'Gwamnatin Yaudara Ce': Barayan Karaye Ya Ce NDC ba Ta Fargabar Abba a Zaben 2027
- Ɗan takarar majalisar jihar Kano na NDC, Injiniya Ibrahim Abdullahi Karaye, ya zargi gwamnatin Abba Kabir Yusuf da gazawa
- Ya ce gwamnati na amincewa da ayyuka ne kawai, amma ba a ganin aiwatar da su a ƙasa lamarin da ya sa babu abin da za a daga
- Injiniya Ibrahim Abdullahi Karaye ya kuma bayyana cewa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya fi Abba Kabir Yusuf ƙwarewa da gogewa a siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano –Ɗan takarar majalisar jihar Kano a inuwar jam'iyyar NDC, Injiniya Ibrahim Abdullahi Karaye, ya yi zargin gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta gaza a Kano.
Ya bayyana haka ne a hira da ya yi da Legit, inda ya ƙara da cewa babu wani aiki da za su ɗaga a ce za a sake zaɓen Abba da shi a Kano

Source: Facebook
Injiniya Ibrahim Abdullahi Karaye ya ƙara da cewa ba su ɗauki gwamnatin Kano a matsayin gwamnati mai aiki ba, sai dai gwamnati mai yaudara.
Ɗan takarar NDC ya fadi gazawar Abba
Injiniya Ibrahim Abdullahi Karaye ya bayyana cewa an gaza a wurare da dama, inda ya buga misali da cewa an ba da amincewar gyaran makarantu, amma shiru ake ji.
Ya ce:
"Sun ce za su ba da kuɗin gyaran makarantu 13 da gwamnatin Ganduje ta rufe. To abin takaici shi ne, an fi shekara ɗaya da bayar da damar a yi wannan aiki, amma ko bulo ba a kai ba."
Ya bayyana cewa, a binciken da suka yi, ba a gyara ko makaranta ɗaya ba a sauran ƙananan hukumomin jihar Kano duk da an amince da aikin.

Source: Facebook
Injiniya Ibrahim Abdullahi Karaye ya ce:
"Mu yanzu sai dai mu ce Abba yana bayar da amincewar ayyuka ne, ba gwamna mai aiki ba."
Injiniya Ibrahim Abdullahi Karaye ya ƙara da cewa duk manyan ayyukan da aka nema, gwamnati tana bayar da amincewa, amma babu aikin a ƙasa.
Gwarzo ya fi Abba nagarta - Barayan karaye
Karaye ya ƙara da bayyana cewa babu yadda za a kwatanta nagartar Gwamna Abba Kabir Yusuf da ta Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.
Injiniya Ibrahim Abdullahi Karaye ya ƙara da cewa:
"Ai ka san an ce ba a haɗa ƙwai da dutse. Kwamared Aminu Abdussalam, ka san tsayayyen namiji ne, ba namiji ba ne da ke tafiya yana rangwaɗa, kamar yadda ya faɗa."
"Yana da tarihin siyasa. Ya tsaya takara tun da farko, kuma ya ci zaɓe. Lokacin da ya tsaya wannan zaɓen ma, ba wai INEC ce ke tantance 'yan takara ba, hukumar tsaron farin kaya ta DSS ce ke tace 'yan takara."
Ya bayyana cewa ko a wancan lokacin mulkin soja ya yi takara, kuma ya yi nasara. Saboda haka, a cewarsa, haɗa shi da Abba Kabir Yusuf ba daidai ba ne.
Injiniya Ibrahim Abdullahi Karaye ya ƙara da cewa Kwamared ya taɓa zama kwamishina, ya zama shugaban ƙaramar hukuma, ya riƙe mukaman kwamishinoni daban-daban kafin ya zama mataimakin gwamna.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta hango kura kurai a kalaman Obi, ta yi masa zazzafan martani
Ya ƙara da bayar da tabbacin cewa Kwamared Aminu Abdussalam zai yi nasara tare da doke Abba Kabir Yusuf ba tare da an samu matsala ba.
NDC ta yi magana kan Kwankwaso
A baya, mun kawo labarin cewa shugaban NDC a Kano, Hussaini Isah Mai Riga, ya ce Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bai taba neman a tsayar da dansa, Mustapha Rabi'u Musa Kwankwaso takara ba.
Ya ce su ne suka yanke shawarar tsayar da Mustapha Rabiu Kwankwaso takarar gwamnan Kano ba tare da umarnin Kwankwaso ba, domin da farko ma sai da ya yi kokarin hana su tsayar da dansa.
Sai dai daga baya an sauya matsaya, jam'iyyar hamayya ta NDC ta yanke shawarar a tsayar da Kwamared Aminu Abdussalam takara, aka ba Mustapha mukamin mataimakin gwamnan jihar Kano.
Asali: Legit.ng

