Ministan Buhari Da Ke Shari'a da EFCC Ya Zama Dan Takarar Gwamnan ADC a Kebbi
- Tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami, ya samu tikitin takarar gwamnan Kebbi na jam’iyyar ADC domin zaben shekarar 2027
- Mai taimaka wa Malami kan yada labarai ya ce jam’iyyar ta kuma tabbatar da Aminu Bande, Ibrahim Mera da Garba Danjuma a matsayin ‘yan takarar majalisa
- Duk da shari’un EFCC da DSS da ake yi masa a Abuja, Malami ya ce zai mayar da hankali kan tsaro, adalci da cigaban Kebbi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Birnin Kebbi - Tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami, ya zama dan takarar gwamnan Kebbi na jam’iyyar ADC domin zaben 2027.
Hakan na zuwa ne yayin da ake zargin tsohon ministan da badakalar makudan kudi lokacin da yake kan kujerar.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin Malami na X ranar Lahadi 24 ga watan Mayun 2026 da muke ciki.
Godiya da Malami ya yi ga shugabannin ADC
Sanarwar ta ce Malami ya gode wa shugabannin jam’iyya, masu ruwa da tsaki da magoya baya saboda goyon bayan da suka nuna masa.
Jam’iyyar ta kuma tabbatar da Aminu Bande mai ritaya daga aikin soja a matsayin dan takarar sanatan Kebbi ta tsakiya a zaben 2027.
Haka kuma, Ibrahim Mera tsohon mataimakin kwanturola janar ya samu tikitin Kebbi ta arewa yayin da Garba Danjuma ya samu na Kebbi ta kudu.
“Tare da haɗin kai da jajircewa, za mu gina makoma mafi armashi ga al’umma masu zuwa.”
Sanarwar ta ce Malami zai ci gaba da mayar da hankali kan shugabanci nagari, adalci, tsaro da cigaba mai dorewa ga Kebbi da Najeriya.
Malami ya ce hadin kai da jajircewa za su taimaka wajen gina kyakkyawar makoma mai anfani ga al’ummomin jihar a nan gaba.
A watan Nuwamban 2025, Malami ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna, yana mai cewa akwai buƙatar ceto jihar daga “wahala da matsananciyar rashin tsaro” da ya ce gwamnatin yanzu ta haddasa.

Source: Facebook
Tuhumar da EFCC ke yi wa Malami
A watan Nuwambar 2025, Malami ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna yana mai cewa jihar na fama da tsananin wahala da rashin tsaro.
Tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya na fuskantar shari’u biyu a babbar kotun tarayya da EFCC da DSS suka shigar a Abuja.
A watan Janairu, kotu ta bada umarnin kwace kadarori 57 da ake zargin suna da alaka da ayyukan haramtattu da Malami da ‘ya’yansa suka mallaka.
Malami ya sayi fom din takara a ADC
A baya, kun ji cewa tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami, ya shiga cikin sahun masu neman takarar gwamnan jihar Kebbi a zaben 2027.
Abubakar Malami ya sayi fom din neman tsayawa takarar gwamnan jihar Kebbi a karkashin inuwar jam'iyyar ADC mai adawa.
Tsohon Ministan ya koka kan halin da jihar take ciki, inda ya zayyano matsalolin da ke ci mata tuwo a kwarya tare da yin alkawarin cewa zai kawo mafita kan halin da ake ciki.
Asali: Legit.ng

