NDC Ta Yi Zargin Wasu Shugabanninta na Karbar na Goro domin Tsayar da 'Dan Takara

NDC Ta Yi Zargin Wasu Shugabanninta na Karbar na Goro domin Tsayar da 'Dan Takara

  • Wani ɓangare na jam’iyyar NDC a jihar Enugu ya roƙi shugabancin ƙasa ya shiga tsakani kan rikicin shugabanci da ke neman kassara ta
  • Dr. Johnpaul Anih ya ce shi ne halastaccen shugaban jam’iyyar da aka zaɓa ta hanyar sahihin taro, amma an samu masu kawo masa matsaloli
  • Ya kuma yi zargin ana karɓar kuɗi daga masu neman takara ta wata hanya da ba ta dace ba, lamarin da ke kara dagula masu al'amura

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Enugu - Wani ɓangare na jam’iyyar NDC a Enugu ya nemi shugabannin jam’iyyar na ƙasa su shiga tsakani domin warware rikicin shugabanci da ya kunno kai a reshen jihar.

Jagoran ɓangaren, Dr. Johnpaul Anih, ya bayyana hakan ne ranar Litinin 25 ga watan Mayu, 2026 yayin wani taron manema labarai da ya gudanar.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Kotu ta kawo karshen shari'ar Jonathan kan takarar shugaban kasa a 2027

Jam'iyyar NDC ta shiga rikici
Alamar jam'iyyar NDC mai adawa a Najeriya Hoto: Nigeria Democratic Congress
Source: Facebook

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Dr. Jonpaul Ani ya bayyana cewa shi ne halastaccen shugaban jam’iyyar da aka samu ta hanyar sahihin babban taro.

Rikici ya danno NDC a reshen Enugu

Rahoton ya ce sai dai wani jigo a jam’iyyar mai suna Ibuchukwu Obetta ya shaida a baya cewa shi ne cikakken shugaban jam’iyyar a jihar.

Obetta ya yi iƙirarin cewa an riga an warware duk matsalolin shugabanci da suka shafi jam’iyyar a yayin babban taron ƙasa da aka gudanar a Abuja.

Amma Anih ya ce sahihan tarurrukan jam’iyyar da aka gudanar a jihar ne suka kai ga babban taron da aka yi a dakin taro na Aborigen Hall da ke Enugu, inda aka zaɓe shi a matsayin shugaban jam’iyyar.

Ana zargin wasu a NDC da karban kudi don bayar da takara
Jagoran NDC na ƙasa, Serieke Dickson a wajen wani taron jam'iyya Hoto: Henry Serieke Dickson
Source: Facebook

Ya ce kwamitin da shugabancin ƙasa ya kafa ne ya gudanar da taron, tare da halartar jami’an tsaro, wakilan hukumar INEC da kuma kafafen yaɗa labarai.

A cewarsa, suna da hujjojin bidiyo da ke nuna yadda aka gudanar da sahihin taron da ya samar da shi da sauran 'yan kwamitinsa.

Kara karanta wannan

2027: Mohammed Abacha ya sha kaye, PDP ta tsaida dan takarar gwamna a jihar Kano

An fara zargin cin hanci a NDC

Dr. Anih ya kuma zargi wasu mutane da ƙoƙarin ƙwace tsarin jam’iyyar ta hanyoyin da suka saɓa wa kundin tsarin mulki, lamarin da ya ce ya haddasa ruɗani a cikin jam’iyyar a jihar.

Haka kuma ya zargi sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam’iyyar, Mista Osa Director, da wallafa abin da ya kira mummunan bayani a kansa, daga ciki har da zargin damfara da kuma yin karya da sunan wani.

Ya ƙalubalanci kakakin jam’iyyar da ya kawo hujjar zargin cewa ya sayar da fam ɗin tsayawa takara ko na nuna sha’awa ga masu neman takara.

Anih ya kuma yi zargin cewa ana tilasta wa wasu masu neman takara biyan kuɗi har N400,000 zuwa wani asusun mutum ɗaya wanda ake zargin wani shugaban riƙo ke sarrafawa.

Ya ce ya aika wasiƙu ga shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Seriake Dickson, tare da kwafin wasiƙar ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a 2027, Mista Peter Obi, domin neman a shiga tsakani.

Kara karanta wannan

An kashe mutum 8 bayan dan majalisa ya bada kyautar miliyoyin Naira a jihar Neja

Ya buƙaci sauran yan jam’iyyar da masu neman takara a jihar su amince da shugabancinsa kaɗai, yana mai cewa za su ci gaba da shirye-shiryen zaɓen fitar da gwani kamar yadda shugabancin ƙasa ya umarta.

Jam'iyyar NDC ta samu karuwa

A baya, mun kawo labarin cewa Hon. Mustapha Dawaki, tsohon shugaban ma'aikata na shugaban APC na kasa ya tabbatar da sauya sheka daga jam'iyya mai mulki zuwa NDC a jihar Kano.

Jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma jigo a NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne ya tarbe shi a gidansa da ke Miller Road a jihar Kano a ranar Talata, 26 ga watan Mayu 2026.

'Dan siyasar ya bar APC ne bayan rasa tikicin komawa Majalisar tarayya sakamakon tsarin sulhun da aka yi amfani da shi, wanda ya kara karfin siyasar jam'iyyar hamayya a jihar Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng