Tiriliyoyin Naira Ta Tinubu Ya Adana wa Yan Najeriya dalilin Cire Tallafin Mai
- Ministan Kudi Taiwo Oyedele ya bayyana makudan kudi da gwamnatin Bola Tinubu ta samu dalilin cire tallafin man fetur
- Daga cikin kudin, gwamnatin tarayya ta samu Naira tiriliyan 5.4, yayin da jihohi da ƙananan hukumomi suka raba Naira tiriliyan 10.4
- Oyedele ya ce gwamnati ta kuma samu karin kudaden shiga na Naira tiriliyan 3.1 tare da karbar bashin Naira tiriliyan 11.9
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Kudi kuma Ministan da ke kula da tattalin arzikin Najeriya, Taiwo Oyedele, ya bayyana alherin da Gwamnatin Bola Tinubu ta samu.
Oyedele ya bayyana an samu makudan kudi dalilin cire tallafin man fetur wanda ya ceto Najeriya ta samu Naira tiriliyan 15.8.

Source: Twitter
Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wani taron manema labarai, inda ya yi bayani kan tasirin sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan
FAAC ta cika aljihun gwamnatin Tinubu da jihohi, an raba abin da ba a taba samu ba
Lokacin da aka samu rarar kudaden
Oyedele ya ce an samu wannan kudin ne tsakanin Yuni 2023 da Disamba 2025, kuma ya taimaka wajen kara albarkatun da ke karkashin Tarayyar Najeriya.
Ya bayyana cewa kudaden da aka samu ba su shiga asusun Tarayya ne da wata sanarwa mai suna “subsidy savings” ba.
Ya ce:
“Tsakanin Yuni 2023 da Disamba 2025, cire tallafin ya samar da Naira tiriliyan 15.8 a matsayin albarkatun Tarayya.”
Oyedele ya ce daga cikin wannan kudi, gwamnatin tarayya ta samu Naira tiriliyan 5.4, yayin da jihohi da kananan hukumomi suka samu Naira tiriliyan 10.4 ta hanyar Asusun Tarayya.
Oyedele ya ce matsayin kudaden gwamnatin tarayya a wannan lokaci ya kuma nuna karin kudaden shiga kai tsaye da kuma karin basussuka domin gudanar da ayyuka.
Ya ce gwamnatin tarayya ta samu karin Naira tiriliyan 3.1 daga kudaden shiga na cikin gida, musamman kudaden da hukumomin gwamnati suka tura da karin rarar kudaden wasu hukumomi.

Source: Facebook
Basukan da gwamnatin ta karba
Gwamnatin ta kuma karbi karin bashin Naira tiriliyan 11.9 tsakanin Yuni 2023 da Disamba 2025.
Oyedele ya ce hada karin kudaden shiga da karin basussukan ya kai jimillar karin albarkatun da gwamnatin tarayya ta samu zuwa Naira tiriliyan 20.4.
Sai dai ya bayyana cewa jimillar karin kudaden da gwamnati ta kashe a wannan lokacin ta kai Naira tiriliyan 30.64.
Ya ce alkaluman suna nuna tasirin sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta bullo da su domin magance matsalolin tattalin arzikin da suka dade suna addabar kasar.
Oyedele ya bayyana cire tallafin man fetur da hada darajar musayar kudaden waje a matsayin wasu daga cikin manyan sauye-sauyen gwamnatin.
Ya ce cire tallafin man fetur ya kasance matakin da ya zama dole saboda tallafin yana kara raunana tattalin arzikin kasar.
'Alfanun cire tallafin mai ga Najeriya' - Tinubu
Mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Tinubu ya ce kudaden da aka samu bayan cire tallafin man fetur suna biyan albashi tare da tallafa manyan ayyukan hanya.
Tinubu ya bayyana cewa gwamnati za ta fara wallafa yadda ake amfani da kudaden tallafin da aka cire, domin nuna amfaninsu ga talakawa.
NUPENG ta roki Tinubu ya dakatar da aikin wucin-gadi a masana'antar man fetur, tare da farfado da matatun mai da ma'ajiyar bututun mai Read more:
Asali: Legit.ng

