Gwamna Fubara Ya Hakura da Takara, Ya Janye daga Zaben Fitar da Gwanin APC

Gwamna Fubara Ya Hakura da Takara, Ya Janye daga Zaben Fitar da Gwanin APC

  • Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya hakura da neman tazarce karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulki a zaben 2027
  • Fubara ya bayyana cewa ya janye daga shiga zaben fitar da gwanin APC, wanda aka shirya yi a gobe Alhamis, 21 ga watan Mayu, 2026
  • Ya gode wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da magoya bayansa, yana mai cewa ya dauki wannan matakin ne saboda kishin Rivers

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers, Nigeria - Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya janye daga shiga zaben fitar da dan takarar gwamna APC, wanda aka shirya gudanarwa ranar Alhamis.

Fubara ya ce bayan dogon tunani da tattaunawa da iyalansa, abokai da makusantansa, ya yanke shawarar janyewa daga neman takara domin amfanin jihar Rivers.

Gwamna Fubara.
Gwamnan jihar Rivers, Sir Siminalayi Fubara yana sa hannu kan wasu takardu a gidan gwamnatinsa da ke Fatakwal Hoto: Sir. Siminalayi Fubara
Source: Facebook

Daily Trust ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai taken “matakina na janyewa daga zaben fidda gwani na gwamnan jihar Rivers” da Fubara ya sanya wa hannu da kansa a daren Laraba,

Kara karanta wannan

"Ku tashi tsaye ku kare kan ku daga ƴan bindiga," Hadimin Tinubu ga ƴan Najeriya

Gwamna Fubara ya tabbatar da cewa yana nan daram a APC, kuma zai mara wa duk wanda ya samu tikitin jam’iyyar baya a zaben 2027.

Dalilin Gwamna Simi Fubara na janyewa

“Jagoranci yana bukatar sadaukarwa. Akwai lokacin da dole a birne burin kashin kai domin maslahar jama’a. Jihar Rivers ta fi kowanne mutum muhimmanci,” in ji shi.

Ya kara da cewa a wannan lokaci mai muhimmanci, zaman lafiya, kwanciyar hankali da hadin kai su ne ya kamata su kasance gaba da duk wani buri na siyasa.

Fubara ya gode wa magoya baya

Gwamnan ya gode wa magoya bayansa bisa goyon bayan da suka ba shi tun farkon tafiyar siyasarsa har zuwa wannan lokaci.

Ya ce ya fahimci takaicin da wasu ke ji sakamakon matakin da ya dauka, amma ya jaddada cewa goyon bayan da suka nuna masa ba zai tafi a banza ba.

Fubara ya ce ya fuskanci matsin lamba da abubuwa masu matukar wahala, amma kaunarsa ga jihar Rivers ta fi komai girma.

Gwamna Fubara ya yaba wa Tinubu da APC

Mai girma gwamnan ya kuma gode wa jam’iyyar APC bisa damar da ta ba shi, tare da yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa goyon baya da karfafa masa gwiwa.

Kara karanta wannan

Pantami ya fusata, ya janye daga neman takarar gwamnan Gombe a APC, ya fadi dalili

Ya kuma bukaci magoya bayan APC su ci gaba da kasancewa masu biyayya da hadin kai domin gina makoma mai kyau ga jihar Rivers.

Gwamna Fubara da Tinubu.
Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana gabatar da kasafin kudi a Majalisa Hoto: @SimFubara, @aonanuga1956
Source: Twitter

Shin Gwamna Fubara ya tsorata ne?

A karshe, Gwamna Fubara ya ce janyewarsa daga takarar ba alamar rauni ko tsoro ba ce, face kaunarsa da zaman lafiya da ci gaban jihar.

“Na janye daga zaben fitar da gwanin APV ne saboda sadaukarwa da kishin ganin jihar Rivers ta samu zaman lafiya da hadin kai,” in ji shi.

Ya tabbatar da cewa zai ci gaba da yi wa al’ummar jihar Rivers aiki har zuwa karshen wa’adinsa, kamar yadda tashar channels tv ta ruwaito.

Gwanna Fubara na shirin barin APC?

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, ya yi karin haske game da jita- jitar da ake yadawa wai yana shirin barin jam'iyyar APC mai mulki

Ya ce rahotanni da da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa ya sauya jam’iyya ba gaskiya ba ne ko kadan, yana nan daram a APC.

Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da fifita ayyukan da za su inganta rayuwa da walwalar al’ummar jihar kai tsaye.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262