Najeriya Ta Yi Rashi: Malamin Addini da Ya Shahara har a Kasashen Waje Ya Mutu
- Prophet Emmanuel Alogbo, shugaban ruhaniya na duniya na Cherubim and Seraphim Movement, ya koma ga mahaliccinsa
- An ce ya fara aiki a Hukumar Kula da Jiragen Ƙasa ta Najeriya kafin ya shiga cocin C&S, inda ya zama fitaccen jagoran waƙoƙin ibada
- Alogbo ya kafa reshen farko na cocin C&S a Kudancin Najeriya, sannan ya jagoranci yaɗa cocin zuwa Amurka da Birtaniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Legas - Allah ya karbi rayuwar Dakta Emmanuel Abiodun Adewale Alogbo, wani fitaccen malamin addinin Kirista a Najeriya.
Mutuwar Alogbo, shugaban cocin Cherubim & Seraphim Movement na duniya baki ɗaya, ta jawo saƙonnin ta'aziyya daga mambobin cocin da kuma al'ummar Kiristoci.

Source: Facebook
Abubuwa 6 game da malamin cocin
Ga muhimman bayanai shida game da rayuwar marigayin kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito:
1. An haife shi a ranar Easter a 1933
An haifi Prophet Emmanuel Alogbo ranar 18 ga Afrilu, 1933, a titin Inabiri da ke Legas, a gidan Dickson Adeleye Alogbo da Maria Ojubomo Alogbo.
Ya yi karatun firamare a makarantar Ago-Ijaiye Primary School da ke Ebute Meta, kafin ya kammala karatun sakandare a St. Paul's Secondary School da Oduduwa College, dukkansu a Ile-Ife.
2. Ya fara aiki a Kamfanin Jirgin Ƙasan Najeriya
A shekarar 1950, ya fara aiki da Kamfanin Jirgin Ƙasan Najeriya (NRC), inda ya yi aiki a sashen lantarki da na'urorin sanyaya iska na sashen injiniya.
Canja wurinsa zuwa Zariya a shekarar 1955 ya kasance wani muhimmin mataki da ya sauya alkiblar rayuwarsa ta addini.
3. Ya shiga cocin ne ta hanyar waƙoƙi
Yayin da yake Zariya, ya ji wasu mambobin cocin Cherubim da Seraphim suna rerawa ɗaya daga cikin waƙoƙin da ya rubuta.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, bayan ya gyara yadda suka rera waƙar, daga bisani ya shiga ƙungiyar mawaƙan cocin a shekarar 1959.
Daga baya ya zama ɗaya daga cikin fitattun jagororin harkar waƙoƙin cocin, inda ya shigar da ganga ta gargajiya (gangan) cikin tsarin ibada.
4. Ya kafa reshen farko na cocin a Kudu
Bayan ya koma Legas a shekarar 1960, Prophet Alogbo ya kafa reshen farko na cocin Cherubim da Seraphim a kudancin kogin Neja, a gidansa da ke titin Cregg a Surulere, Legas.
An gudanar da ibadar farko ranar 29 ga Satumba, 1960, tare da kusan masu ibada 10, wanda ya zama tubalin faɗaɗa cocin a Kudancin Najeriya.
5. Ya kawo sauyi a tsarin waƙoƙin ibada

Source: Facebook
Ana kallon Prophet Alogbo a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda suka fara amfani da salon waƙoƙin ibada na zamani a cocin.
Ya fara amfani da ƙaho a waƙoƙin ibada kafin daga baya ya ƙara amfani da gita, orga da sauran kayan kiɗa.
Waɗannan sauye-sauye sun yi tasiri sosai a tsarin ibadar cocin Cherubim da Seraphim da ma wasu majami'u.
6. Ya faɗaɗa cocin zuwa ƙasashen waje
Baya ga Najeriya, Prophet Alogbo ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa rassan cocin Cherubim da Seraphim a ƙasashen waje.
Ya taimaka wajen bunƙasa cocin musamman a Amurka, inda aka kafa rassa a Los Angeles, New York da Houston a jihar Texas, sannan har da Birtaniya.
Marigayin ya rasu ya bar 'ya'ya, jikoki da kuma tattaba kunne.
Malamin Muslunci a Najeriya ya rasu
A wani labari kuma, mun ruwaito cewa, Sheikh Surajudeen Akanni, wanda aka fi sani da Arizukuna, ya yi bankwana da duniya bayan gajeriyar rashin lafiya.
Malamin addinin Musuluncin ya rasu ne da yammacin ranar Talata, 28 ga Yulin 2026, kuma aka yi jana'izarsa ranar Laraba, 29 ga watan Yulin 2026.
Matar fitaccen mawakin Fuji, Kwam 1, ta bayyana Arizukuna a matsayin uba a gare ta yayin da ta yi masa ta'aziyya.
Asali: Legit.ng


