'Yan Ta'adda Sun Farmaki Sanatar Abuja, Sun Tarwatsa Taron Jam'iyyar ADC

'Yan Ta'adda Sun Farmaki Sanatar Abuja, Sun Tarwatsa Taron Jam'iyyar ADC

  • Sanata Ireti Kingibe ta ce wasu ‘yan ta'adda sun kai hari hedikwatar ADC yayin rabon kayan zaben fitar da gwani na majalisar dokoki a Abuja
  • Ta yi zargin cewa wani mutum mai suna Tijani Mubarak ya jagoranci harin inda aka ci zarafin ‘yan takara da jami’an kwamitin zaben jam'iyyar
  • Kingibe ta bayyana cewa an ci zarafinta ta hanyar buga ta da bango tare da raunata wata ‘yar takarar majalisar wakilan tarayya yayin wannan harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Sanatar da ke wakiltar babban birnin tarayya Abuja, Ireti Kingibe, ta bayyana yadda wasu ‘yan ta'adda suka kai hari hedikwatar ADC.

Kingibe ta ce lamarin ya faru ne ranar Alhamis lokacin da ta kai ziyara sakatariyar jam’iyyar domin sa ido kan rabon kayan zaben fitar da gwani na majalisar dokoki a Abuja.

Kara karanta wannan

ADC ta fitar da sanarwa, Atiku na shirin fafatawa da masu neman takarar 2027

Sanata Ireti Kingibe ta bada labarin yadda 'yan ta'adda suka farmake ta a ofishin ADC a Abuja.
Ireti Kingibe, 'yar majalisar dattawa mai wakiltar birnin tarayya Abuja. Hoto: @IretiKingibe
Source: Twitter

An farmaki sanatar Abuja a taron ADC

'Yar majalisar dattawan ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Asabar.

A cewar Kingibe, jim kaɗan bayan ta isa ofishin, wani mutum mai suna Tijani Mubarak ya shiga wurin tare da wasu mutane huɗu.

Ta ce jami’an kwamitin sun tambayi ko shi ne mutumin da ya kira su tun farko, amma nan take ya fusata tare da yin magana cikin rashin mutunci.

Kingibe ta ce:

“Lokacin da shugaban kwamitin ya nuna cewa ba zai amince da irin wannan rashin kunya ba, Mubarak ya miƙe ya mari shugaban kwamitin da ƙarfi.”

An ci zarafin wata ‘yar takarar ADC

Sanatar ta ce wata ‘yar takarar majalisar wakilai da ke wurin ta fara ɗaukar bidiyon abin da ke faruwa da wayarta.

Sai dai ta ce hakan ya fusata Mubarak wanda ya umarci mutanensa su ƙwace wayar.

Kara karanta wannan

'Dan gwagwarmaya Sowore ya fito takarar shugaban kasa, zai kara da Tinubu a 2027

A cewarta, ‘yan ta'addan sun ɗaga matar sama suna ƙoƙarin ƙwace wayar tare da raunata hannuwanta kafin daga baya aka kuɓutar da ita.

An wurga Sanata Kingibe jikin bango

Sanata Kingibe ta ƙara da cewa bayan an ci zarafin matar, ɗaya daga cikin mutanen ya juya kanta.

Ta ce:

“Ya kama ni ya wurga ni da ƙarfi a jikin bango har kaina ya bugi bangon sosai.”

Ta bayyana cewa jami’an tsaronta ne suka shiga tsakaninsu tare da hana mutumin ci gaba da kai mata hari.

Sanatar ta yi zargin cewa Mubarak ya kulle ƙofar fita domin hana su tserewa daga ɗakin, har sai da magoya bayanta da ke a waje suka suka karya ƙofar domin fitar da su.

'Yan ta'adda sun farmaki Sanata Ireti Kingibe a hedikwatar ADC a Abuja.
Sanata Ireti Kingibe ta karfi katin shaidar zama 'yar jam'iyyar ADC a Abuja. Hoto: @IretiKingibe
Source: Twitter

Magoya baya sun ceci sanatar Abuja

A cewarta, lokacin da suka isa ƙasan bene domin fita daga ofishin, sun gano cewa an sake kulle babbar ƙofar fita kuma an gudu da makullin.

Sanata Kingibe ta ce hakan ya nuna cewa an shirya harin ne tun farko domin tsare su da cutar da su.

Kara karanta wannan

'Ba za mu bar 'yan adawa ba,' Tinubu ya magantu kan zaben 2027

Ta ce daga bisani mambobin ADC da magoya bayanta sun samu damar buɗe ƙofar tare da kare ta da wata mata mai suna Dr. Fatima.

Kingibe ta zargi gwamnatin kan dokar zabe

A wani labari, mun ruwaito cewa, Sanata Ireti Kingibe, ta bayyana fargabar cewa an canja wasu sassa na Dokar Zaɓe ta 2026 bayan majalisa ta miƙa wa shugaban ƙasa.

Ireti Kingibe ta yi zargin cewa an cire ko an raunana matakan tsaro da aka saba gani a jikin takardun ƙuri'a na INEC, wanda zai bude kofar tafka maguɗi.

Wannan kalami na 'yar majalisar dattawan ya yi daidai da koke-koken Mike Igini, tsohon kwamishinan INEC, wanda ya nuna damuwa kan sashe na 63.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com