‘Ku Dakatar da Gina Gadar Sama’: Tinubu ga Gwamnoni, Ya Kawo Masu Mafita

‘Ku Dakatar da Gina Gadar Sama’: Tinubu ga Gwamnoni, Ya Kawo Masu Mafita

  • Shugaba Bola Tinubu ya bukaci gwamnonin jihohi su fifita gina hanyoyi maimakon wasu ayyuka da ke cin kudi kuma marasa amfani
  • Tinubu ya ce gwamnati ba ta biya kuɗin fansa ga masu satar ɗaliban makarantar Oriire ba, yana mai jaddada cewa babu sasanci
  • Shugaban ya bayyana shirin faɗaɗa rundunar soji zuwa rukunoni 12, ƙarfafa masu gadin dazuka da kafa ‘yan sandan jihohi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci gwamnonin jihohi su mayar da hankali wajen gina hanyoyi da sauran muhimman ababen more rayuwa.

Tinubu ya bukaci gina hanyoyi ne maimakon gina gadar sama da ayyukan da ba su da amfani sosai ga jama'a.

Tinubu ya shawarci gwamnonin Najeriya
Shugaba Bola Tinubu da wasu gwamnonin Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Tinubu ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi tawagar sarakunan gargajiya daga Oyo ƙarƙashin jagorancin Olubadan na Ibadan, Oba Rashidi Adewolu Ladoja, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Remi Tinubu ta lallaba Saudiyya, tana so a taimaka wa Najeriya kan karatun allo

Shawarar Tinubu ga gwamnonin Najeriya

Ya ce inganta hanyoyi zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki, rage matsalolin tsaro da kuma sauƙaƙa rayuwar ‘yan Najeriya.

Shugaban ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatinsa sun ƙara yawan kuɗaɗen shiga da jihohi ke samu.

Saboda haka ya bukaci gwamnoni su karkata waɗannan kuɗaɗe zuwa ayyukan da za su amfani al'umma kai tsaye maimakon manyan ayyukan nuna ƙarfi da ba su da tasiri.

Ya bayyana cewa shimfiɗa hanyoyi zuwa yankunan da ba su da isasshen ci gaba zai ƙara harkokin kasuwanci tare da bai wa jami'an tsaro damar isa wuraren da ake buƙatar agaji cikin gaggawa yayin da matsalar tsaro ta taso.

Shawarar da Tinubu ya ba gwamnoni
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yayin taro. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Facebook

Ninkin kudaden da Tinubu ke ba gwamnoni

Tinubu ya ce kuɗin da jihohi ke samu yanzu ya ninka sau huɗu zuwa biyar idan aka kwatanta da baya.

Ya ƙara da cewa jihohi ba sa sake karɓar bashi domin biyan albashi, yayin da masu karɓar fansho ke samun haƙƙoƙinsu.

Kara karanta wannan

Yadda aka ware N400bn na gyaran masallatai, masarautu a kasafin kudin 2026

Shugaban ya bukaci sarakunan gargajiya su isar da wannan saƙo ga gwamnoni, yana mai cewa maimakon gina gadar sama a wuraren da babu cunkoson ababen hawa, ya dace a gina manyan hanyoyin da za su inganta zirga-zirga, rayuwar jama'a da kuma ayyukan tsaro.

Shugaban ya ce tsare-tsaren gina ababen more rayuwa dole su kasance bisa buƙatun jama'a da kuma manufofin tsaron ƙasa.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati na shirin faɗaɗa rundunar sojin Najeriya daga rukunoni takwas zuwa goma sha biyu domin rage lokacin kai ɗauki.

Haka kuma, ya ce gwamnati na aiki kan kafa ‘yan sandan jihohi tare da matakan kariya domin hana amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba.

Ya ƙara da cewa sarakunan gargajiya za su taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar wannan tsari.

Sakon Tinubu ga wasu gwamnoni a Najeriya

A baya, an ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci masu mulki da shugabannin musulmi da kiristoci su tausayawa talakawa musamman a wannan lokaci na azumi.

Tinubu wanda ya shiga Aso Rock a 2023 ya ce haɗuwar azumin Ramadan da na Kiristoci (Lent) na nuna cewa dukkan addinai suna da manufa ɗaya.

A wurin taron shan ruwa da ya shirya a fadar shugaban kasa, Tinubu ya yabi gwamnan Borno bisa tallafin da ya raba wa musulmi da kiristoci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.