Kashim Shettima Ya Dawo Bakin Aiki kafin Hutunsa Ya Kare

Kashim Shettima Ya Dawo Bakin Aiki kafin Hutunsa Ya Kare

  • Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya dawo Abuja bayan hutun makonni biyu, kwanaki biyu kafin ranar da aka tsara zai dawo
  • Shettima ya dawo Najeriya da yammacin Talata, 18 ga Agusta, kamar yadda jami’an ofishinsa suka tabbatar
  • Dawowarsa ta zo a ranar da aka fara yakin neman zaɓe gabanin zaɓen 2027, amma bai halarci taron FEC na ranar Laraba ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya dawo Najeriya bayan hutun makonni biyu da ya tafi.

Kashim Shettima ya koma Abuja ne kwanaki biyu kafin ranar 20 ga Agusta, 2026 da aka tsara zai dawo bakin aiki.

Shettima ya dawo Najeriya
Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima Hoto: Kashim Shettima
Source: Twitter

An tabbatar da dawowar Shettima

Wasu manyan jami’an da ke aiki tare da Mataimakin Shugaban Ƙasar sun tabbatar wa jaridar The Punch cewa Shettima ya dawo Abuja da yammacin Talata, 18 ga Agusta, 2026.

Kara karanta wannan

FAAC ta cika aljihun gwamnatin Tinubu da jihohi, an raba abin da ba a taba samu ba

“Ya dawo jiya da yamma,” in ji wani jami’i ranar Laraba.

Wani hadimi shi ma ya tabbatar da cewa, “Muna sa ran dawowarsa tun jiya. Ya dawo bakin aiki.”

Bai halarci taron FEC ba

Sai dai Shettima bai halarci taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) na ranar Laraba ba, wanda Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a zauren majalisar da ke Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja.

Dawowar Mataimakin Shugaban Ƙasar da wuri ta zo ne a daidai lokacin da aka fara yakin neman zaɓe a ranar 19 ga Agusta, gabanin zaɓen 2027, kamar yadda Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar.

Hutun farko tun 2023

Shettima ya tafi hutun makonni biyu ne a ranar 6 ga Agusta, 2026, bisa amincewar Shugaba Tinubu. Wannan shi ne hutunsa na farko tun bayan rantsar da shi a matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya dace a sani game da yarjejeniyar da aka yi tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya

A cikin wata sanarwa da Stanley Nkwocha, babban mataimaki na musamman ga Mataimakin Shugaban Ƙasa kan yaɗa labarai da sadarwa, ya fitar a lokacin, an ce Shettima zai yi amfani da hutun wajen “nazari, yin tunani da sabunta tunani na ilimi”.

Nkwocha ya bayyana hutun a matsayin wata dama ga Mataimakin Shugaban Ƙasar ya duba shirye-shiryen da gwamnatin ke ci gaba da aiwatarwa tare da ƙara fahimtar sababbin batutuwan manufofin ƙasa da na duniya, gabanin ƙara zage damtse wajen aiwatar da Ajandar Renewed Hope.

Sanarwar ta kuma ce tun bayan hawansa mulki, Shettima ya ci gaba da taka rawa wajen daidaita da kuma sa ido kan wasu muhimman shirye-shiryen gwamnati.

Kashim ya dawo gida Najeriya
Kashim Shettima na addua a wajen taro Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Daga cikin wuraren da ya fi mayar da hankali akwai bunƙasa tattalin arziƙi, samar da wadataccen abinci, harkokin jin kai, sauya fasalin ayyuka zuwa na zamani, samar da guraben aikin yi da haɗin gwiwar yankuna.

Shettima kuma shi ne shugaban Majalisar Tattalin Arziƙin Ƙasa, wadda ta ƙunshi gwamnonin jihohi 36, gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) da sauran jami’an gwamnati.

Shettima ya yabi gwamnatin Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta cancanci yabo maimakon suka.

Kashim Shettima ya ce Najeriya ta samu gagarumin ci gaba a fannin tattalin arziki sakamakon sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ta aiwatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng