Tsohon Hadimin Shugaban APC na Kasa, Mustapha Dawaki Ya Bi tafiyar Kwankwaso a Kano

Tsohon Hadimin Shugaban APC na Kasa, Mustapha Dawaki Ya Bi tafiyar Kwankwaso a Kano

  • Hon. Mustapha Dawaki, tsohon shugaban ma'aikata na shugaban APC na kasa ya sauya sheka daga jam'iyya mai mulki zuwa NDC
  • Jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma jigo a NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne ya tarbe shi a gidansa da ke Miller Road a jihar Kano
  • Dan siyasar ya bar APC ne bayan rasa tikicin komawa Majalisar tarayya sakamakon tsarin sulhun da aka yi amfani da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Tafiyar Kwankwasiyya ta yi babban kamu a jihar Kano yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen tunkarar babban zaben 2027 da ke tafe.

Hon. Mustapha Baba Dawaki, tsohon shugaban ma’aikatan shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya fice daga jam'iyya mai mulkin Najeriya.

Dawaki.
Hon. Mustapha Dawaki tare da jigon NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Kwankwaso ya yi babban kamu a Kano

Kara karanta wannan

NDC: Kwankwaso ya ɗaga hannun Batayya, Gaya ya rasa takarar sanata a Kano

Rahoton da Daily Trust ta tattaro ya nuna cewa tsohon hadimin shugaban na APC ya bi tafiyar madugun Kwankwasiyya, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, inda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar NDC.

Hon Mustapha Dawaki, wanda tsohon ɗan majalisar wakilai ne mai wakiltar mazaɓar Dawakin Kudu/Warawa ta jihar Kano, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar adawa ta NDC ne bayan rasa tikitin APC.

'Dan siyasar na cikin wadanda suka rasa tikitin komawa majalisa sakamakon tsarin maslaha da APC ta yi amfani da shi a jihar Kano.

NDC ta tarbi Hon. Mustapha Dawaki

Hadimin Kwankwaso, wanda yana ɗaya daga cikin jagororin NDC kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Saifullahi Hassan, ya tabbatar da sauya shekar a ranar Litinin, 25 ga watan Mayu, 2026.

Saifullahi Hassan ya wallafa hotunan sauya ahekar Hon. Mustapha a shafinsa na Facebook, yana mai cewa sauya shekar ta gudana ne a gidan Kwankwaso da ke Miller Road a Kano.

A hotunan dai an ga Sanata Kwankwaso ya sanya wa Mustapha Dawaki jar hula ta yan Kwankwasiyya, alamar da ke tabbatar daa ya shiga wannan tafiya a hukumance.

Kara karanta wannan

'Mutumina ne': Peter Obi ya yi magana da ake zargin yana gujewa Atiku

Hadimin Kwankwaso ya ce:

“Jagora (Kwankwaso) ya karɓi tsohon shugaban ma’aikatan shugaban APC na ƙasa, Mustapha Bala Dawaki (Mai Gidan Ruwa) zuwa jam'iyyar NDC Kwankwasiyya."
Kwankwaso.
Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso lokacin da yake sanya wa Mustapha Dawaki jar hula Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

NDC za ta ba shi tikitin takara?

Sauya shekar na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyar NDC ke ci gaba da tantance masu neman takarar da za ta bai wa tikiti a faɗin jihar Kano ta hanyar tsarin maslaha.

Sai dai har yanzu ba a bayyana ko Dawaki zai samu tikitin kai-tsaye domin sake tsayawa takarar kujerar majalisar ba.

Kabiru Gaya ya rasa takara a NDC

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon sanatan Kano ta Kudu, Kabiru Gaya, ya rasa tikitin takarar Sanata a NDC bayan zaman da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya jagoranta.

Tun farko dai, Kabiru Gaya ya fice daga jam’iyyar APC a ranar 5 ga watan Afrilu, 2026 inda ya shiga ADC kafin daga bisani ya koma NDC tare da Kwankwaso.

Sai dai burin nasa ya gamu da cikas a ranar Lahadi, 24 Mayu, 2026 bayan da jam’iyyar ta zaɓi Kassim Batayya a matsayin ɗan takarar Sanatan Kano ta Kudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262