Yadda Daliban Jami’ar Jos Suka Hallaka Matashi Kan Zargin Sata Wayar iPhone
- Wani matashi wanda ya kammala jami'ar Jos, ya rasu bayan wasu da ake zargi sun yi masa dukan tsiya kan zargin satar iPhone
- Rundunar 'yan sandan Plateau ta kama mutane uku da ake zargi, bayan bidiyon yadda aka doke marigayin da katako da bulala ya bazu sosai
- 'Yan sanda sun ce maimakon kai korafi ga hukuma, wadanda ake zargi sun dauki doka a hannunsu, tare da gargadin jama'a su guji daukar doka a hannu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau - Rundunar ƴan sanda a jihar Plateau sun cafke wasu daliban Jamiar Jos kan zargin kashe wani matashi.
Matashi mai shekaru 25 mai suna Ibrahim Mbaya, wanda aka fi sani da Ibee, ya mutu bayan wasu da ake zargi sun yi masa dukan tsiya kan zargin satar waya.

Source: Facebook
Daily Trust ta ce lamarin ya faru ne a wani gida da ke wajen harabar Jami'ar Jos, bayan yankin City of David da ke kan hanyar Ring a Jos.
Yadda aka zargi Mbaya da satar waya
Rahotanni sun ce Mbaya ya halarci wani taro a harabar jami'a kafin ya kwana a gidan wani abokinsa saboda dare ya yi, ana kuma cewa yana kokarin kammala wani sauran al'amari na karatunsa a jami'ar.
Da safe, abokan da suke tare da shi sun ce wata wayar iPhone ta bace. Saboda su kadai ne ke cikin dakin, suka zarge shi da satar wayar tare da fara dukansa.
Bidiyon da ya bazu a shafukan sada zumunta ya nuna yadda ake dukansa da katako da bulala, tare da azabtar da shi har sai da ya rasa hayyacinsa. Daga bisani ya mutu sakamakon raunukan da ya samu.
Rundunar 'yan sandan Plateau ta tabbatar da kama mutane uku da ake zargi da hannu a lamarin. Kakakin rundunar, SP Alabo Alfred, ya ce an mika su zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka domin ci gaba da bincike.
A cewarsa, 'yan sanda sun samu rahoto daga wani mutumin kirki bayan an kai marigayin Asibitin Koyarwa na Jami'ar Jos cikin halin rashin sani.
Likita ya tabbatar da rasuwarsa, sannan aka ajiye gawarsa a dakin ajiyar gawa domin binciken gawa, cewar Sahara Reporters.

Source: Original
An cafke wasu da ake zargi
Binciken farko ya nuna cewa daya daga cikin wadanda aka kama, Emmanuel Newyear, shi ne aka gani a bidiyon yana dukan marigayin da wani katon katako, haka kuma hotuna sun taimaka wajen gano wadanda ake zargi.
'Yan sandan sun ce wadanda ake zargin sun amsa cewa sun yi zargin Mbaya ya saci iPhone 12. Sai dai maimakon su kai karar lamarin ga jami'an tsaro, sun dauki doka a hannunsu har lamarin ya kai ga mutuwarsa.
Rundunar ta yi gargadin cewa kowa da ake zargi da laifi yana da hakkin a bi masa ka'idojin shari'a. Ta bukaci jama'a su daina hukuncin kangaroo, su rika kai rahoton laifi ga hukumomin da abin ya shafa.
An kashe iyalan Fasto a Plateau
A wani labarin, an ji cewa gwamnatin Amurka ta yi Allah-wadai da mummunan kisan da aka yi wa wasu daga cikin iyalan Fasto Ezekiel Dachomo a jihar Plateau.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce dole ne a hukunta masu hannu a kisan tare da ƙara tsaurara matakan tsaro ga Kiristoci da sauran al'ummomin da ke cikin haɗari.
Lamarin ya haifar da martani daga masu amfani da kafafen sada zumunta, inda wasu suka nuna shakku kan matsayar gwamnatin Amurka kan matsalar tsaro a Najeriya.
Asali: Legit.ng


