2027: ADC Ta Fitar da Dan Takarar Shugaban Kasa, Ta Ajiye Atiku a Gefe

2027: ADC Ta Fitar da Dan Takarar Shugaban Kasa, Ta Ajiye Atiku a Gefe

  • Tsagin jam’iyyar ADC ya rusa kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) karkashin jagorancin David Mark da ke aiki da su Atiku Abubakar
  • Rahotanni sun nuna cewa tsagin ADC ya ayyana Dumebi Kachikwu a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2027
  • An dauki matakin ne a babban taron tsagin jam’iyyar da zaben fidda gwani da aka gudanar a Abuja, inda wakilai suka amince da Kachikwu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wani tsagin jam’iyyar ADC mai biyayya ga Dumebi Kachikwu ya rusa Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) na jam’iyyar a ranar Lahadi tare da ayyana shi a matsayin dan takarar shugaban kasa.

An dauki matakin ne a babban taron jam’iyyar da zaben fidda gwani da aka gudanar a Abuja, inda wakilai suka amince da Kachikwu ta hanyar kada kuri’a da baki.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari da ke shari'a da EFCC ya zama dan takarar gwamnan ADC a Kebbi

Dumebi Kachikwu da zai yi wa tsagin ADC takara
Dumebi Kachikwu yayin bayani bayan ayyana shi a matsayin dan takarar tsagin ADC a Abuja. Hoto: Imran Mohammed
Source: Facebook

Tsagin ADC ya zabi shugabanni

Rahotan da jaridar Puch ta wallafa ya nuna cewa tsagin ADC ya sanar da rusa NWC da ake da shi tare da maye gurbinsa nan take da sababbin shugabanni a matakin kasa.

Sababbin shugabannin sun hada da Kingsley Oggah a matsayin Shugaban Kwamitin Amintattu, Abdulkadir Bashir a matsayin Shugaban Jam'iyya na Kasa.

An zabi Johnny Derek a matsayin Sakatare na Kasa, Kennedy O. Odion a matsayin Ma’aji na Kasa, Amirigoye a matsayin Sakataren Kudi na Kasa, da kuma Sakataren Yada Labarai na Kasa, Dr Chris Ugwu.

Bayanin dan takarar tsagin ADC

Da yake jawabi bayan karbar tutar jam’iyyar, Kachikwu ya ce Najeriya na cikin wani mawuyacin hali kuma tana bukatar shugabanci mai karfi domin magance rashin tsaro, rashin aikin yi, matsin tattalin arziki da rarrabuwar kai.

Ya ce kasar na fuskantar tabarbarewar yanayin zamantakewa da tattalin arziki, yana mai cewa ‘yan Najeriya da dama na barin kasar domin neman ingantacciyar rayuwa a ketare.

Kara karanta wannan

'Mutumina ne': Peter Obi ya yi magana da ake zargin yana gujewa Atiku

A cewarsa, dole jam'iyyar ADC tsaya a matsayin wata sahihiyar kafar samar da sauyi a harkokin gwamnati tare da dawo da fatan samun cigaba a zukatan ga ‘yan kasa.

Wasu daga cikin shugabannin ADC
Jagororin ADC da ke bangaren Sanata David Mark. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

A lokacin da ya yi bayani a Abuja, Dumebi Kachikwu ya kara da cewa Najeriya mallakin dukkan ‘yan kasa ce kuma bai kamata wasu tsirarun mutane su kasance su ne masu cin gajiyarta ba.

Ga bayanin da Dumebi Kachikwu ya yi a wani bidiyo da tashar Arise News ta wallafa a X:

Tinubu ya zama dan takarar APC

A wani labarin, kun ji cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a babban zaben 2027 da ke tafe.

An sanar da haka ne bayan samun gagarumar nasara a zaben fidda gwani na shugaban kasa da jam’iyyar ta gudanar a fadin kasa a ranar Asabar, 23 ga Mayu, 2026.

An ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben a ranar Lahadi bayan gudanar da zaben a dukkan mazabu 8,809 da ke cikin kananan hukumomi 774 na kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng