'Yan Takarar Gwamna a PDP Sun Hana Yin Fasakwaurin Sunan Pantami gabanin Zabensu
- Yan takarar gwamna huɗu na PDP a Gombe sun ce sun ƙi yunkurin shigar da Farfesa Isa Ali Pantami cikin neman zaɓen fitar da gwani
- Dukkanin yan takarar sun ce doka ba ta yarda ɗan takara ya sauya jam’iyya bayan ya shiga zaɓen fitar da gwani a wata jam’iyya daban ba
- Wani na kusa da tsohon minista Isa Ali Pantami ya tabbatar da cewa tsohon mai neman takarar gwamna a APC na shirin komawa PDP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Gombe – Wasu ’yan takarar gwamna huɗu na jam’iyyar PDP a jihar Gombe sun bayyana rashin amincewarsu da abin da suka kira yunƙurin shigar da Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami cikin takarar gwamna ta jam’iyyar.
’Yan takarar sun haɗa da Alhaji Abdulkadir Hamma Saleh, Hon. Khamisu Ahmed Mailantarki, Hon. Usman Aliyu Garry da kuma Misis Monica Kaltho

Source: Twitter
A ruwayar Daily Trust, yan takarar sun bayyana haka ta cikin wata sanarwa da suka fitar bayan wani taron gaggawa da suka gudanar a ranar Lahadi 24 ga watan Mayu, 2026 a Gombe.
'Yan PDP sun yi adawa da Pantami
Jaridar Aminiya ta kawo labarin cewa yan takarar sun ce doka da ƙa’idojin dimokuraɗiyya ba su yarda mutum ya sauya jam’iyya sannan ya sake shiga irin wannan zaɓe ba bayan an riga an kaɗa ƙuri’u a wata jam’iyya.

Source: Facebook
Wani ɓangare na sanarwar ya ce:
“Biyo bayan raɗe-raɗin cewa wani ɗan takara, Farfesa Isa Ali Pantami, wanda ya shiga zaɓen fitar da gwani na gwamna na jam’iyyar APC da aka kammala kwanan nan, yana shirin komawa PDP domin ya shiga zaɓen fidda gwani na jam’iyyarmu, mun ga ya dace mu bayyana matsayarmu.”
Sun ƙara da cewa: “Saboda haka muna Allah-wadai da duk wani yunƙuri na shigar da wani ɗan takara cikin zaɓen fitar da gwani na PDP alhali bisa doka da ƙa’idojin dimokuraɗiyya bai cancanci shiga ba, kasancewar ya riga ya fafata a zaɓen fidda gwani na APC da aka gudanar ranar 21 ga Mayu, 2026.”

Kara karanta wannan
2027: Kakakin majalisar Kwara ya raba gardama a zaben fitar da dan takarar gwamnan APC
A yi taka tsan-tsan - Yan takarar PDP
’Yan takarar sun ce suna girmama shugabancin jam’iyyar PDP a jihar Gombe ƙarƙashin jagoran jam’iyyar, Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo, tare da dukkanin tsarin jam’iyyar a ƙananan hukumomi 11 na jihar.
Sun bayyana cewa sun amince shugabannin jam’iyyar su zaɓi mutum ɗaya daga cikinsu da zai zama ɗan takarar gwamna ba tare da wani sharadi ba.
Sanarwar ta ce:
“Mu ’yan takarar da muka sanya hannu, saboda girmamawa ga shugabancin jam’iyya musamman jagoran jam’iyyar PDP a Gombe, Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo, da sauran shugabanni da dattawan jam’iyyar, mun amince a bai wa shugabancin jam’iyya damar zaɓar mutum ɗaya daga cikinmu da zai ɗaga tutar PDP a zaɓen gwamna mai zuwa.”
Haka kuma sun gargadi shugabannin jam’iyyar da su guji duk wani mataki da zai sa a karya doka ko jefa PDP cikin rikicin shari’a.
'Yan Pantamiyya sun bi Jamilu
A baya, kun ji cewa kungiyar Pantamiyya Movement Brotherhood mai goyon bayan Farfesa Isa Pantami ta fice daga ci gaba da zama a bangaren tsohon ministan bayan dambarwa kan takarar gwamnan Gombe.

Kara karanta wannan
Gwanna Alia ya tika mutum 2 da kasa, ya lashe tikitin takarar gwamnan APC a zaben 2027
Pantamiyya ta bayyana goyon bayanta ga Jamilu Isyaku Gwamna bayan zaben fitar da gwani na APC a Gombe da ya samu nasara na samun tikitin takarar gwamna gabanin zaben 2027 a jihar.
Jamilu Gwamna ya samu kuri’a 247,161 wajen kayar da Farfesa Isa Ali Pantami da Saidu Alkali, duk da cewa an samu sabani kafin gudanar da zaben fitar da gwanin har sauran yan takarar sun janye.
Asali: Legit.ng
