Bayanai Sun Fito: An ji dalilin Tinubu da APC na Kin Marawa Fubara Baya domin Takara
- Gwamna Siminalayi Fubara ya rasa goyon bayan Shugaba Bola Tinubu da jam'iyyar APC a Rivers
- Majiyoyin APC sun ce an hana Fubara tikitin takarar gwamna a 2027 saboda yarjejeniyar da ya amince ba zai nemi wa’adi na biyu ba
- Kungiyoyin matasan Kudu maso Kudu da magoya bayan Fubara sun nuna takaici kan janyewarsa daga takara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt - Sababbin bayanai sun bayyana yadda gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara kan dalilin janyewa daga takara.
Majiyoyi sun Fubara ya rasa goyon bayan Shugaba Bola Tinubu da shugabannin APC a rikicin siyasa tsakaninsa da Nyesom Wike.

Source: Twitter
Rahotanni daga Punch sun nuna cewa Fubara ya sabawa yarjejeniyar sulhu da aka cimma tsakaninsu bayan rikicin siyasar jihar ya yi kamari.
Yadda matsalar Wike da Fubara ta munana
Wani mamba na kwamitin gudanarwar APC ya bayyana cewa shugabancin jam’iyyar bai yi wa Fubara tarba ta musamman bayan sauyawa APC ba saboda bai samu amincewar Wike ba.
Ya ce Tinubu ya mika tsarin siyasar Rivers ga Wike, sannan ya shawarci Fubara ya mayar da hankali kan mulki.
Majiyar ta kara da cewa shugaban kasa ya taba ceton Fubara daga yunkurin tsige shi sau biyu, amma daga baya an cimma yarjejeniya cewa ba zai nemi wa’adi na biyu ba.
Ta ce Wike yana yawan fadin “yarjejeniya yarjejeniya ce” saboda Fubara ya taba amincewa da hakan.
Rahotanni sun ce wasu jiga-jigan APC sun yaudari Fubara da alkawarin goyon bayan jam’iyya, alhali shugaban kasa da kungiyar gwamnoni ba sa tare da shi.
Haka kuma an ce an hana duk ‘yan takararsa shiga zaben fitar da gwani na majalisar dokoki da ta tarayya.

Source: Facebook
Dalilin rashin tantance Gwamna Fubara
Wata majiya daga APC a Abuja ta ce kwamitin tantance ‘yan takarar gwamna karkashin jagorancin shugaban jam’iyya, Farfesa Nentawe Yilwatda, bai tantance Fubara ba.
Ta ce ya fusata tare da fita daga wajen tantancewar bayan an sanar da shi cewa ba zai tsaya takara karkashin APC ba, cewar Daily Post.
Wani kusa da Wike ya tabbatar da cewa APC ta hana Fubara tsayawa takara domin mutunta yarjejeniyar da aka cimma tun bayan rikicin siyasar jihar.
Ya ce Fubara ya tsira daga tsigewa ne saboda taimakon Tinubu da Wike, saboda haka dole ya cika alkawarin da ya dauka.
Jam’iyyar APC ta ki shirya wa Fubara tarbar shiga jam’iyya duk da cewa ya koma APC a watan Disambar 2025.
Sauran gwamnoni daga PDP kamar Sheriff Oborevwori da Umo Eno sun samu tarba ta musamman daga shugabannin APC, amma Fubara bai samu irin wannan kulawa ba.
Makusancin Wike ya samu takara
Mun ba ku labarin cewa na kusa da Nyesom Wike kuma dan majalisar tarayya, Kingsley Chinda, ya lashe tikitin takarar gwamnan APC da aka yi a Rivers.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa hakan ya biyo bayan kasancewarsa shi kadai a zaɓen fitar da gwani da aka yi.
Chinda, da ke da alaka da Nyesom Wike, ya yi alƙawarin gudanar da mulki cikin gaskiya, tsoron Allah da bin doka idan aka zaɓe shi.
Asali: Legit.ng

