2027: Muhammad Abacha Ya Sha Kaye, PDP Ta Tsaida dan Takarar Gwamna a Jihar Kano

2027: Muhammad Abacha Ya Sha Kaye, PDP Ta Tsaida dan Takarar Gwamna a Jihar Kano

  • Jam'iyyar adawa ta PDP ta kammala zaben fitar da dan takarar gwamna a jihar Kano yayin da shirye-shiryen babban zaben 2027 ke kara kankama
  • Sakamakon zaben da ya gudana a Kano ya nuna cewa dan tsohon shugaban kasa dlna mulkin soja, Mohammed Sani Abacha ya rasa tikitin PDP
  • Shugaban Kwamitin Zaɓen, Umar Danjani Hadejia ya ayyana Muhammad Bello Dalhatu a matsayin wanda ya samu nasara kuma dan takarar gwamna na PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Mohammed Sani Abacha, babban ɗan marigayi tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha, ya sha kaye a ƙoƙarinsa na samun tikitin takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar PDP a zaɓen 2027.

Rahotanni sun nuna cewa Mohammed Abacha ya sha kaye ne a hannun Muhammad Bello Dalhatu bayan gudanar da zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar adawa ta PDP.

Kara karanta wannan

"Kamar nadin sarauta," Masani ya yi kaca kaca a nasarar da Tinubu ya samu a APC

PDP .
Tutar jam'iyyar adawa a Najeriya (PDP) Hoto: PDP Nigeria
Source: Facebook

'Dan Abacha ya rasa tikitin PDP a Kano

Shugaban kwamitin zaɓen, Umar Danjani Hadejia, ne ya bayyana sakamakon, inda ya ce an gudanar da shi cikin lumana ba tare da wata matsala ba, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Ya sanar da cewa Muhammad Bello Dalhatu ya zama zakara bayan ya samu ƙuri’u 2,233, yayin da Mohammed Sani Abacha ya zo na biyu da ƙuri’u 749.

PDP ta tsaida dan takarar gwamna

Umar Hadejia ya ce an gudanar da zaɓen ne bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar, Dokar Zaɓe da kuma ƙa’idojin hukumar INEC.

“Da yake ya samu mafi yawa kuma ingantattun ƙuri’u, na ayyana Alhaji Muhammad Bello Dalhatu a matsayin wanda ya lashe zaɓen fid-da-gwani na gwamna na PDP kuma ɗan takarar jam’iyyar a Kano,” in ji shi.

Ya kuma yaba wa ‘yan takara, wakilai, jami’an jam’iyya, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki bisa nuna haɗin kai da jajircewa yayin gudanar da zaɓen.

Kara karanta wannan

Tsohon IGP Adamu ya yi barazana bayan rasa tikitin APC na zaben gwamnan Nasarawa

Yadda 'dan Abacha ya nemi takara a Kano

Tun da farko, babban dan Abacha ya nemi tikitin takarar gwamna na PDP a 2023 amma ya sha kaye a hannun Sadiq Aminu Wali bayan rikicin cikin gida tsakanin ɓangarorin jam’iyyar a lokacin.

Kafin hakan kuma, Mohammed Abacha ya tsaya takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar APDA a zaɓen 2019 a Kano, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Muhammad Abacha.
Muhammad Abacha, dan marigayi tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Sani Abacha Hoto: Muhammad Abacha
Source: Facebook

Jonathan na shirin fitowa takara a PDP?

A wani rahoton, kun ji cewa hadimi ga tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Ebele Jonathan , Wealth Dickson Omimim-Imagwa, ya yi magana kan jita-jitar da ake yadawa kan ubangidansa.

Hadimin na Jonathan ya yi watsi da jita-jitar da ke alaƙanta tsohon shugaban na Najeriya da tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP gabannin babban zaɓen 2027 mai zuwa.

A cewarsa, Jonathan bai bayyana sha’awarsa ga neman takarar shugaban ƙasa na 2027 ba, kuma bai ba wa wani mutum ko ƙungiya izinin sayen fom ɗin takara ko yin kamfen a madadinsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262