Bayan Dattawan Kiristoci, Soyinka Ya Dura kan Tinubu kan Kashe Kashe

Bayan Dattawan Kiristoci, Soyinka Ya Dura kan Tinubu kan Kashe Kashe

  • Farfesa Wole Soyinka ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya kawo ƙarshen kashe-kashen da jami'an gwamnati ke yi ba tare da bin doka ba
  • Wanda ya lashe kyautar Nobel ya ce shiru da 'yan Najeriya ke yi kan irin wadannan laifuffuka na ƙara ƙarfafa masu aikata su
  • Soyinka ya sadaukar da laccarsa ta shekarar 2026 ga mutanen da suka mutu sakamakon kashe-kashen ba bisa ka'ida ba da kuma cin zarafin gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Fatakwal – Fitaccen marubuci kuma wanda ya lashe kyautar Nobel, Farfesa Wole Soyinka, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kawo ƙarshen kashe-kashen da jami'an gwamnati ke yi ba tare da bin ka'ida ba.

Soyinka ya bayyana haka ne yayin laccarsa ta 28 da aka gudanar a birnin Fatakwal da ta mayar da hankali kan adalci da inganta rayuwar dan Adam.

Kara karanta wannan

Dattawan Kiristoci sun yi matsaya kan tazarcen Tinubu a zaben 2027

Bola Tinubu da Farfesa Wole Soyinka
Bola Tinubu a hagu da Farfesa Wole Soyinka a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Source: Facebook

Soyinka ya koka kan kashe-kashe

Punch ta wallafa cewa Soyinka ya ce ya sadaukar da laccar ta bana ga mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon kashe-kashen da jami'an gwamnati suka aikata da kuma gazawar tsarin adalci.

Ya ce:

"Na sadaukar da wannan rana ga mazauna Ughelli 18 da jami'an gwamnati suka kashe ba tare da wani dalili ba; ga saurayin da wani ɗan sanda ya harbe da rana tsaka saboda zargi; da kuma Deborah wadda abokan karatunta suka bi suka ƙona da ranta."

Ya ƙara da cewa babban laifin al'umma shi ne yin shiru kan irin waɗannan abubuwa, wanda hakan ke ba masu aikata laifin damar ci gaba da kauce wa hukunci.

Soyinka ya yi kira kan tsarin adalci

The Cable ta rahoto cewa Farfesan ya yi watsi da masu zarginsa da tayar da rikicin addini duk lokacin da ya yi magana kan irin waɗannan abubuwa.

Ya ce irin waɗannan taruka suna da muhimmanci domin tunatar da 'yan Najeriya cewa rayuwar ɗan Adam ita ce abu mafi muhimmanci a cikin kowace al'umma.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Yadda aka kama mutum 2 da zargin cefanar da filayen gwamnatin Kano

Ya kuma bukaci 'yan ƙasa su ci gaba da sa ido kan shari'ar ɗan sandan da ake zargi da harbe wani matashi domin tabbatar da cewa tsarin shari'a bai gaza ba.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Bola Tinubu na yi wa 'yan Najeriya jawabi. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A nasa jawabin, tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Osita Chidoka, ya ce adalci yana farawa tun kafin a shiga kotu.

Ya bayyana cewa 64% na fursunonin da ke gidajen yari a Najeriya, sama da mutum 50,000, na jiran fara shari'a ne ba tare da an same su da wani laifi ba.

Ana so Tinubu ya hakura a 2027

A wani labarin, mun ruwaito cewa Ƙungiyar Dattawan Kiristoci ta Kasa (NCEF) ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da kada ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Ƙungiyar ta bayyana cewa yadda gwamnatin Tinubu ta gudanar da harkokin tsaro, tattalin arziki da walwalar 'yan ƙasa bai gamsar ba.

NCEF ta ce maimakon neman wa'adi na biyu, ya kamata shugaban ƙasar ya mayar da hankali wajen sake fasalin Najeriya da kuma samar da sabon kundin tsarin mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng