Kotu Ta Yi Hukunci a Shari'ar Cire Rubutun Larabci a Tambarin Sojoji? Gaskiya Ta Fito

Kotu Ta Yi Hukunci a Shari'ar Cire Rubutun Larabci a Tambarin Sojoji? Gaskiya Ta Fito

  • Wasu rahotanni sun yi ta yawo cewa wata kotu ta yi hukunci game da rubutun Larabci a tambarin sojojin Najeriya
  • Wani bincike ya gano ikirarin cewa Kotun Tarayya ta yi watsi da ƙarar neman cire rubutun Larabci daga tambarin rundunar sojin Najeriya ba gaskiya ba ne
  • An tabbatar da cewa lauya Malcolm Omirhobo ya shigar da ƙarar tun shekarar 2020, amma babu rahotannin sahihai da suka nuna kotu ta yanke hukunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wasu na ta yada jita-jitar cewa Kotun Tarayya ta yi zama kan shari'ar neman cire rubutun Larabci a tambarin sojojin Najeriya.

Wani lauya Malcolm Omirhobo ya shigar da ƙarar tun shekarar 2020, inda ya ke neman a cire rubutun daga jikin tambarin.

An yi bincike kan shari'ar neman cire rubutun Larabci a tambarin sojoji
Hafsan sojojin Najeriya, Laftanar kanal Waidi Shaibu. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Twitter

Sai dai rahoton Dubawa ya binciki wani ikirari da ake yadawa a Facebook cewa Kotun Tarayya ta Najeriya ta yi watsi da ƙarar neman cire rubutun Larabcin.

Kara karanta wannan

An fitar da hotunan yaran da ake ba horo kan jirage marasa matuka

Binciken ya nuna cewa wannan ikirari yaudara ne saboda babu wata hujja da ke tabbatar da cewa an yanke irin wannan hukunci.

An fara yada ikirarin ne ta wani mai amfani da Facebook mai suna Musa Muhammad Tajudeen a ranar 20 ga Yuli, 2026.

Rubutun ya ce kotun ta yi watsi da ƙarar tare da bayyana cewa wanda ya shigar da ita ba shi da hurumin wakiltar dukkan 'yan Najeriya a gaban kotu.

Sakon ya jawo martani daga mutane da dama, inda wasu suka nuna shakku tare da neman a gabatar da hujjoji.

Wasu sun tambayi sunan wanda ya shigar da ƙarar, tare da neman bayanan hukuncin kotu da rahotannin kafafen yaɗa labarai masu inganci.

Binciken ya gano cewa asalin lamarin ya samo ne daga ƙarar da lauya kuma mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam, Malcolm Omirhobo, ya shigar a Kotun Tarayya da ke Legas a shekarar 2020.

Omirhobo ya ƙalubalanci amfani da rubutun Larabci a kan wasu alamomin ƙasa, ciki har da tambarin rundunar sojin Najeriya da kuma takardun kuɗin Najeriya.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta hango kura kurai a kalaman Obi, ta yi masa zazzafan martani

Ya yi hujjar cewa hakan bai dace da tsarin mulkin Najeriya da ya tanadi rashin fifita wani addini ba.

Sai dai kasancewar an shigar da ƙarar ba yana nufin an yanke hukuncin da ake yadawa ba.

Rahotanni sun bincika rahotannin kafafen yaɗa labarai amma ba ta samu wata sahihiyar hujja da ke nuna cewa kotun ta yanke hukuncin da aka ambata ba.

Har ila yau, sakon ya yi kuskuren kiran Kotun Tarayya da suna kotun koli.

A gaskiya, Kotun Koli ce mafi girman kotu a Najeriya, yayin da Kotun Tarayya ke daga cikin manyan kotunan ƙasar amma ba ita ce ta ƙarshe ba.

Rahoton ya kuma tuna cewa akwai wata shari'a daban kan rubutun Larabci a kan takardun kuɗin Najeriya da Kotun Tarayya ta yi watsi da ita a shekarar 2024. Wannan hukunci bai shafi tambarin rundunar sojin Najeriya ba.

Saboda haka, binciken ya kammala cewa ikirarin da ke cewa Kotun Tarayya ta yi watsi da ƙarar neman cire rubutun Larabci daga tambarin rundunar sojin Najeriya yaudara ce, domin babu wata hujja mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan hukunci.

Kara karanta wannan

Dara ta ci gida, sojan da ake nema ruwa a jallo ya shigo hannu

An ƙaryata rahoton harbo jirgin Iran a Sokoto

A wani labarin, an ji cewa wasu rahotanni sun yada cewa rundunar sojojin Najeriya ta harbo wan jirgi marar matuki mallakin kasar Iran a jihar.

Sokoto Rahoton da aka yada kan lamarin ya jawo fargaba duba da yadda ake ci gaba da rigima tsakanin Iran da Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka.

Wani bincike ya nuna ainihin inda bidiyon ya fito da aka danganta da kasar Iraki, ba daga Najeriya ba kamar yadda ake ta yadawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.