Za a Fatata a Kaduna, ADC Ta Fitar da Dan Takara da Zai Kara da Uba Sani
- Tsohon dan majalisar tarayya daga Kaduna, Isah Ashiru Kudan ya samu tikitin takarar gwamna a jihar karkashin ADC mai hamayya
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa hakan ya biyo ne bayan zaben fitar da gwani da aka gudanar a fadin jihar inda ya samu dubban kuri'u
- Sai dai tsohon Kwamishinan Ilimi na jihar Kaduna ya yi watsi da sakamakon zaben, yana mai cewa an tafka magudi da karkatar da kuri’u a wasu yankuna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Tsohon dan majalisar tarayya a mazabar Makarfi/Kudan, Isah Ashiru Kudan ya samu nasarar zama dan takarar gwamna a Kaduna.
Ashiru ya samu takarar a karkashin jam’iyyar ADC a jihar Kaduna bayan kammala zaben fitar da gwani na jam’iyyar a fadin jihar baki daya.

Source: Facebook
Jimillar kuri'u da Isah Ashiru ya samu
Premium Times ta ce Ashiru ya samu jimillar kuri’u 86,113 daga dukkan mazabu da kananan hukumomi na jihar Kaduna.
Majiyoyi suka ce hakan ya nuna karfin goyon bayansa a tsakanin ‘yan jam’iyya da masu kada kuri’a da kuma alamar samun daman nasara a 2027.
Sai dai wani tsohon Kwamishinan Ilimi na jihar Kaduna, Jafaru Sani wanda ya zo na biyu da kuri’u 29,580, ya yi watsi da sakamakon zaben.
Ya bayyana cewa an shirya shi ne tare da tafka magudi da karkatar da sakamakon a lokacin gudanar da zaben fidda gwani, ya ce ba a gudanar da gaskiya a wasu wurare ba.
Sauran ‘yan takara sun hada da Mohammed Sani Bello da ya samu kuri’u 13,559, Ahmed Tijjani da ya samu 13,550, da Shuaibu Mikati da ya samu 10,819.
Isah Ashiru ya taba zama dan takarar gwamna na PDP a 2019 da 2023, inda ya kara samun karbuwa a siyasar adawa ta jihar Kaduna.
Haka zalika tsohon 'dan majalisar ya nemi tikitin APC, amma Nasir El-Rufai ya yi galaba a kan shi a 2014.

Kara karanta wannan
Atiku ya lallasa yan takara 2, ya samu nasara a zaben fitar da gwanin ADC a Sakkwato

Source: Original
Jafaru Sani ya yi watsi da sakamakon zaben
Jafaru Sani ya yi watsi da sakamakon da aka bayyana, yana mai cewa an tafka magudi domin fifita Hon. Ashiru, cewar Daily Post.
Ya ce:
“Dukkanmu mun san cewa ba a gudanar da zabe ba a wurare da dama, sannan wasu sakamakon ma ba su kammala ba lokacin da aka sanar da sakamakon.”
Tsohon kwamishinan ya ambaci kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Kaduna ta Arewa da Kauru a matsayin wuraren da ake zargin har yanzu ba a kammala tattara sakamakonsu ba kafin sanarwar.
Ya kara da cewa:
“Mun samu labarin cewa an kafa kwamitin da zai sake duba sakamakon, ya daidaita tsarin tare da sauraron korafe-korafenmu.”
Gombe: Tinka ya zama dan takarar gwamnan ADC
A baya, mun ba ku labarin cewa jam'iyyar adawa ta ADC ta sanar da wanda zai yi mata takarar gwamnan Gombe bayan kammala zaben fitar da gwani da aka gudanar.
Rahotanni sun nuna cewa Alhaji Bala Bello Tinka ne ya lashe kujerar takarar gwamna a karkashin jam'iyyar ADC a jihar Gombe a 2027.
Dr Bala Bello Tinka dan kasuwa ne da ya ke harkokin siyasa kuma ya sha neman takara a matakai daban-daban a shekarun baya a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

