"Ka GujI Tarko": Sule Lamido Ya Shawarci Jonathan game da Takarar Shugaban Kasa
- Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya yi fatali da kiraye-kirayen da ake yi wa Goodluck Jonathan kan ya tsaya takarar shugaban kasa a 2027.
- Sule Lamido, wanda jigo ne a PDP da ake ganin Jonathan zai iya neman takara a cikinta ya ce kiran ya samo asali ne daga takaicin halin da siyasar Najeriya ke ciki
- Tsohon gwamnan ya gargadi Jonathan da kada ya bari yabon mutane ko neman faranta masa rai ya sa ya koma siyasar jam’iyya yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Jigawa– Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana cewa bai dace tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya shiga takarar shugaban kasa ta shekarar 2027 ba.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 20 ga watan Mayu, 2026 Sule Lamido ya bayyana kiran da ake yi wa Jonathan da ya dawo siyasa a matsayin takaicin jama'a kan halin da kasa ke ciki.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta ruwaito cewa jigon jam’iyyar PDP ya ce ana iya maraba da dawowar Jonathan harkar siyasa, amma ba a wannan lokaci ba, musamman duba da yanayin siyasar Najeriya a yanzu.
Sule Lamido ya yabi Jonathan
Jaridar The Guardian ta kawo labarin cewa Sule Lamido, wanda ya taba rike mukamin ministan harkokin waje, ya ce Jonathan yana da matsayi mai daraja a cikin Najeriya da ma duniya baki daya saboda kasancewarsa tsohon shugaban kasa.
Ya ce bai kamata a jawo Jonathan cikin abin da ya kira gurbatacciyar siyasar Najeriya mai cike da mutane marasa akida da masu neman abin da za su mora kawai.
A cewarsa:
“Tsohon shugaban kasa Jonathan ya san matsayinsa a Najeriya a matsayin jagora kuma tsohon shugaban kasa da ake mutunta wa."

Source: Facebook
Ya kara da cewa:
“Haka kuma yana cikin jerin manyan tsofaffin shugabannin duniya. Bai dace a jawo shi cikin wannan gurbatacciyar siyasa mai cike da masu son kansu ba.”
Sule Lamido ya gargadi Jonathan
Alhaji Sule Lamido ya ce lokacin da aka fara wannan kira bai dace ba, musamman ganin cewa ana dab da rufe karbar takardun neman mukamai gabanin babban zaben 2027.
Ya bayyana cewa masu neman Jonathan ya dawo siyasa na iya yin hakan ne saboda yadda jama’a ke jin rashin kwarin gwiwa da gajiya da halin da kasa ke ciki.
Sule Lamido ya kuma gargadi Jonathan da cewa ya kamata tsohon shugaban kasar ya ci gaba da kare mutuncinsa da matsayinsa na dattijo mai kishin kasa.
Ya ce:
“Dole Jonathan kada ya fada tarkon wannan kiraye-kirayen. Za mu iya adana shi domin wata bukatar kasa a gaba."
Jonathan zai yi takarar shugaban kasa
A baya, mun ruwaito cewa ana ta rade-radi dangane da batun yiwuwar takarar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, a zaben farkon shekarar 2027 yayin da jama'a ke neman ya dawo.
Wani hadimi ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Wealth Dickson Omimim-Imagwa, ya yi watsi da jita-jitar da ke alaƙanta tsohon shugaban na Najeriya da tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP.
Ya bayyana cewa babu wata shaida da ke nuna cewa tsohon shugaban ƙasar yana neman tsayawa takarar shugaban ƙasa ko kuma ya amshi wani tayin takarar shugaban ƙasa a cikin jam’iyyar PDP.
Asali: Legit.ng

