goyon bayan Naziru saboda ƙwarewarsa, cancantarsa da kuma halayen shugabanci da yake da su.

Ɗan Sheikh Dahiru Bauchi ya yi alkawari

A jawabinsa na karɓar tikitin takarar Naziru, wanda ɗa ne ga fitaccen malamin addinin Musulunci marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yi alkawarin sauya fasalin jihar Bauchi zuwa cibiyar kasuwanci da bunƙasar tattalin arziƙi idan aka zaɓe shi.

Ya gode wa shugabannin jam’iyyar da mambobinta bisa yarda da suka nuna masa, yana mai tabbatar da cewa APGA za ta bai wa manyan jam’iyyun siyasa a jihar ƙalubale mai ƙarfi a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Zaben ADC: Atiku Abubakar ya shiga gaba, ya samu gagarumar nasara a jihohi 5

“Burina na zama gwamna ya samo asali ne daga ƙudirin samar da shugabanci nagari, bunƙasa tattalin arziƙi, ƙarfafa matasa, tabbatar da adalci da bai wa kowa dama iri ɗaya a jihar Bauchi,” in ji shi.

Ɗan takarar ya yi alƙawarin samar da shugabanci na gaskiya da riƙon amana tare da bai wa matasa da mata muhimmanci ta hanyar shirye-shiryen ci gaba masu ɗorewa.

A cewarsa, idan ya zama gwamna zai mayar da hankali wajen samar da ayyukan yi, rage talauci, gyaran ilimi, inganta kiwon lafiya, bunƙasa noma da karkara, tsaro, gine-ginen more rayuwa da gyaran birane.

Haka kuma ya yi alkawarin ƙarfafa mata da tabbatar da adalci da gaskiya a shugabanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262