Auren Dole: Yadda Mahaifi Ya Lakadawa 'Yarsa Duka har Ta Mutu a Katsina
- ‘Yan sanda a jihar Katsina sun fara bincike kan mutuwar wata yarinya mai suna Ummul Khair da ake zargin mahaifinta ya yi mata duka har ta rasu
- Rahotanni sun ce yarinyar ta yi ta kin amincewa da yunkurin mahaifinta na aurar da ita ga mutumin da ya zaba mata
- Majiyoyi sun bayyana cewa an gano gawarta ne lokacin da wasu kawayenta suka je gidansu domin su tafi makaranta tare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta fara bincike kan mutuwar wata yarinya mai suna Ummul Khair, wadda ake zargin mahaifinta ya yi mata duka har ta rasu.
An kama wanda ake zargin, Kabir Sani, wanda direban mota ne kuma mazaunin yankin Shagari Low-Cost da ke cikin birnin Katsina.

Source: Original
Mazauna yankin sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa ana kyautata zaton Ummul Khair tana tsakanin shekara 16 zuwa 18.
Sun ce yarinyar ta yi ta kin amincewa da yunkurin mahaifinta na aurar da ita ga mutumin da ya zaba mata, lamarin da suka ce ya haifar da rikici a tsakaninsu.
An ji kukan yarinyar
A cewar wasu shaidu, ana zargin mahaifin ya fara dukan ‘yarsa ne a ranar Laraba, 29 ga watan Yulin shekarar 2026.
Makwabta sun ce sun fara shiga damuwa bayan sun ji kukan yarinyar, inda suka rika kwankwasa kofar gidan domin su shiga tsakani.
Sai dai ana zargin Kabir Sani ya ki bude musu kofar gidan ko ya bari wani ya shiga.
Rahotanni sun ce dukan ya ci gaba har zuwa safiyar ranar Alhamis, 30 ga watan Yulin 2026 lokacin da yarinyar ta suma.
An gano abin da ya faru ne bayan wasu daga cikin kawayen Ummul Khair sun je gidansu da safiyar Alhamis domin su tafi makaranta tare.
An ce sun tarar da ita babu rai, yayin da mahaifinta ke shirin yi mata sutura domin jana’izarta. Nan take suka sanar da makwabta, wadanda daga bisani suka kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda.
Wata majiya ta ce:
“Mun ji tana kuka a tsawon dare, kuma mun yi kokarin shiga tsakani sau da dama, amma mahaifinta ya ki bude kofar gidan. Da safiyar Alhamis ne muka ji cewa ta rasu. Kowa a unguwar ya shiga cikin jimami.”
An yi jana’izarta a Katsina
Wani mazaunin yankin ya ce yarinyar ta dage cewa tana son ta yanke shawara da kanta kan makomarta. Sai dai ya ce mahaifinta ya tsaya tsayin daka kan aurar da ita ga mutumin da ya zaba mata.
An yi jana’izar Ummul Khair da safiyar ranar Alhamis a makabartar Abbatoir da ke cikin birnin Katsina, bisa tsarin addinin Musulunci.

Source: Facebook
Me 'yan sanda suka ce?
Wasu majiyoyin ‘yan sanda sun tabbatar da cewa Kabir Sani yana tsare a ofishin ‘yan sandan Kasuwar Central ta Katsina. Ana ci gaba da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru da yarinyar.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, DSP Sadik Aliyu, ya ce ya san da faruwar lamarin. Sai dai ya ce zai bayar da karin bayani bayan kammala binciken da ake yi.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: An hango yadda malaman makaranta masu yawa za su ajiye aiki a Borno
Sardaunan Sokoto ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Dattijon ɗan siyasa kuma tsohon jami'in diflomasiyyar, Abubakar Alhaji ya yi bankwana da duniya.
Marigayin wanda ya taba zama babban kwamishinan Najeriya a Birtaniya ya rasu ne da safiyar ranar Alhamis 29 ga watan Yuli, 2026 a wani asibiti da ke Abuja.
Asali: Legit.ng

