Hukumar Makaranta Ta Hango Babbar Matsala, An Dakatar da Karatu a Jami'ar Jos
- Hukumar Jami’ar Jos ta dakatar da dukkan karatu tare da gayyatar ɗalibai zuwa taron gaggawa domin tattauna matsalolin tsaro
- Matakin ya biyo bayan gano gawar wani manomi da aka sare masa kai da kuma mutuwar wani ɗalibi bayan dukan da jama'a suka yi masa
- Shugaban jami’ar ya ce taron zai mayar da hankali kan hanyoyin kare rayuka da tabbatar da zaman lafiya a cikin jami’ar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Filato - Hukumar Jami'ar Jos ta dakatar da dukkan harkokin karatu tare da gayyatar ɗalibai zuwa wani taron gaggawa saboda ƙarin matsalolin tsaro da suka kunno kai a ciki da wajen jami'ar.
Hukumar ta bayyana cewa za a dakatar da karatu na ɗan lokaci domin tabbatar da cewa dukkan ɗalibai sun halarci taron.

Source: Twitter
Tashe tashen hankula da aka samu

Kara karanta wannan
Minista ya cire tsoro, ya fadi babban abin da ke rura wutar ta'addanci a Najeriya
Matakin ya zo ne yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a cikin al'ummar jami'ar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Rahotanni sun nuna cewa wannan taro ya zo ne kusan makonni biyu bayan gano gawar wani manomi da aka sare wa kai a gonarsa da ke cikin harabar dindindin ta jami'ar.
Haka kuma, mako guda bayan wannan al'amari, wasu fusatattun mutane sun yi wa wani ɗalibi mai suna Ibrahim Mbaya dukan tsiya har ya rasu a wani gida da ke wajen harabar jami'ar, bisa zargin satar wayar hannu.
Shugaban jami'a ya yi bayani
A cikin wata sanarwar cikin gida da mataimakin shugaban jami'ar, Farfesa Ishaya Tanko, ya sanya wa hannu ranar Laraba, ya bayyana cewa za a gudanar da taron ranar Juma'a.
Ya ce an shirya taron ne domin ƙarfafa doka da oda a ciki da wajen jami'ar.
Sanarwar ta ce:
"Dangane da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan waɗanda ke barazana ga zaman lafiya, tsaro da kuma kyakkyawan sunan Jami'ar Jos, na amince da kiran wannan muhimmin taro tare da dukkan ɗaliban jami'ar."
Abin da za a tattauna a taron

Source: Original
Farfesa Ishaya Tanko ya ce taron zai mayar da hankali kan matsalolin tsaro da ke addabar jami'ar, wasu halaye marasa kyau da suka shafi ɗalibai, da kuma hanyoyin haɗin gwiwa wajen kare lafiyar kowa a cikin jami'ar.
Ya ce:
"Babbar manufar wannan taro ita ce tattauna matsalolin tsaro da ke cikin al'ummar jami'a, abubuwan da ba su dace ba da suka shafi wasu ɗalibai, tare da tsara matakan haɗin gwiwa domin kare rayuwa da walwalar dukkan mambobin jami'ar."
Asali: Legit.ng
