ADC Ta Hango Matsala ga APC bayan Hukuncin Babbar Kotu kan Zabe a Najeriya
- Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta yi martani kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke dangane da tanade-tanaden hukumar INEC kan zabe
- ADC ta bayyana cewa ta yi maraba da hukuncin wanda zai ba 'yan siyasa damar sauya sheka daga wannan jam'iyya zuwa wancan kafin zaben 2027
- Babbar am'iyyar hamayyar ta bayyana cewa hukuncin da kotun ta yanke, zai ba da dama ga 'yan siyasa su fice daga APC mai mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta yi martani kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yi kan wasu bangarori na ka'idojin da hukumar INEC ta gindaya kan zabe.
Jam'iyyar ADC ta bayyana cewa hukuncin soke wasu ɓangarori na ƙa’idojin da INEC ta gindaya kan zaɓubbukan 2027 zai haifar da ficewar mambobi da dama daga jam’iyyar APC mai mulki.

Source: Twitter
ADC ta bayyana hakan ne ranar Alhamis, 21 ga watan Mayun 2026 ta hannun mai magana da yawun bakinta na kasa, Bolaji Abdullahi, cikin wata sanarwa a shafinsa na X.
Jam'iyyar ADC ta ji dadin hukuncin kotu
An fitar da sanarwar ne yayin da take mayar da martani ga hukuncin kotun kan dokokin INEC da suka shafi wa’adin gudanar da zaɓubbukan fitar da gwani na jam’iyyu da kuma rajistar mambobi.
Jam’iyyar hamayyar ta bayyana hukuncin a matsayin tabbacin gaskiyar ƙorafe-korafenta na baya-bayan nan game da wasu tanade-tanade na hukumar zaɓen.
A cewar ADC, ta riga ta nuna damuwa kan abin da ta bayyana da taƙaitaccen lokaci na gudanar da zaɓubbukan fitar da gwani na jam’iyyu da rajistar mambobi lokacin da aka ƙaddamar da tanade-tanaden.
“Saboda haka, shawarar da kotu ta yanke kan waɗannan batutuwa, har da waɗanda suka saba wa kundin tsarin mulki kai tsaye, wani abin farin ciki ne da ke tabbatar da matsayarmu."
- Bolaji Abdullahi
ADC ta ce 'yan siyasa za su bar APC
Jam’iyyar ta kafa hujjar cewa hukuncin kotun zai ƙarfafa ’yancin taron ƙungiyoyi ta hanyar kawar da iyakokin da aka sanya wa ’yan siyasa masu neman tsayawa takara a wasu jam'iyyun siyasa na daban.
“Mun yi amanna a wancan lokacin cewa an tsara wancan takaitaccen tsari ne domin hana mutane barin jam’iyya mai mulki, wato APC.”
“Yanzu da yake kotu ta yanke hukunci a kansa, muna da yakinin cewa, a kwanaki masu zuwa, za mu shaida ficewar gungun mutane da dama daga jam’iyya mai mulki."
- Bolaji Abdullahi

Source: Facebook
ADC ta ce tana maraba da wannan hukunci kuma ta nuna kyakkyawan fatan cewa hukuncin zai zurfafa shigar da jama'a cikin harkokin dimokuraɗiyya gabanin babban zaɓen 2027.
ADC ta tantance 'yan takarar shugaban kasa
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta tantance masu neman takarar shugaban kasa a karkashin inuwarta a zaben 2027.
Kwamitin tantance ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC ya tantance tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a birnin tarayya Abuja.
Hakazalika, kwamitin ya tantance tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi da kuma babban masanin tattalin arziki, Muhammed Hayatu-Deen.
Asali: Legit.ng


