'Fulani ba 'Yan Ta'adda ba ne,' Sarkin Musulmi Ya Yi Magana kan Matsalar Tsaro
- Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya ce bai dace a rika kiran masu garkuwa da "Fulani makiyaya" ba
- Ya ce Fulani a shirye suke su hada kai da gwamnati wajen korar masu aikata miyagun ayyuka daga matsugunansu
- A hannu daya, kungiyar Fulani ta MACBAN ta sake yin Allah wadai da ta'addanci, garkuwa da mutane da satar shanu a kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Abuja - Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa bai kamata a ci gaba da danganta laifukan garkuwa da mutane, ta'addanci da fashi da makami da Fulani makiyaya ba.
Mai alfarma sarkin ya yi nuni da cewa duk wanda ya aikata irin waɗannan laifuka, ya aikata laifi ne kawai ba tare da la'akari da ƙabilarsa ba.

Source: Twitter
A daina kiran Fulani 'yan ta'adda
Sarkin ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin buɗe taron ƙasa na shekarar 2026 nakungiyar Fulani ta MACBAN da aka gudanar a Abuja, in ji rahoton Tribune.
Sarkin ya bukaci 'yan Najeriya su daina amfani da kalmar "Fulani makiyaya" wajen bayyana masu garkuwa da mutane da 'yan ta'adda.
A cewarsa, ya kamata a rika kiran su da sunansu na gaskiya, wato masu aikata laifuffuka.
Sarkin ya ce:
"Ku kira su masu laifi da ke garkuwa da mutane, ta'addanci da sauran miyagun ayyuka. A kowace iyali akwai nagari da kuma marasa nagarta. Ni ina cikin iyalin mutanen kirki."
Ya kara da cewa miliyoyin Fulani masu zaman lafiya bai kamata su fuskanci zargi saboda ayyukan wasu tsiraru masu aikata laifi ba.
Fulani za su taimaka wajen yakar 'yan bindiga
Sarkin Musulmin ya tabbatar wa gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro cewa Fulani a shirye suke su hada kai domin gano da kuma korar masu aikata laifuffuka daga matsugunansu.
"Muna tabbatar wa Shugaban Kasa da sauran masu ruwa da tsaki cewa a shirye muke dari bisa dari mu yi aiki tare da gwamnati da jami'an tsaro domin korar masu laifi daga yankunanmu."
- Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III.
Ya yaba da kafa Ma'aikatar Raya Kiwo
Sarkin ya yabawa Shugaba Bola Tinubu kan kafa Ma'aikatar Raya Kiwo, yana mai cewa matakin zai taimaka wajen bunkasa bangaren kiwo a Najeriya.
Haka kuma ya yaba da kwamitin sauye-sauyen kiwo karkashin jagorancin Farfesa Attahiru Jega, yana mai tabbatar da goyon bayan sarakunan gargajiya ga shirye-shiryen ma'aikatar.
Ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya da su yi kokarin fahimtar juna domin karfafa zaman lafiya da hadin kai, in ji rahoton The Nation.

Source: Twitter
MACBAN ta sake yin Allah wadai da ta'addanci
Tun da farko, shugaban kungiyar MACBAN na kasa, Baba Othman Ngelzarma, ya sake yin Allah wadai da ta'addanci, garkuwa da mutane, fashi da makami da satar shanu.
Ya ce bai kamata a rika hukunta wata kabila ko sana'a saboda ayyukan wasu tsiraru masu aikata laifi ba.
A cewarsa, matsalar tsaro ita ce babbar barazana ga makiyaya da manoma, domin hare-haren masu laifi sun jawo asarar rayuka, raba iyalai da muhallansu da kuma lalata hanyoyin samun abin rayuwa a sassan Najeriya.
Taimakon sarkin Musulmi ga gwamnatin Tinubu
A wani labari, mun ruwaito cewa, uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yabawa Sarkin Musulmin Najeriya Muhammadu Sa’ad Abubakar.
Sarkin Musulmi ya bukaci shugabanni su ci gaba da neman taimakon Allah kan matsalar masu aikata ta'addanci, tare da addu'ar su tuba su rungumi zaman lafiya.
Gwamnan Sokoto Ahmad Aliyu da Sarkin Musulmi sun yabawa shirin Renewed Hope Initiative, suna cewa ya amfani mata, matasa, yara da iyalai a fadin Najeriya.
Asali: Legit.ng


