An Kafawa Tinubu Sharuda 9 yayin da za a Yi Zanga Zangar Kasa Baki Daya
- Ƙungiyar Take It Back ta buƙaci 'yan Najeriya su fito zanga-zangar lumana a faɗin ƙasar nan ranar 5 ga Agusta, 2026, domin nuna damuwa kan matsalar tsaro da tsadar rayuwa
- Ƙungiyar ta ce gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta gaza magance matsalolin da suka addabi al'umma, tare da zargin cewa ana tauye 'yancin faɗar albarkacin baki
- Take It Back ta kuma gabatar da wasu buƙatu da suka haɗa da inganta tsaro, rage tsadar rayuwa, soke dokar yanar gizo da kuma ƙarin albashi ga ma'aikatan Najeriya da sauransu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Ƙungiyar Take It Back ta sanar da shirinta na gudanar da zanga-zangar lumana a faɗin Najeriya ranar 5 ga Agusta, 2026, wadda ta sanya wa suna ranar wadanda aka zalunta.
Ƙungiyar ta bayyana cewa zanga-zangar za ta bai wa 'yan ƙasa damar bayyana koke-kokensu kan matsalar tsaro, tsadar rayuwa, zargin tauye haƙƙin jama'a a ƙarƙashin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Source: Getty Images
Punch ta rahoto cewa ƙungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai kula da ita na ƙasa, Juwon Sanyaolu, ya sanya wa hannu a ranar Laraba.
Dalilan shirya zanga-zangar
A cewar ƙungiyar, Najeriya na fuskantar matsaloli masu yawa, inda ta ce hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane na ci gaba da addabar jihohi da dama.
Sanarwar ta ce:
"Najeriya na cikin mawuyacin hali. A kowane yanki na ƙasar nan, talakawa na shan wuya alhali masu mulki na fantamawa."
Ta ƙara da cewa iyalai da dama na ci gaba da biyan kuɗin fansa domin ceto 'yan uwansu, yayin da jami'an gwamnati ke ci gaba da yin alkawuran da ba su cikawa.
Ƙungiyar ta kuma danganta hauhawar farashin kayan masarufi da cire tallafin man fetur a shekarar 2023 da kuma ci gaba da faɗuwar darajar Naira.
Buƙatun da ƙungiyar ta gabatar
Take It Back ta zargi gwamnati da amfani da dokar yanar gizo wajen takura wa 'yan jarida, masu fafutuka, ɗalibai da sauran 'yan ƙasa masu bayyana ra'ayoyinsu.
Ta ce ma'aikatan Najeriya da suka haɗa da sojoji, 'yan sanda, malamai, ma'aikatan lafiya da sauran ma'aikatan gwamnati sun cancanci albashi mai inganci.
The Guardian ta wallafa cewa kungiyar ta buƙaci gwamnati ta:
- Inganta tsaro tare da ceto mutanen da ke hannun masu garkuwa
- Sakin duk waɗanda ta kira fursunonin siyasa
- Soke dokar yanar gizo
- Aiwatar da mafi ƙarancin albashin ₦500,000
- Rage tsadar rayuwa
- Janye shari'ar da ake yi wa Omoyele Sowore
- Cire shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila
- Sallamar babban daraktan DSS, Tosin Ajayi
- Kare ikon Najeriya

Source: Facebook
Ƙungiyar ta buƙaci 'yan Najeriya su fito zanga-zangar cikin lumana, tana mai cewa lokaci ya yi da jama'a za su haɗa kai domin neman sauyi.
Martanin APM ga kalaman Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar APM ta ce kalaman da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa limaman cocin Katolika cewa tattalin arziki da tsaro sun inganta ba su dace da halin da ake ciki ba.
Jam'iyyar ta bayyana cewa miliyoyin 'yan Najeriya na ci gaba da fuskantar matsananciyar talauci, yayin da hare-haren 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane ke ƙaruwa a sassan ƙasar.
APM ta ce ikirarin da shugaban ƙasa ya yi ya saba da abin da talakawan Najeriya ke fuskanta a rayuwarsu ta yau da kullum a fadin kasar nan.
Asali: Legit.ng

