Kano: Kotu Ta Yanke Hukunci kan Amaryar da Ta Kashe Mijinta Kwanaki 9 da Aurensu

Kano: Kotu Ta Yanke Hukunci kan Amaryar da Ta Kashe Mijinta Kwanaki 9 da Aurensu

  • Babbar Kotun Kano ta yanke wa Saudat Jibrin hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunta da laifin kashe mijinta kwana tara kacal bayan aure
  • Kotun ta ce an tabbatar ba tare da shakka ba cewa Saudat ta ba mijinta gubar zobo kafin ta kai masa hari da wuƙa
  • Lauyan gwamnati ya yaba da hukuncin, yana mai cewa ya nuna kudirin gwamnatin Kano na tabbatar da adalci ga duk masu karya doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Kano - Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wata mata mai shekara 19, Saudat Jibrin, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunta da laifin kashe mijinta, Salisu Idris, kwana tara kacal bayan aurensu.

Mai shari'a Maryam Sabo ce ta yanke hukuncin ranar Alhamis bayan shari'ar da ta ɗauki watanni 14, inda ta ce masu gabatar da ƙara sun tabbatar da laifin ba tare da wata shakka mai ma'ana ba.

Kara karanta wannan

Dattawan Kiristoci sun yi matsaya kan tazarcen Tinubu a zaben 2027

Kotu ta yanke hukunci kan Saudat Jibrin da ta kashe mijinta a Kano
Sandar girma da alkalai ke amfani da ita a kotu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An yanke wa amarya hukuncin kisa

Saudat, mazauniyar ƙaramar hukumar Kumbotso a jihar Kano, ta gurfana a gaban kotu ne bisa tuhumar kisan kai bayan kama ta da aka yi a watan Mayun 2025, in ji rahoton Channels TV.

A hukuncinta, Mai shari'a Maryam Sabo ta ce girman laifin ya dace da hukuncin mafi tsauri da doka ta tanada.

Ta bayyana cewa irin waɗannan hukunce-hukunce na taimakawa wajen hana wasu aikata irin wannan laifi a gaba.

Sai dai kotun ta sanar da Saudat cewa tana da damar ɗaukaka ƙara cikin wa'adin da doka ta tanada.

Yadda ake zargin ta kashe mijinta

Lauyan gwamnati, Lamido Abba Sorondinki, ya shaida wa kotu cewa Saudat ta sanya guba a cikin abin shan zobo da mijinta ke sha kafin daga bisani ta kai masa hari da wuƙa da misalin ƙarfe tara na dare a ranar da lamarin ya faru.

A cewarsa, wannan hari ne ya yi sanadin mutuwar Salisu Idris, lamarin da ya sa jami'an tsaro suka fara bincike har aka kama Saudat tare da gurfanar da ita a gaban kotu, kamar yadda Legit Hausa ta taba rahotowa.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Yadda aka kama mutum 2 da zargin cefanar da filayen gwamnatin Kano

Gwamnati ta gabatar da shaidu biyu domin tabbatar da tuhume-tuhumen, tana mai cewa laifin ya saɓa da sashe na 221(a) na dokar Penal Code.

Lauyan amarya ya nemi sassauci

Yayin kare wanda ake tuhuma, lauyanta Abdulfatah Muhammad ya roƙi kotu da ta yi amfani da tausayi wajen yanke hukunci.

Ya ce Saudat ta nuna alamun sauya hali yayin da take tsare, inda ta haddace Alƙur'ani mai girma a lokacin da take gidan yari.

Har ila yau, ya bayyana cewa ita ce babbar 'ya a gidansu kuma tana taka muhimmiyar rawa wajen kula da ƙannenta, saboda haka ya roƙi kotun da ta yi mata afuwa.

Gwamnatin Kano ta yi martani

Da yake martani kan hukuncin, Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari'a na Jihar Kano, Abdulkarim Kabiru Maude (SAN), ya bayyana hukuncin a matsayin babban ci gaba wajen tabbatar da adalci a jihar.

An samu Saudat Jibrin da laifin kashe mijinta a Kano, an yanke mata hukuncin kisa.
Taswirar jihar Kano inda aka yanke wa wata mata hukuncin kisa kan kashe mijinta. Hoto: Legit.ng
Source: Original

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Maude ya yabawa lauyan gwamnati, Lamido Abba Sorondinki, bisa ƙwarewa da jajircewar da ya nuna wajen gudanar da shari'ar.

Ya ce hukuncin ya nuna ƙudirin gwamnatin jihar Kano na tabbatar da cewa duk wanda ya karya doka zai fuskanci hukunci ba tare da la'akari da matsayinsa ba.

Kara karanta wannan

Ribadu: "Dabarar gwamnati na yaki da ta'addanci ya fara murkushe yan bindiga"

Lamarin ya jawo hankalin jama'a sosai saboda mutuwar Salisu Idris ta faru ne cikin ƙasa da makonni biyu bayan da ma'auratan suka ɗaura aure.

Matar aure ta kashe mijinta

Tun da fari, mun ruwaito cewa, wata matar aure a jihar Delta ta kashe mijinta da budurwarsa bayan ta yi amfani da adda da guduma wajen fasa masu kai.

Rundunar yan sanda ta kama matar bayan ta raunata makwabciyarta wadda ta yi kokarin shiga tsakani domin ceton ran mijin.

A jihar Ondo ma wata matar ta fasa wa mijinta kai da tabarya sakamakon zargin cin amana wanda hakan ya janyo mutuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com