Rivers: Wike Ya Fito da Komai kan Hana Fubara Shiga Takara a 2027

Rivers: Wike Ya Fito da Komai kan Hana Fubara Shiga Takara a 2027

  • Ministan birnin tarayya, Nyesom Wike, ya ce bai yi mamakin janyewar gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, daga zaben fidda gwani ba
  • Rahoto ya nuna cewa Nyesom Wike ya bayyana hakan ne a ranar Litinin bayan duba wasu ayyukan ci gaba da ake gudanarwa a fadin Abuja
  • A bayanin da ya yi, Wike ya sanar da cewa janyewar Fubara daga neman takarar gwamna ya yi daidai da yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce janyewar gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, daga neman takarar gwamna a 2027 ya yi daidai da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma domin tabbatar da kwanciyar hankali a jihar.

An bayyana cewa Nysom Wike ya fadi hakan ne yayin ganawa da ‘yan jarida bayan duba ayyukan da suka hada da abubuwa more rayuwa a Abuja.

Kara karanta wannan

'Ba za mu bar 'yan adawa ba,' Tinubu ya magantu kan zaben 2027

Nyesom Wike da Siminalayi Fubara
Ministan Abuja, Nyesom Wike a hagu, Gwamna Simi Fubara a dama. Hoto: Sir Siminalayi Fubara|Lere Olayinka
Source: Facebook

Maganar Wike kan takarar Fubara

Punch ta wallafa cewa Wike ya ce matakin ya dace da fahimtar juna da aka cimma yayin kokarin sulhu tsakanin manyan ‘yan siyasar jihar Rivers.

A kwanakin baya Fubara ya janye daga zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC, yana mai cewa ya dauki matakin ne bayan tuntubar jama'arsa.

Sai dai Wike ya dage cewa janyewar ba abin mamaki ba ne, yana mai cewa ta yi daidai da yarjejeniyoyin da aka cimma yayin tattaunawar zaman lafiya a baya.

Shiga tsakani da Tinubu ya yi

Idan ba a manta ba, shugaba Bola Tinubu ya shiga tsakani a rikicin da aka yi tsakanin Wike da Fubara, ciki har da jagorantar yarjejeniyar sulhu da bangarorin biyu suka sanya wa hannu.

An ce daga baya gwamna Fubara ya saba wasu sharudan yarjejeniyar, lamarin da ya kai ga ayyana dokar ta-baci a jihar da dakatar da shi.

Kara karanta wannan

Bayanai sun fito: An ji dalilin Tinubu da APC na kin marawa Fubara baya domin takara

Shugaban kasar ya sake ganawa da bangarorin biyu kafin kawo karshen dokar ta-bacin ranar 18 ga Satumba, 2025, inda Fubara ya bayyana cewa a shirye yake ya sadaukar da mukaminsa domin zaman lafiya ya dawo a jihar Rivers.

Dalilin janye takarar Fubara

Premium Times ta wallafa cewa Wike ya ce daga cikin yarjejeniyar shi ne a janye yunkurin tsige Fubara daga gwamna da sharadin cewa ba zai nemi wa’adi na biyu ba.

Wike ya kuma soki matakin da gwamnan ya dauka na sayen fom din APC, yana mai cewa hakan ya saba da yarjejeniyar kuma ya kara rikitar da kokarin sulhu.

“Ban yi mamakin janyewar gwamnan ba. Tun farko ma bai kamata ya saye fom din ba, saboda an cimma yarjejeniya cewa a dakatar da yunkurin tsige shi, sannan shi ma ba zai nemi wa’adi na biyu ba,”

In ji Wike.

Ya kara da cewa matakan da gwamnan ya dauka a baya ba su nuna halin dattako ba duk da kokarin da aka yi domin dawo da zaman lafiya.

“Amma duk wani abu da zai biyo baya dai ya janye, sannan wani ya fito,”

Kara karanta wannan

An kawar da Fubara, na kusa da Wike ya samu tikitin takarar gwamna a Rivers

In ji shi.

Nyesom Wike na duba aiki a Abuja
Nyesom Wike da jami'an gwamnati a wajen duba aiki a Abuja. Hoto: Lere Olayinka
Source: Facebook

Fubara ya janye neman takara

A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya sanar da janyewarsa daga zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC.

Ya bayyana haka ne a a cikin wata sanarwa da ya ce ya dauki matakin ne bayan tuntubar masana, iyalan shi, abokai da makusantan shi.

Ya ce bayan dogon nazari da tattaunawa mai yawa ya janye daga zaben fidda gwani na gwamna a APC domin samar da zaman lafiya a Rivers.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng