Babbar Magana: An Bayyana Abin da Ke Kashe Mutane Fiye da 'Yan Bindiga a Najeriya
- MiDaraktan asibitin UNIMEDTH ya yi gargadin cewa jabun magunguna na zama babbar barazana ga lafiyar jama’a
- Farfesa Michael Gbala ya bayyana cewa amfani fa jabun magunguna na iya zama hadari ga mutane ciye da illar yan bindiga
- ya buƙaci masu ruwa da tsaki su inganta hanyoyin saye, rarrabawa da sa ido kan magunguna domin kare marasa lafiya daga amfani da jabun magunguna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ondo- Babban Daraktan Asibitin Koyarwa na Jami’ar Kimiyyar Lafiya ta Ondo (UNIMEDTH), Farfesa Michael Gbala, ya nuna damuwa kan ƙara yaɗuwar jabun magunguna da marasa inganci a Najeriya
Ya fadi haka ne da yake magana yayin ziysrar da Babban Mai Ba da Shawara kan Zuba Jari a Fannin Magunguna da Kiwon Lafiya ga Gwamnatin Jihar Ondo, Dakta Samuel Oluwaoromipin Adekota, ya kai wa asibitin a ranar Laraba.

Kara karanta wannan
Abubuwan da ya dace a sani game da yarjejeniyar da aka yi tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya

Source: Facebook
Farfesa Gbala ya yi gargadin cewa jabun magunguna na iya yin sanadin mutuwar mutane fiye da ’yan bindiga, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa domin kare tsarin samarwa da rarraba magunguna daga shiga cikin matsala.
Illar da ke tattare da magungunan jabu
Bayan taron, shugaban UNIMEDTH ya jaddada illar magungunan da ba su da inganci da kuma jabun magunguna, yana mai bayyana su a matsayin barazanar ɓoye amma mai matuƙar haɗari ga lafiyar jama’a.
“Jabun magunguna na kashe mutane da sauri fiye da ’yan bindiga,” in ji shi, yana mai jaddada buƙatar tsaurara sa ido da tabbatar da inganci wajen saye da rarraba magunguna.
Abin da ya taba faruwa da Farfesa Gbala
Gbala ya tuna da wata matsala da ta taɓa faruwa da shi da ta ƙara nuna masa muhimmancin lamarin.
Ya bayyana cewa a wani lokaci ya fara shakkar sahihancin wani magani da ya saya wa ’yarsa duk da cewa ya biya kuɗi mai yawa.

Kara karanta wannan
Kasar Birtaniya ta aiko saƙo Najeriya bayan APC ta sha kaye a zaben gwamnan jihar Osun
A cewarsa, cibiyoyin kiwon lafiya ya kamata su ƙara mayar da hankali kan inda aka samo magungunan da ake bai wa marasa lafiya da kuma ingancinsu.
Ya ce sayen magani daga sanannen mai samar da magunguna ba lallai ne ya tabbatar da cewa maganin na gaske ne ba.
“Kasancewarsa daga hukumar samar da magunguna (DMA) ba ya tabbatar da cewa magani ne na gaske,” in ji Gbala.

Source: Getty Images
Wane mataki ya kamata a dauka?
Babban Daraktan ya buƙaci masu ruwa da tsaki su inganta hanyoyin saye, rarrabawa da sa ido kan magunguna domin kare marasa lafiya daga amfani da jabun magunguna ko waɗanda ba su da inganci.
Ya kuma yi kira da a riƙa adana cikakkun bayanai kan umarnin sayen magunguna da kuma lokutan da masu samar da magunguna suka kasa cika buƙatun da aka gabatar musu.
Likita ya rasu bayan isa asibiti
Kun ji cewa wani kwararren likitan da ke aiki a Jihar Kano ya rasu bayan ya fadi jim kadan bayan ya isa Asibitin Arewa Surgery da ke Hotoro.
Lamarin ya faru ne bayan an bukaci marigayin, wanda aka bayyana sunansa da Dokta Ibrahim, ya mayengurbin wani likitan da ya kasa halartar aikinsa na yamma a asibitin.
Asali: Legit.ng