Kurunkus: Kotu Ta Kawo Karshen Shari'ar Jonathan kan Takarar Shugaban Kasa a 2027

Kurunkus: Kotu Ta Kawo Karshen Shari'ar Jonathan kan Takarar Shugaban Kasa a 2027

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukunci game da karar da aka shigar gabanta na neman hana tsohon shugaban kasa takara a 2027
  • Wani lauya mai suna Johnmary Jideobi ya nemi kotu ta hana Jonathan shiga takara, amma kotun ta yi watsi da bukatar a hukuncin da aka yanke a yau
  • Alƙali Peter Lifu ya hukunta cewa kundin tsarin mulkin Najeriya bai hana Jonathan sake neman kujerar shugaban ƙasa ba duk da yunkurin wasu na hana hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta yanke hukuncin cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, na da cikakkiyar damar shiga takarar shekarar 2027.

Hukuncin ya zo ne bayan wata taƙaddama da ta taso kan ko tsohon shugaban ƙasar zai iya sake neman kujerar shugaban ƙasa ƙarƙashin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

NDC ta yi zargin wasu shugabanninta na karbar na goro domin tsayar da 'dan takara

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar Goodluck Jonathan
Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, gudumar kotu a hannun dama Hoto: Stringer/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

A ruwayar Daily Trust, a kwanakin baya ne wani ɓangare na PDP ƙarƙashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki ta amince da Jonathan a matsayin dan takarar shugaban kasar jam'iyyar..

An kai Goodluck Jonathan kara gaban kotu

Politics Nigeria ta kawo labarin cewa Sai dai wani lauya da ke zaune a Abuja mai suna Johnmary Jideobi ya garzaya kotu domin neman a hana Jonathan bayyana kansa ga kowace jam’iyya a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.

Lauyan ya kuma roƙi kotun ta hana Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC karɓa ko wallafa sunan Jonathan a matsayin ɗan takara a zaɓen shugaban ƙasa.

Kotu ta ce Gooluck Jonathan zai iya tsaya wa takara a zaben 2027
Tsohon shugaban kasa Gooluck Jonathan a wani taron UN Hoto: Goodluck Jonathan
Source: Getty Images

Mai shari’a Peter Lifu, wanda ya saurari ƙarar, ya bayyana a hukuncinsa ranar Talata 26 ga watan Mayu, 2026 cewa Jonathan har yanzu yana da cancantar tsayawa takarar shugaban ƙasa bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin shekarar 1999.

Kotun ta yi nazari kan sassa na 1(1), 1(2), 1(3) da kuma 137(3) na kundin tsarin mulkin Najeriya kafin ta yanke hukuncin.

Kara karanta wannan

'Dan gwagwarmaya Sowore ya fito takarar shugaban kasa, zai kara da Tinubu a 2027

Jonathan zai iya tsaya wa takara - Kotu

Alƙalin ya ce babu wani sashe da ya hana tsohon shugaban ƙasar sake neman kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Hukuncin na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da tattaunawa da rade-radin siyasa kan yiwuwar Jonathan komawa takarar shugaban ƙasa bayan shekaru da barin mulki.

Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin hukuncin zai iya ƙara ɗaga zazzafar siyasar 2027, musamman a cikin jam’iyyun adawa da ke ƙoƙarin sake tsara dabarunsu kafin babban zaɓen ƙasar.

Obi ya magantu kan takarar Jonathan

A baya, mun kawo labarin cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a LP, Peter Obi ya yi magana game da zaben shekarar 2027 da ake tunkara nan gaba yayin da ake kara samun masu neman kujerar Bola Tinubu.

Mista Peter Obi ya bayyana cewa ko kadan bai damu da rade-radin cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2027 ba, domin akwai inda hankalinsa ya karkata.

Kara karanta wannan

"Ni ma na rame": Tinubu ya amince manufofinsa sun jefa ƴan Najeriya a wahala

Ya bayyana cewa hankalinsa na wajen hada kan Najeriya, inganta tsaro, farfado da tattalin arziki da kuma dakile cin hanci domin rayuwar jama’a ta gyaru yayin da ake sa ran zai hada kai da Rabiu Musa Kwankwaso

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng