Atiku vs Amaechi: ADC Ta Sanar da Sakamakon Zaben Fitar da 'Dan Takarar Shugaban Kasa a Kano

Atiku vs Amaechi: ADC Ta Sanar da Sakamakon Zaben Fitar da 'Dan Takarar Shugaban Kasa a Kano

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar na ci gaba da samun nasara a zaben fitar da gwanin jam'iyyar adawa ta ADC
  • Shugaban kwamitin zaɓen, John Ayuba, ya ce Atiku ya samu nasara a Kano da ƙuri’u 155,595 yayin da Rotimi Amaechi ya samu ƙuri’u 9,994
  • Wannan na zuwa ne bayan Atiku ya samu nasara a jihohi biyar, lamarin da ya sa ya shiga gaban sauran masu neman takarar shugaban kasa a inuwar ADC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya lashe zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a Jihar Kano.

Shugaban kwamitin zaɓen, John Ayuba, ya bayyana cewa an gudanar da zaɓen a dukkan ƙananan hukumomi 44 da kuma gundumomi 484 na jihar.

Kara karanta wannan

2026: Muhimman abubuwa da Tinubu Ya Fadawa 'Yan Najeriya a Sakon Barka da Sallah

Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a taron kaddamar da hadaka a ADC a Abuja Hoto: @Atiku
Source: Facebook

Yadda sakamakon ya kasance a Kano

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa bisa ga sakamakon da aka tattara daga kananan hukumomin Kano, Atiku ya samu ƙuri’u 155,595.

Masanin tattalin arziki, Mohammed Hayatu-Deen ya zo na biyu da ƙuri’u 15,914, yayin da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya samu ƙuri’u 9,994.

Dr Ayuba ya ce za a tura sakamakon zuwa cibiyar haɗa sakamakon zaɓe ta jam’iyyar a Abuja domin tantancewa da kuma ayyana ɗan takarar shugaban ƙasa a hukumance.

Atiku Abubakar ya shiga gaba a zaben ADC

Ya kuma buƙaci mambobin jam’iyyar su ci gaba da haɗa kai domin tabbatar da ADC ta samar da shugaban Najeriya na gaba.

Wannan na zuwa ne bayan Atiku ya samu nasara a jihohi biyar, lamarin da ya sa ya shiga gaban sauran masu neman takarar shugaban kasa a inuwar ADC da mafi rinjayen kuri'u.

Kara karanta wannan

Zaben ADC: Atiku Abubakar ya shiga gaba, ya samu gagarumar nasara a jihohi 5

Daga cikin jihohin da tsohon mataimakin shugaban kasar ya lashe akwai Sakkwato, Gombe, Abia, Zamfara da Ebonyi.

Shin ADC ta tsaida dan takarar gwamna?

A daya ɓangaren kuma, jam’iyyar ta dakatar da sanar da sakamakon zaɓen fitar da gwani na takarar gwamnan jihar Kano har sai shugabancin jam’iyyar ADC na ƙasa ya yanke hukunci.

Jamiyyar ADC
Tambarin jam'iyyar hadakar yan adawa a Najeriya, ADC Hoto: ADC Party
Source: Twitter

Ana fafatawar ne tsakanin Ibrahim Ali Amin Little da Ibrahim Khalil, yayin da jam’iyyar ke nazarin yiwuwar amfani da tsarin maslaha domin zaɓen ɗan takararta.

Jam'iyyar ADC ta dakatar da sanar da sakamakon ne saboda takaddamar da ta biyo baya, inda a yanzu uwar jam'iyya ta kasa za ta yanke hukuncin karshe.

Atiku ya yi nasara a jihar Sakkwato

A wani labarin, kun ji cewa Alhaji Atiku Abubakar ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben fitar da 'dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC da aka gudanar a jihar Sakkwato.

Sakamakon da aka bayyana a jihar Sakkwato, ya nuna cewa Atiku ya kayar da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi da masanin tattalin arziki, Mohammed Hayatu-Deen.

Atiku Abubakar ya samu ƙuri’u 68,823, Rotimi Amaechi, ya samu ƙuri’u 292, yayin da Muhammad Hayatuddeen ya samu ƙuri’u 319.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262