'Yan APC Sun Yi wa Peter Obi Rubdugu da Ya Tabo Bola Tinubu

'Yan APC Sun Yi wa Peter Obi Rubdugu da Ya Tabo Bola Tinubu

  • Fadar Shugaban Ƙasa da Sanata Adams Oshiomhole sun soki Peter Obi bayan hirarsa ta talabijin inda ya yi suka ga shugaba Bola Tinubu
  • Mai ba shugaban ƙasa shawara, Bayo Onanuga, ya ce Obi ya sha sauya jam'iyyu, yana mai cewa tafiyarsa ta siyasa ba ta yi kama da ta Tinubu ba
  • Oshiomhole kuma ya zargi Obi da rashin fahimtar tattalin arzikin Najeriya, yana mai kare manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Fadar shugaban kasa da Sanatan Edo ta Arewa, Adams c, sun mayar da martani mai zafi ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi.

Hakan na zuwa ne bayan kalaman da Peter Obi ya yi game da shugaba Bola Ahmed Tinubu yayin da ake tunkarar zaben 2027.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta hango kura kurai a kalaman Obi, ta yi masa zazzafan martani

Dan takarar shugaban kasa, Peter Obi
Peter Obi da yake yi wa NDC takarar shugaban kasa a Najeriya. Hoto: Mr Peter Obi.
Source: Facebook

The Nation ta rahoto cewa martanin ya biyo bayan hirar da Obi ya yi a tashar Channels TV ranar Lahadi, inda ya yi suka kan salon mulkin Tinubu tare da bayyana ra'ayinsa kan tafiyar shugaban ƙasar a fagen siyasa.

Onanuga ya ragargaji Obi

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Peter Obi yana ƙoƙarin kwatanta sauya jam'iyyunsa da tafiyar siyasar Tinubu ne domin farfaɗo da burinsa na takarar shugaban ƙasa a 2027.

Onanuga ya bayyana cewa tafiyar siyasar Tinubu ta kasance cikin tafarkin masu ra'ayin ci gaba tun daga jam'iyyar SDP, zuwa AD, AC, ACN har zuwa kafa APC.

A sakon da ya wallafa a X, Onanuga ya ce:

"Tinubu ya tsaya kan akidarsa ta siyasa. Ya ci gaba da gina jam'iyyun da ya shiga maimakon ya rika barinsu."

A cewarsa, Obi kuwa ya sauya daga APGA zuwa PDP, daga nan zuwa LP, sannan ADC, kafin daga bisani ya koma NDC.

Kara karanta wannan

Kai mutane Hajji, taimakon almajirai da ayyukan Peter Obi a Arewa

Onanuga ya kuma ce ya kamata Obi ya amince da hukuncin Kotun Ƙoli kan zaɓen shugaban ƙasa na 2023, maimakon ci gaba da ikirarin cewa shi ne ya yi nasara.

Ya ce:

"Obi, lokaci ya yi da za ka amince da gaskiyar cewa ka sha kaye. Ka daina mafarkin nasarar da ba ka taɓa samu ba."

Oshiomhole ya caccaki Obi

Shi ma Sanata Adams Oshiomhole ya caccaki Peter Obi, yana mai cewa tsohon gwamnan Anambra bai fahimci yadda tattalin arzikin Najeriya ke aiki ba.

Oshiomhole ya ce maimakon Obi ya samar wa 'yan Najeriya ayyukan yi, yana taimakawa wajen fitar da ayyukan zuwa ƙasashen waje.

Ya kuma kare manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, yana mai cewa duk da wahalhalun farko da aka fuskanta sakamakon sauye-sauyen da aka yi, ƙasar na fara komawa kan hanya madaidaiciya.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu a ofis. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Obi ya buƙaci Tinubu ya yi ritaya

A wani labarin, mun ruwaito cewa Peter Obi ya buƙaci shugaba Bola Tinubu ya janye daga takarar zaɓen 2027, yana mai cewa shugaban ƙasar ya gaji kuma ba shi da ƙarfin magance matsalolin Najeriya.

Kara karanta wannan

Magana ta fito kan zargin Obasanjo ya yi wa Tinubu aiki, an hada Obi da Kwankwaso

Obi ya bayyana a wata hira da ya yi cewa Tinubu na yanzu ba shi ne mutumin da ya jagoranci Legas a baya ba, yana mai cewa ya kamata a bar shi ya yi ritaya cikin kwanciyar hankali.

Ya kuma yi zargin cewa Najeriya na tafiya ta hanyar da ba ta dace ba, yana mai cewa ƙasar na buƙatar shugaba mai kuzari da zai iya sauya alkiblar tattalin arziki da tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng