Bala Bello Tinka Ya Samu Takarar Gwamna a ADC a Gombe
- Jam'iyyar adawa ta ADC ta sanar da wanda zai mata takarar gwamna a jihar Gombe bayan kammala zaben fitar da gwanai da aka gudanar
- Rahotanni sun nuna cewa Alhaji Bala Bello Tinka ne ya lashe kujerar takarar gwamna a karkashin jam'iyyar ADC a jihar Gombe a 2027
- Dr Bala Bello Tinka dan kasuwa ne da ya ke harkokin siyasa kuma ya sha neman takara a matakai daban-daban a shekarun baya a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - Wani dan kasuwa kuma dan siyasa, Dr Bala Bello Tinka, ya lashe tikitin takarar gwamna na jam’iyyar ADC a jihar Gombe.
Rahotanni sun bayyana cewa Dr Bala Bello Tinka ya samu tikitin takarar ne bayan zaben fitar gwani da aka gudanar ranar Litinin.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa jami’in da ya jagoranci zaben ya ce Tinka ya zama dan takarar gwamna na jam’iyyar ADC ta hanyar amincewar mambobin jam’iyyar.
Bayanin dan takarar ADC a Gombe
Da yake jawabi jim kadan bayan ayyana shi a matsayin dan takarar jam’iyyar, Bala Tinka ya nuna godiyarsa bisa amincewa da kuma yarda da mambobin jam’iyyar suka nuna masa.
Dr Bala Bello ya yi magana yana mai cewa idan aka zabe shi, zai yi duk mai yiwuwa domin cika alkawarin da aka daura masa.
Ya yi alkawarin samar da shugabanci nagari tare da aiwatar da ayyukan da suka shafi rayuwar talakawa kai tsaye idan ya yi nasara a zabe.
Hadimin Atiku Abubakar mai suna Abdul Rashid ya tabbatar da cewa Dr Bala Bello ne ya yi nasara a zaben fitar da gwanin a wani sako da ya fitar a X.
Tinka ya nemi takara a Gombe baya
Bala Bello Tinka ya taba neman tikitin takarar Sanata mai wakiltar yankin Gombe ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC a shekarar 2022.
Amma Dr Bala ya sha kaye a hannun Sanata Saidu Ahmed Alkali, wanda daga baya tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Hassan Dankwambo, ya kayar a babban zabe.
Bala Bello ne ya jagoranci kungiyar yakin neman zabe mai suna ‘Neighbour-to-Neighbour’, wadda ta samar da tsarin siyasa ga Ibrahim Dankwambo a shekarar 2015.

Source: Facebook
Masu lura da al’amuran siyasa da dama sun yi imanin cewa kungiyar ta taimaka wa Dankwambo wajen tsallake guguwar APC da ta kwace kujerun gwamnoni 16 a jihohin Arewa.
Wannan ne karo na farko da Tinka ya zama dan takarar wata babbar jam’iyya domin shiga babban zabe, wani mataki da ke nuna babban sauyi a siyasar Gombe gabanin babban zaben shekarar 2027.
Gwamna zai yi wa APC takara
A wan labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta sanar da cewa Dr Jamilu Isiyaku Gwamna ne zai yi mata takarar gwamna a jihar Gombe.
Hakan na zuwa ne bayan kammala zaben fitar da gwani da jam'iyyar ta gudanar a kananan hukumomi 11 da ke fadin jihar a makon da ya wuce.
Tun kafin shiga zaben fitar da gwanin, Sheikh Isa Ali Pantami da Sanata Saidu Ahmed Alkali da suka saye fom din neman takara sun sanar da janyewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


