An Kawar da Fubara, na Kusa da Wike Ya Samu Tikitin Takarar Gwamna
- Na kusa da Nyesom Wike kuma dan majalisar tarayya, Kingsley Chinda, ya lashe tikitin takarar gwamnan APC da aka yi a Rivers
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa hakan ya biyo bayan kasancewarsa shi kadai a zaɓen fitar da gwani da aka yi a ranar Alhamis
- Chinda, da ke da alaka da Nyesom Wike, ya yi alƙawarin gudanar da mulki cikin gaskiya, tsoron Allah da bin doka idan aka zaɓe shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - An gudanar da zaben fitar da gwanin APC a ranar Alhamis 21 ga watan Mayun shekarar 2026 da muke ciki.
Dan majalisar wakilai mai wakiltar Obio/Akpor, Kingsley Chinda, ya zama ɗan takarar gwamnan APC a Rivers domin zaɓen shekarar 2027.

Source: Facebook
Shugaban kwamitin zaɓen fitar da gwani, Bitrus Kwamoti, ya bayyana cewa Chinda ya samu kuri’u 268,497 a zaɓen da aka gudanar, cewar TheCable.
Rivers: Dan majalisar tarayya ya samu tikitin takara
Chinda tsohon shugaban marasa rinjaye ne a majalisar wakilai kuma yana daga cikin na kusa da ministan Abuja, Nyesom Wike wanda ke rikici da Gwamna Sim Fubara tun bayan hawansa mulki.
Da yake magana bayan kammala zaɓen, Chinda, wanda na kusa ne da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce idan aka zaɓe shi gwamna zai yi mulki cikin “tsoron Allah da mutunta doka.”
“Al’ummar Rivers su sa ran shugabanci mai gaskiya da cikakken riƙon amana. Jihar Rivers mai zaman lafiya da ci gaba na dawowa kuma."
Ya kuma yi alƙawarin samar da shugabanci mai gaskiya tare da tabbatar da adalci da ci gaba ga al’ummar jihar Rivers baki ɗaya.

Source: Instagram
Musabbabin da ya sa Fubara ya janye daga takara
A ranar Laraba 20 ga watan Mayun 2026 da muke ciki, Gwamna Siminalayi Fubara da wasu ‘yan takara biyu sun janye daga fafatawar neman tikitin APC na gwamna a jihar.
Fubara ya bayyana cewa ya janye ne domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a Rivers duk da rikicin siyasa da ake fama da shi, cewar Punch.
Kafin zaɓen, APC ta tantance Fubara da Chinda yayin da ake rade-radin cewa an cire wasu magoya bayan gwamnan daga takara.
Rikicin siyasa tsakanin Fubara da Wike ya daɗe yana ci gaba har ya kai ga yunƙurin tsige gwamnan daga mukaminsa a baya.
Yawancin ‘yan majalisar Rivers da suka goyi bayan yunƙurin tsige Fubara ana kallonsu a matsayin magoya bayan Nyesom Wike a jihar.
ADC ta ba mazaunin Amurka takara a jam'iyyar
A baya, kun ji cewa wani dan siyasa mazaunin Amurka ya samu tikitin takarar dan majalisar tarayya daga jihar Abia.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Emeka Bahadur, ya zama ɗan takarar ADC na mazabar Ikwuano/Umuahia ta tarayya gabanin zaɓe mai zuwa.
Jam’iyyar ADC ta amince da Bahadur ta hanyar masalaha bayan mambobi sun amince da tsarin kaɗa kuri’ar murya wajen zaɓen.
Asali: Legit.ng

