Peter Obi Ya Magantu kan 'Barazanar' Jonathan ga Takararsa da Kwankwaso

Peter Obi Ya Magantu kan 'Barazanar' Jonathan ga Takararsa da Kwankwaso

  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a LP, Peter Obi ya yi magana game da zaben shekarar 2027 da ake tunkara nan gaba
  • Obi ya bayyana cewa ko kadan bai damu da rade-radin cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2027 ba
  • Ya bayyana cewa hankalinsa na kan hada kan Najeriya, inganta tsaro, farfado da tattalin arziki da kuma dakile cin hanci domin rayuwar jama’a ta gyaru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, ya tabo batun takarar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Peter Obi ya yi watsi da rade-radin cewa Goodluck Jonathan, na iya zama barazana ga burinsa na takarar shugaban kasa a 2027.

Obi ya yi magana kan 'takarar' Jonathan a 2027
Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi da Sanata Rabi'u Kwankwaso bayan komawa NDC. Hoto: Mr. Peter Obi.
Source: Facebook

Obi ya bayyana hakan ne bayan tantancewar da jam’iyyar NDC ta yi masa a sakatariyarta da ke Abuja, cewar Punch.

Kara karanta wannan

2027: Martanin Kwankwaso ga zargin yana yi wa Tinubu aiki a NDC

Obi ya magantu kan takarar Jonathan a 2027

Da yake mayar da martani kan rahotannin cewa Jonathan na iya shiga takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Obi ya ce bai damu da wadanda za su tsaya takara ba.

Ya ce dimokuradiyya tana bai wa mutane damar neman mukami domin yi wa kasa hidima, sannan jama’a su zabe su bisa cancanta.

Obi ya bayyana cewa babban burinsa shi ne hada kan Najeriya, tabbatar da tsaro da farfado da tattalin arziki.

Ya ce dole ne gwamnati ta yi aiki bisa kundin tsarin mulki, musamman wajen tabbatar da daidaito da bai wa kowa dama.

Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a 2023 ya bayyana tsawon lokacin tantancewar a matsayin “dimokuradiyya a aikace.”

Ya ce jam’iyyar NDC ta dauki matakin ne domin tabbatar da gaskiya, cancanta da bin ka’ida wajen tantance masu neman takara da takardunsu.

Peter Obi ya fadi bangaren da zai gyara a Najeriya
Tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Peter Obi. Hoto: Mr Peter Obi.
Source: Twitter

Da gaske an tsayar da Obi takara?

Obi ya kuma yi watsi da rahotannin cewa ya zama dan takarar shugaban kasa na bai daya a jam’iyyar bayan tuntuba da shugabanni.

Kara karanta wannan

An dora Hayatu Deen a gaban Atiku, Obi da Amaechi a takarar zama shugaban kasa a 2027

Ya ce har yanzu jam’iyyar na sayar da fom din nuna sha’awa da na takara, don haka babu wani matsaya kan dan takara guda daya tukuna.

Ya nuna damuwa kan karuwar talauci da rashin tsaro a kasar, yana cewa mutane da dama na kwana ba tare da sanin inda abincin gobe zai fito ba.

Obi ya ce dole ne a kawo karshen amfani da dukiyar jama’a domin anfani na kashin kai tare da yaki da cin hanci yadda ya kamata, cewar Vanguard.

Ya ce yayin da mutane ke fama da matsaloli da mutuwa, wasu shugabanni suna ta shirye-shiryen zabe kawai, abin da ya ce dole ne ya tsaya.

Kwankwasiyya za ta yi wa Kwankwaso, Obi gata

A wani labarin, an ji cewa maasoyan tsofaffin ƴan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso sun fara shirin neman mafita game da zaben 2027.

Ƴan Kwankwasiyya da Obidienta suna shirin haɗa kai domin takarar shugaban ƙasa a 2027, suna ganin haɗin gwiwa zai kayar da jam’iyya mai mulki.

Jagoran Obidient Movement, Yunusa Tanko, ya ce magoya baya za su tara miliyoyi domin sayen fom ɗin takarar haɗaka ta Obi da Kwankwaso.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.