'Ba Kwankwaso ba ne': Shugaban NDC Ya Fadi Wanda Ya Tsayar da Mustapha Takara
- Shugaban NDC a Kano, Hussaini Isah Mai Riga, ya ce Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bai taba neman a tsayar da dansa takara ba
- Ya ce su ne suka yanke shawarar tsayar da Mustapha Rabiu Kwankwaso takarar gwamnan Kano ba tare da umarnin Kwankwaso ba
- Sai dai daga baya an sauya matsaya, aka tsayar da Kwamared Aminu Abdussalam takara, aka ba Mustapha mukamin mataimaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Shugaban jam'iyyar NDC na Jihar Kano, Hussaini Isah Mai Riga, ya wanke Sanata Rabiu Musa Kwankwaso daga zargin cewa ya nemi a tsayar da dansa takara.
Wannan na zuwa ne bayan Sanata Rufa'i Hanga ya yi ikirarin cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya so a tsayar da yaronsa, Mustapha Rabiu Kwankwaso, takarar gwamnan Kano.

Source: Facebook
A wata hira da ya yi da Freedom Radio, wadda aka wallafa a shafin Facebook na kafar, Mai Riga ya rantse cewa babu wani lokaci da Kwankwaso ya zaunar da su domin neman a ba wa dansa takara.
Yadda NDC ta tsayar da Mustpaha takara
A cikin tattaunawar, Mai Riga ya bayyana cewa babu wani lokaci da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zaunar da su yana neman a ba wa Mustapha takara, ko ta wace hanya.
A kalamansa:
"Muhammadu Sarina ya ce da ni, 'Mai Riga.' Na ce, 'Na'am.' Ya ce, 'Na dauko wani aiki. Tun daga ADC ina so ka taya ni aikin nan.' Na ce, 'Wane aiki ne?' Ya ce, 'Na dauko batun tsayar da dan gidan Kwankwaso, Mustapha Rabiu, a matsayin dan takarar gwamnan Jihar Kano.'"
Ya kara da cewa, ko a lokacin da suka shaida wa Kwankwaso aniyarsu a filin jirgin sama, jagoran Kwankwasiyya bai ce musu komai a kan batun ba.

Kara karanta wannan
Magana ta fito kan zargin Obasanjo ya yi wa Tinubu aiki, an hada Obi da Kwankwaso
An kai Mustapha Kwankwaso Abuja
Hussaini Mai Riga ya kara da cewa bayan sun dawo Kano ne suka kira Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso, suka sanar da shi cewa suna son su tsayar da shi takarar gwamnan Kano.
Ya ce sun kuma umarce shi da ya raka su zuwa wurin jagoran jam'iyyar, Seriake Dickson, a Abuja domin tattauna wannan lamari.

Source: Facebook
Mai Riga ya ce ba su sani ba ko Mustapha ya sanar da Kwankwaso ko a'a, amma ya bi su zuwa wurin Dickson, inda aka gabatar da shi domin a tsayar da shi takara.
Ya ce Dickson ya sa wa Mustapha Kwankwaso albarka, sannan ya ce a ci gaba da shirye-shiryen tsayar da shi takarar gwamnan Kano ba tare da an sanar da jagora ba.
Ya kara da cewa, lokacin da aka sanar da Kwankwaso cewa an tsayar da Mustapha takara, sai ya ce hakan ba zai yiwu ba. Daga nan ya kira dansa, ya tambaye shi ko ya bayar da kudi kafin a tsayar da shi takara.
Daga karshe, an sake zama, inda aka tsayar da Kwamared Aminu Abdussalam takarar gwamnan Kano, aka kuma ba Mustapha Rabiu Kwankwaso mukamin mataimakin dan takara.
Yaron Kwankwaso ya samu takara
A baya, mun kawo labarin cewa 'dan jagoran Kwankwasiyya, Mustapha Rabiu Kwankwaso ya ajiye muƙaminsa na Kwamishinan Matasa da Wasanni na jihar Kano a gwamnatin Abba Kabir Yusuf.
Mustapha Rabi'u Musa Kwankwaso ya ajiye mukaminsa ne a ranar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke koma cikin APC mai mulki a hukumace yayin da siyasar Kano ta dauki sabon salo bayan raba gari da Kwankwaso.
Ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, yana fatan matasa da wasanni za su ci gaba da samun kulawa a gwamnatinsa tare da bayyana cewa zai ci gaba da alaka da siyasa domin taimakon jama'a.
Asali: Legit.ng

