Fadar Shugaban Kasa Ta Hango Kura Kurai a Kalaman Obi, Ta Yi Masa Zazzafan Martani
- Fadar Shugaban Ƙasa ta yi martani ga sababbin kalaman Peter Obi kan gwamnatin Bola Tinubu tare da bayyana cewa shugaban ya tsufa
- Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce Peter Obi bai fahimci irin ci gaban da ake samu a faɗin Najeriya da ayyukan da ake yi ba
- Ya ce gwamnatin Tinubu na da rahotannin da ke nuna tasirin manufofinta da sauye-sauyen tattalin arziki kuma jama'ar Najeriya na ji a jikinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Fadar Shugaban Ƙasa ta mayar da martani kan kalaman da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya yi kwanan nan.
Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da sukar da ya yi wa tasirin shirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Renewed Hope Agenda.

Source: Facebook
Martanin na dauke a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin 27 ga watan Yuli, 2026.
Martanin Fadar shugaban kasa ga Obi
Nigerian Tribune ta wallafa cewa cewa yadda Obi ya yi nazarin ayyukan gwamnatin bai yi daidai da abin da ke faruwa a sassa daban-daban na ƙasar ba.
A cewar Onanuga, manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Tinubu na ci gaba da haifar da sakamako mai kyau a al'ummomi da ke dukkan shiyyoyin siyasar Najeriya guda shida.
Ya rubuta cewa:
"Peter Obi yana bukatar ya daina kallon abubuwa ta fuskar mabiya ƙungiyarsa masu tsananin goyon baya. Alamomin shirin Renewed Hope suna bayyana a fili a ƙauyuka, garuruwa, birane da kuma dukkan ƙananan hukumomi da ke cikin shiyyoyin siyasar Najeriya guda shida."
Onanuga ya bayyana cewa tawagar sadarwa ta Fadar Shugaban Ƙasa ta yi rangadi a dukkannin shiyyoyin ƙasar domin ganin yadda ake aiwatar da manufofin gwamnati da kuma jin ra'ayin al'umma kai tsaye.
Fadar shugaban kasa ta na aiki - Onanuga
Mai magana da yawun shugaban ƙasar ya ƙara da cewa akwai cikakkun bayanai da ke nuna tasirin sauye-sauyen tattalin arziki da kuma ayyukan ci gaban da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa.

Source: Twitter
Ya ce:
"Idan Peter Obi ya na son ya sani, akwai kundin rahotanni na zamani da ke cike da bayanan yadda tattalin arzikin Najeriya ke farfaɗowa a ƙarƙashin wannan gwamnati. Rahotannin sun haɗa da manyan ayyuka, manufofi da shirye-shirye masu sauya rayuwa, ciki har da NELFUND, waɗanda ke tasiri kai tsaye ga rayuwar 'yan Najeriya."
Martanin na zuwa ne bayan Peter Obi ya yi wata hira inda ya soki tasirin manufofin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, lamarin da ya jawo muhawara a fagen siyasar ƙasar.
An nemi Tinubu ya yi murabus
A baya, mun wallafa cewa jam'iyyar ADC ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya sauya manufofinsa na tattalin arziki ko ya sauka daga mulki saboda ƙarin talauci da yunwa da ake fama da shi a Najeriya.
Jam'iyyar ta ce rahotannin Bankin Duniya da WFP sun nuna manufofin gwamnatin APC sun gaza wajen inganta rayuwar miliyoyin 'yan Najeriya wanda kullum su ke kuka da matsalar rayuwa.
Jam'iyyar ADC ta yi alƙawarin farfaɗo da noma, gyara madatsun ruwa da tabbatar da tsaro idan ta lashe babban zaɓen shugaban ƙasa tare da bayar da hadin kai aka kayar da gwamnatin Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng


