Sojoji Sun Yi Gumurzu Sun Ceto Babban Sojan Najeriya da aka Sace
- Rundunar sojin Najeriya ta ceto wani babban jami'in soja da aka sace tare da wani farar hula bayan gudanar da samame na kwanaki 10 a jihar Enugu
- An gano mutanen biyu a gefen wani daji bayan matsin lambar da dakarun hadin gwiwa suka ci gaba da yi wa masu garkuwa da mutane
- Rahotanni sun nuna cewa masu garkuwar sun tsere tare da barin wadanda suka sace yayin da bincike ke ci gaba domin cafke su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Enugu – Rundunar hadin gwiwar sojojin Najeriya ta samu nasarar ceto wani babban jami'in soja, Laftanar Kanar Ofor Amobi, da wani farar hula mai suna Ikechukwu Onwuanra bayan kwanaki 10 ana gudanar da samame domin gano inda suke.
An gudanar da aikin ceton ne da sanyin safiyar ranar 1 ga watan Agusta bayan dakarun Operation UDO KA sun ci gaba da matsa wa masu garkuwa da mutane lamba.

Source: Facebook
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa aikin ya samu nasara ne sakamakon hadin gwiwar rundunonin soja daban-daban tare da taimakon rundunar sojin saman Najeriya.
Sojoji sun ceto sojan Najeriya
Rahotanni sun nuna cewa tsakanin yammacin ranar 31 ga watan Yuli da safiyar 1 ga watan Agusta, dakarun sun gudanar da samame a dazukan Inyi, Awlaw da Akpugo-Eze da wasu kauyuka da ke karamar hukumar Oji River.
Da misalin karfe 2:00 na dare, jami'in 'yan sanda mai kula da sashen Inyi ya sanar da sojojin inda ake zargin wadanda aka sace suke.
Nan take dakarun suka kutsa cikin yankin, inda suka gano Laftanar Kanar Amobi da Mista Onwuanra a gefen wani daji bayan masu garkuwar sun bar su a wurin.
An bayyana cewa farar hular ya samu raunin harbin bindiga, inda aka garzaya da su zuwa Inyi kafin daga bisani a kai su Asibitin Sojoji domin kula da lafiyarsu.
Me wadanda aka ceto suka ce?
A yayin tambayoyin farko, mutanen biyu sun bayyana cewa masu garkuwar sun rufe musu idanu tun bayan sace su tare da kai su wani wuri da ba su sani ba.
Sun ce daga baya masu garkuwar sun bar su a wani daji da ke iyakar jihohin Enugu da Anambra bayan matsin lambar da jami'an tsaro suka ci gaba da yi musu.

Source: Original
Majiyoyin soji sun ce ci gaba da sintiri a kasa da kuma sa ido ta sama ya hana masu garkuwar samun damar motsi, lamarin da ya tilasta musu guduwa tare da barin wadanda suka sace.
An kuma bayyana cewa ana ci gaba da bincike da kuma farautar wadanda suka aikata satar domin gurfanar da su a gaban doka.
Nesanta Musulunci da ta'addanci
A wani labarin, mun ruwaito cewa Farfesa Safiyanu Ishiaku ya sake jaddada cewa Musulunci bai halatta tilasta wa mutane karbar addinin Musulunci ko kashe wadanda ba Musulmi ba.
Ya bayyana hakan ne yayin gabatar da lakca a jami'ar Gombe, inda ya ce yawancin rikice-rikicen da ake dangantawa da addini a Najeriya suna samo asali ne daga bukatun siyasa, kabilanci da tattalin arziki.
Farfesan ya kara da cewa masu aikata ta'addanci da sunan Musulunci suna tafiya ne sabanin koyarwar addinin, wanda ya ginu a kan zaman lafiya da hakuri.
Asali: Legit.ng


