ADC Ta Fitar da Sanarwa, Atiku na Shirin Fafatawa da Masu Neman Takarar 2027

ADC Ta Fitar da Sanarwa, Atiku na Shirin Fafatawa da Masu Neman Takarar 2027

  • Jam’iyyar ADC ta bukaci masu neman takarar shugaban kasa, shugabannin jam’iyya da mambobinta su bayar da hadin kai gabanin zaben fidda gwani
  • Hakan na zuwa ne yayin da Atiku Abubakar da wasu 'yan takara biyu za su fafata a zaben fidda gwani na jam'iyyar a yau Litinin, 25 ga Mayun 2026
  • Sakataren yada labaran ADC, Bolaji Abdullahi ya bayyana zaben fidda gwanin a matsayin wani muhimmin lokaci ga jam’iyyar da kuma ‘yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta bukaci masu neman takarar shugaban kasa, shugabannin jam’iyya, wakilai da mambobi a fadin kasa da su rungumi hadin kai gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa da aka shirya yi a ranar Litinin.

Jam’iyyar ta ce wannan zabe wani muhimmin lokaci ne ba ga ADC kadai ba har ma ga ‘yan Najeriya masu neman abin da ta bayyana a matsayin sahihin dandalin siyasa gabanin babban zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

'Dan gwagwarmaya Sowore ya fito takarar shugaban kasa, zai kara da Tinubu a 2027

Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi
Sakataren yada labaran ADC, Bolaji Abdullahi. Hoto: ADC Vanguard
Source: Facebook

Kiran ADC kan fidda gwani

A wata sanarwa da sakataren yada labarai na kasa na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar a X a ranar Lahadi a Abuja, ya yi karin haske kan zaben da su yi.

Ya ce yadda masu ruwa da tsaki za su gudanar da kansu kafin, yayin da kuma bayan zaben fidda gwanin zai tsara yadda jama’a za su kalli kimar dimokuradiyya da shugabanci na jam’iyyar.

“ADC tana alfahari da kasancewa a yau ita kadai ce sahihiyar jam’iyyar dimokuradiyya a Najeriya, domin ita kadai ce jam’iyyar siyasa da ake tantance dan takarar shugaban kasarta ta hanyar zaben fidda gwani a bayyane,”

In ji sanarwar.

Kiran ADC ga masu son takara

Jam’iyyar adawar ta jaddada bukatar duk masu takara da magoya bayansu su gudanar da kansu cikin zaman lafiya a lokacin gudanar da zaben, tana mai cewa dole ne zaben fidda gwanin ya nuna ka’idojin da ADC ke ikirarin wakilta.

Kara karanta wannan

'Ba za mu bar 'yan adawa ba,' Tinubu ya magantu kan zaben 2027

Sanarwar ta ce:

“Saboda haka muna kira ga duk masu neman takara, magoya bayansu, wakilai da mambobin jam’iyya da su gudanar da kansu cikin zaman lafiya, da alhaki da kuma mutunci a duk lokacin wannan tsari.
"Wannan zabe dole ne ya nuna kimar da muke ikirarin wakilta a matsayin jam’iyyar da ta kuduri aniyar gaskiya, dimokuradiyya cikin gida, hadin kan kasa da bin doka,”
Shugabannin ADC a Abuja
Atiku Abubakar da wasu jagororin ADC a Abuja. Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Facebook

ADC ta ce za a yi adalci

Jam’iyyar ta kuma tabbatar wa mambobinta cewa an yi dukkan shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da gaskiya da sahihancin tsarin zaben fidda gwani.

Punch ta rahoto sanarwar ta ce:

“Tarihi zai yi mana hukunci bisa yadda muka gudanar da kanmu a wannan muhimmin lokaci. Muna kira ga kowane mamba na babbar jam’iyyarmu da ya tashi tsaye,”

Tsagin ADC ya fitar da dan takara

A wani labarin, mun kawo muku wasu da suka bayyana cewa su ne shugabannin jam'iyyar ADC sun fitar da dan takarar shugaban kasa na 2027.

Kara karanta wannan

2027: ADC ta fitar da dan takarar shugaban kasa, ta ajiye Atiku a gefe

Dumebi Kachikwu da tsagin jam'iyyar ya tsayar a matsayin dan takara ya bayyana cewa ya shirya domin kalubalantar shugaba Bola Tinubu.

Bugu da kari, tsagin ADC ya sanar da rusa shugabancin David Mark da sauran da yake aiki tare da su tare da nada wasu shugabanni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng