'Ba Abuja ba ne,' 'Yan Sanda Sun Gano Jihar da 'Yan Ta'adda Suka Kashe Babban Soja
- Rundunar 'yan sandan Abuja ta musanta rahotannin da ke cewa an kai hari kan wani kanal na soja a cikin babban birnin tarayya
- Binciken da kwamishinan 'yan sanda ya ba da umarni ya gano cewa harin ya faru ne a yankin jihar Nasarawa ba a Abuja ba
- Rundunar ta gargadi kafafen yada labarai da masu amfani da shafukan sada zumunta kan yada rahotannin tsaro ba tare da tantance su ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya (FCT) ta yi karin haske kan rahotannin da suka bazu a shafukan sada zumunta cewa wasu masu garkuwa da mutane sun kai hari kan wani jami'in soja mai mukamin Kanal a Abuja.
Rundunar ta bayyana cewa duk da muhimmancin lamarin, binciken da ta gudanar ya tabbatar da cewa harin bai faru a cikin Abuja ba kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da jami'ar hulda da jama'a ta rundunar FCT, SP Josephine Adeh ta fitar a Facebook, ta ce kwamishinan 'yan sandan Abuja, Ahmed Muhammed Sanusi, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
A ina aka kashe sojan Najeriya?
Binciken da rundunar ta gudanar ya nuna cewa lamarin ya faru ne a garin Badna da ke karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa, ba a yankin da ke karkashin ikon rundunar 'yan sandan FCT ba.
Rundunar ta nuna damuwa kan yadda wasu shafukan yanar gizo da kafafen yada labarai suka danganta harin da Abuja domin jan hankalin jama'a.
A cewarta, irin wannan rahoto mara tushe yana haifar da fargaba da rudani ga mazauna babban birnin tarayya tare da yada bayanan da ba su dace ba.
Matakan da rundunar ta dauka
Kwamishinan 'yan sandan FCT ya kuma bayar da umarnin tura jami'an tsaro da na tattara bayanan sirri zuwa yankunan kan iyakar Abuja da jihar Nasarawa.
Sanarwar ta ce an dauki wannan mataki ne domin hana masu aikata laifi kutsawa cikin babban birnin tarayya ko aikata wani laifi a yankin.
Rundunar ta yi Allah wadai da yada labaran karya da ba a tantance ba, tare da yin kira ga kafafen yada labarai, masu rubutun yanar gizo da masu amfani da shafukan sada zumunta da su tabbatar da bayanan da suka shafi tsaro daga hukumomi.

Source: Original
Ta kuma bukaci al'umma su ci gaba da kasancewa cikin natsuwa, su kasance masu lura tare da kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga ofishin 'yan sanda mafi kusa ko ta hanyoyin gaggawa na rundunar.
Jihar Oyo ta karbi jiragen sintiri
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Oyo ta tabbatar da karbar sababbin jiragen sama guda biyu na sintiri domin karfafa tsaro da tattara bayanan sirri.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Dotun Oyelade, ya bayyana cewa isowar jiragen wani muhimmin mataki ne na bunkasa aikin sa ido ta sama domin tallafawa jami'an tsaro wajen dakile ayyukan masu laifi.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta sanar da shirin sayen jiragen tun a watan Yulin 2025 domin kara karfin hukumomin tsaro wajen tunkarar matsalolin rashin tsaro.
Asali: Legit.ng

