An Kashe Mutane 8 bayan Dan Majalisa Ya Bada Kyautar Miliyoyin Naira a Jihar Neja

An Kashe Mutane 8 bayan Dan Majalisa Ya Bada Kyautar Miliyoyin Naira a Jihar Neja

  • Akalla mutum takwas ne aka tabbatar sun mutu bayan rikici ya barke tsakanin Fulani da Kamuku a garin Tegina da ke jihar Neja
  • Rikicin ya samo asali ne bayan kashe shugaban Fulani da aka ce wani dan majalisa ya ba shi tallafin N10m domin rabawa al'umarsa
  • ‘Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin tare da tura jami’an tsaro domin dawo da zaman lafiya bayan ayyana dokar hana fita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Neja - Akalla mutum takwas ne suka rasa rayukansu a wani rikici tsakanin Fulani da Kamuku a garin Tegina da ke ƙaramar hukumar Rafi a jihar Neja.

Rikicin ya fara ne bayan wata gudummawar kuɗi da Sanata Sani Musa mai wakiltar Neja ta Gabas ya bayar a ranar Lahadi.

Rikicin da ya barke a Neja bayan dan majalisa ya raba N10m ya jawo sanadin mutuwar mutum 8.
Sanata Sani Musa, mai wakiltar Neja ta Gabas da ya bada kyautar N10m da ake zargin ta jawo mutuwar mutum 8. Hoto: Senator Mohammed Sani Musa
Source: Facebook

Rikici bayan kisan shugaban Fulani a Neja

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun farmaki sanatar Abuja, sun tarwatsa taron jam'iyyar ADC

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa mazauna yankin sun ce rikicin ya ɓarke ne ranar Juma’a lokacin da wasu makiyaya suka kai hari kan 'yan sa-kai a kasuwar Tegina.

An ce makiyayan sun zargi 'yan sa-kai da kashe shugabansu, Muhammed Shehu, wanda ake zargin ta hannunsa ne aka bai wa al’ummar Fulani tallafin kuɗin.

Wani mazaunin yankin mai suna Garba AP ya ce:

“Sanatan ya bayar da N10m ga al’ummar Fulani ta hannun shugabansu Muhammed Shehu. Amma daga baya aka kashe shi.”

Ya ƙara da cewa bayan an gano gawar Shehu kusa da ofishin 'yan sa-kai da Kamuku suka fi rinjaye ne Fulani suka fara kai hare-haren ramuwar gayya.

An birne gawarwaki 8 a Neja

Garba AP ya shaida wa jaridar cewa Fulani dauke da makamai sun kutsa cikin kasuwar Tegina inda suka kai hari kan 'yan sa-kai tare da tarwatsa harkokin kasuwanci.

A cewarsa:

“An binne gawarwaki takwas daga ɓangarorin biyu bayan rikicin.”

Rahotanni sun nuna cewa an sanya dokar hana fita tare da tura sojoji domin shawo kan lamarin.

Sai dai duk da sassauta dokar hana fita a ranar Asabar, an ci gaba da samun rikice-rikice a wasu sassan garin.

Kara karanta wannan

Albarkacin bikin babbar Sallah, gwamna zai fara rabon kayan abinci ga ma'aikata

Akalla mutane 8 aka kashe da rikici ya barke a Neja bayan dan majalisa ya raba kudi
Wani gari da 'yan bindiga suka cinnawa wuta ya kone kurmus a Neja. Hoto: @MP_Muye
Source: Twitter

‘Yan sandan Neja sun tabbatar da lamarin

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da aukuwar rikicin da mutuwar mutum takwas.

Ya ce jami’an tsaro na neman babban wanda ake zargi da kashe shugaban Fulani, yana mai cewa:

“An samu rikici tsakanin wasu Fulani da 'yan sa-kai kan zargin kashe Mohammed Shehu na ƙauyen Gimi.”

Ya ƙara da cewa bayan tura jami’an tsaro zuwa yankin, an samu kwanciyar hankali yayin da ake ci gaba da bincike da neman waɗanda suka aikata laifin.

An kashe mutane 60 a kasuwar Neja

A wani labari, mun ruwaito cewa, akalla mutane 60 ne suka rasa rayukansu bayan wani mummunan hari da ’yan bindiga suka kai a Kasuwan Daji da ke Borgu a Jihar Nijar.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun fito ne daga dajin Kainji, inda suka kewaye kasuwar, suka sace mutane da dama musamman mata da yara, tare da banka wa kasuwa wuta.

An gudanar da aikin gano gawarwaki a dazuka da ke kewaye da wajen, yayin da gwamnati ta bayyana matakan da take ɗauka domin dakile irin waɗannan hare-hare.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com