Pantami Ya Fusata, Ya Janye daga Neman Takarar Gwamnan Gombe a APC, Ya Fadi Dalili

Pantami Ya Fusata, Ya Janye daga Neman Takarar Gwamnan Gombe a APC, Ya Fadi Dalili

  • Farfesa Isa Ali Pantami ya janye daga zaben fitar da gwani na gwamnan jihar Gombe da APC ta shirya gudanarwa saboda wasu zarge zarge
  • Tsohon ministan ya bayyana cewa ba a bai wa masu neman takara bayanan da suka dace kan wurin zabe da yadda za a tantance wakilai ba
  • Fitaccen malamin ya ce dama ya shiga neman takarar gwamnan ne bayan kiraye kirayen al'umma, amma yanzu ba zai iya ba saboda matsalolin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Gombe - Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya sanar da janyewarsa daga zaben fitar da gwani na kujerar gwamnan jihar Gombe karkashin jam’iyyar APC.

Pantami ya bayyana cewa ya dauki matakin ne saboda abin da ya kira 'karya dokar zabe ta 2026' da kuma 'rashin sahihin tsarin gudanar da zaben fitar da gwani' a jihar Gombe.

Kara karanta wannan

APC ta hana 'yan siyasa 47 shiga takarar sanata, ta saki cikakken jerin sunayen

Sheikh Isa Ali Pantami ya janye daga neman takarar gwamnan Gombe a APC
Sheikh Isa Ali Pantami yayin da yake gudanar da tafsirin Alkur'ani a 2026 a Abuja. Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Pantami ya fasa neman takarar gwamna a APC

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Barista Ibrahim M. Attahir ya fitar a madadin tafiyar Pantamiyya a ranar 19 ga watan Mayun 2026, a shafin Pantami na Facebook.

Sanarwar ta ce:

"Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya janye daga shiga zaben fitar da gwani na kujerar gwamnan jihar Gombe karkashin APC don nuna adawa kan karya dokar zabe ta 2026 da kuma gazawar jam'iyyar na samar da sahihan hanyoyin tattaunawa da samun bayanai ga masu neman takara."

A cikin sanarwar, fitaccen malamin addinin Musuluncin ya ce dama ya shiga takarar ne bayan kiraye-kirayen matasa, mata da sauran masu ruwa da tsaki a jihar.

Sanarwar ta ce Pantami ya nuna cikakken biyayya ga jam’iyyar APC ta hanyar bin dukkan sharudda da dokokin takarar gwamna.

An bayyana cewa Pantami ne kadai daga cikin masu neman takarar gwamna a APC da ya tura wakili zuwa taron yarjejeniyar zaman lafiya da rundunar ‘yan sanda ta shirya a Gombe ranar 14 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Pantami ko Jamilu Gwamna: An ji wanda ya fi cancanta ya zama ɗan takarar APC a Gombe

Pantami ya zargi APC da boye bayanai

Pantami ya ce duk da biyayyarsa ga jam’iyyar, an hana shi samun muhimman bayanai da suka shafi zaben fitar da gwanin.

Ya ce lauyoyinsa sun rubuta wasiku zuwa sassa daban-daban na jam’iyyar APC domin neman bayanai kan tsarin zaben kato-bayan-kato da za a gudanar, amma babu amsa ko tantancewar karbar wasikun.

Sanarwar ta ce:

“A dimokuradiyya, dole ne doka ta zama jagora. Rashin bin dokar zabe ta 2026 da dokokin jam’iyya ya sa tsarin zaben ya zama mara inganci da rashin sahihanci.”

Pantami ya kara da cewa abin da ya faru a zabukan fitar da gwani na majalisar tarayya da aka gudanar a ranakun 16 da 18 ga watan Mayu, 2026 ya nuna cewa ba a bai wa ‘yan kasa damar yin zabe yadda ya kamata ba.

Pantami ya ce an karya dokokin zabe a APC jihar Gombe
Sheikh Isa Ali Pantami ya na jawabi a lokacin da yaje sabunta rajistar zama dan APC a Gombe. Hoto: @Imranmuhdz
Source: Twitter

“Ba a gudanar da sahihin zabe ba”

Sanarwar ta zargi shugabannin APC da gaza samar da bayanai kan wuraren tattara sakamako, tsarin kada kuri’a da tantance wakilai da masu sa ido.

Kara karanta wannan

Gwamna Makinde ya manta da PDP, zai yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar hadaka

Pantami ya ce har zuwa lokacin da ya sanar da janyewarsa, ba a sanar da shi wurin tantance wakilai ko yadda za a gudanar da zaben ba.

Ya ce duk da umarnin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar na tabbatar da adalci da gaskiya a zabukan fitar da gwani, ba a aiwatar da hakan a Gombe ba.

Karanta sanarwar a nan kasa:

Wanda ya fi cancantar takara a Gombe

A wani labari, mun ruwaito cewa, APC ta tabbatar da cewa za ta yi amfani da tsarin kato bayan kato wajen zaben fitar da gwani na gwamna a jihar Gombe bayan rikicin sulhu.

Barista Isiyaku Danlawan ya ce mafi yawan masu neman takara sun amince da tsarin sulhu da ya fifita Dr. Jamilu Gwamna, in banda tsiraru.

Danlawan ya bayyana cewa Sheikh Isa Pantami malami ne mai kima amma bai da tubalin siyasar da zai iya kai shi ga nasara a jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com