NDC: Kwankwaso Ya Ɗaga Hannun Batayya, Gaya Ya Rasa Takarar Sanata a Kano

NDC: Kwankwaso Ya Ɗaga Hannun Batayya, Gaya Ya Rasa Takarar Sanata a Kano

  • Tsohon Sanatan Kano ta Kudu, Kabiru Gaya, ya rasa tikitin takarar Sanata a jam’iyyar NDC bayan zaman da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya jaoranta
  • NDC ta tsayar da Kassim Batayya a matsayin ɗan takararta tilo da zai goga da sauran jam'iyyu a fafatawar da za a yi a babban zaben 2027
  • Matakin na zuwa a yayin da NDC ta fara gangamin shiga babban zaben 2027 da ke tafe, inda za a fafata a tsakanin jam'iyyun Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – NDC ta tsayar da sabon ɗan takarar Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, inda ta yi ajiye tsohon Sanata Kabiru Gaya wanda ya koma jam’iyyar da niyyar sake komawa majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

'Dan gwagwarmaya Sowore ya fito takarar shugaban kasa, zai kara da Tinubu a 2027

Kwankwaso ya zabi Kassim Ibrahim Batayya a matsayin dan takarar NDC
Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Tun farko dai, Kabiru Gaya ya fice daga jam’iyyar APC a ranar 5 ga watan Afrilu, 2026 inda ya shiga ADC kafin daga bisani ya koma NDC tare da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Premium Times ta wallafa cewa bayan sauya sheƙarsa, tsohon ɗan majalisar ya nuna aniyarsa ta sake neman kujerar Sanata karkashin inuwar sabuwar jam’iyyarsa ta adawa.

NDC ta tsayar da dan takara

Sai dai burin nasa ya gamu da cikas a ranar Lahadi, 24 Mayu, 2026 bayan da jam’iyyar ta zaɓi Kassim Batayya a matsayin ɗan takarar bai ɗaya na Kano ta Kudu.

Kabiru Gaya ya taba wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa na tsawon wa’adi biyu a karkashin APC daga shekarar 2015 zuwa 2023.

An y i taron zaben dan takarar Sanatan Kano ta Kudu
Kassim Batayya (na 2 daga hannun hagu) tare da manyan NDC a taron gidan Kwankwaso Hoto: Aliyu Hamza Adam
Source: Facebook

Rahotanni sun nuna cewa an cimma matsayar tsayar da Kassim Batayya ne a wani zama da aka gudanar a gidan Rabiu Kwankwaso da ke titin Miller a Kano.

Kara karanta wannan

Dan Ganduje ya fara nema takarar majalisar tarayya a NDC mai adawa

Daga baya kuma, ya sake wallafa wani gajeren bidiyo inda aka ga Kabiru Gaya yana bayyana goyon bayansa ga Batayya.

Ana zaben fitar da gwani a NDC

A halin yanzu, jam’iyyar NDC a Kano na ci gaba da gudanar da zaɓukan fitar da gwani na kujerun Sanata da na majalisar wakilai da kuma majalisar dokokin jihar.

Kabiru Gaya ya taba zama gwamnan Kano a jamhuriya ta uku tsakanin 1992 zuwa 1993, daga baya ya wakilci Kano ta Kudu a majalisar dattawa har zuwa shekarar 2023 lokacin da Kawu Sumaila na jam’iyyar NNPP ta wancan lokaci ya kayar da shi a zaɓe.

Abin da ya ja hankali shi ne, Kawu Sumaila ma ya fice daga NNPP zuwa APC, kuma tuni aka tsayar da shi domin tsayawa takara a zaɓen shekarar 2027 mai zuwa.

NDC ta daidaita kanta a Kano

A baya, mun kawo labarin NDC ta warware rikicin shugabanci a Kano, bayan wasu kalamai da shugaban jam'iyyar Hon. Husaini Isah Mai Riga ya fara jawo rikici a kan shugabancin jam'iyya.

Kara karanta wannan

Tsohon dan acaba da ya zama ɗan majalisa ya rasa takara bayan ya koma APC

Hon Mai Riga ya fito kafafen yada labarai yana zargin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya shigo NDC da mutanensa kuma za a tura su gefe yayin da shi da jama'arsa za su rike mukaman jam'iyya.

Shugaban jam'iyyar ya bayyana cewa ba za su taba lamunta ba a yi masu abin da ya kira ture kaza kwashe kwai gabanin zaben 2027 ba, lamarin da ya sa Kwankwaso da shugabancin NDC ya kira taron gaggawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng